Wasu Abubuwan Da Ya Kamata Iyayen Su Tarbiyantar Da 'Ya'yansu Mata A Kai:


Wasu Abubuwan Da Ya Kamata Iyayen Su Tarbiyantar Da 'Ya'yansu Mata A Kai:

#Tsangayarmalamtonga 
Hakkin iyayena suyiwa abunda suka haifa tarbiya. Domin Allah (SWT) ne Yayiwa iyayen umurnin kare kawunansu dana iyalansu daga shiga wuta.

Hanya mafi sauki na kare Iyalanka daga shiga wuta shine na musu tarbiya akan tsarin Allah.

Sai dai wajen yiwa yara tarbiya, 'ya'ya mata sun fita daban. Domin hanyoyin da ake yiwa 'ya mace tarbiya yana da bambamcin dana abunda aka haifa namiji.

Ita diya mace tunda ta zo duniya har komawanta a karkashin kulawar iyayenta, mijinta da kuma abunda zata haifa take. 
Ga wasu abubuwan nan da iyaye zasu daura 'ya'yansu mata akai tun sunada karancin shekaru.

#Tarbiya
1: Ku nunawa 'yar ku mace ita ba kamar namiji bace. Akwai abubuwan da maza kadai suke yi da basu dace mata suyi ba.
Ku fahimtar da ita mace bata aiyukan karfi, ko wasannin buge buge irin na maza. Ta fahimci halittar daban yake dana halitun 'yan uwanta maza.

2: Nunawa Yar ku maza ba abokan da zata rika shiga cikin su wasa bane. Mata sune abokan wasanta.

3: Ku nunawa 'yar ku mace, mata basa zama da kanzata. Kuma mace a kullum tsaf ake son ganita. Don haka ta guji zama cikin kazanta a kuma nuna mata yadda zata tsaftace jikinta a duk lokacinda ta shiga ban daki. 

4: Ku nunawa 'yarku mace ta mutunta kanta ta kuma girmama mutane ta hanyar gaisuwa da bin umurnin na gaba da ita.

5: Ku hanata yin roko, da kuma rowa. Ku koya mata godiya idan an mata kyauta kuma tare da nuna mata ta kawo duk abunda aka bata wajen iyayenta ba tayi gaban kanta da shi ba.

6; Ko koyawa diyarku yadda 'ya mace take zama, kwanciya, tafiya, tsayuwa da kuma cin abinci.

Dukkanin wadannan abubuwan yadda mace take yinsu ya bambamta da na maza.

7: Ku guji barin ana yiwa 'yarku karama wasan mata da miji da wasu haka kawai suke yiwa yaran. Haka ku saka idanuwa sosai irin wasannin da yaran suke yi a junansu na mata da miji wanda a hakan suke kwaikwayon abunda miji da mata suke yi.

8: Ku tsawatarwa 'yar ku mace zama akan cinyar maza baki idan sun zo muku ko kunje musu. Wasu ta irin haka ne suke yiwa yara fyade. 

9: Ku fahimtar da diyar ku duk wanda ya mata maganar banza ko ya taba mata mahimman wurarenta ta fada a gida.

10: Duk girman da diyar ku mace tayi kada a rabata kwana daki guda da mahaifiyarta. Akwai alfanu da fa'ida matuka na barin 'ya'yan ku mata ko bayan balagansu ne su rika kwana da uwarsu daki daya.

#tsangayarnalam 
Wadannan wasu ne daga cikin hanyoyin yiwa 'ya'ya mata tarbiya.

Allah Ya datar damu wajen yiwa abunda muka haifa tarbiya na gari.

Post a Comment

0 Comments