NEMAN AURE AKAN NEMAN AURE:
Manzon Allah saw yace: kada wani ya nemi aure akan neman auran ɗan uwansa har sai ya bari ko ya bayar da izni. Bukhari da Muslim.
Wannan hadisi ya tabbatar mana da cewa :
1. Idan ka tabbatar an bashi ko an yi baiko, haramun ne ka shiga,
2. Idan ka tabbatar an dakatar da shi, ko ba a amsa masa ba, babu laifi ka shiga nema.
3. Idan ka sani zato mai karfi an bashi kada ka shiga nema.
4. Idan kana da zato mai ƙarfi ba a bashi ba, babu laifi ka shiga, tunda a farkon nema ne,
5. Idan kana kokwanto kada ka shiga sai ka tabbatar tukunna.
6. Wannan doka da Manzon Allah saw ya sanyawa hannu, domin Samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi, da kawar da gaba da kiyayya tsakanin al'umma, yanzu anyi fatali da wannan doka saboda son duniya da yayi katutu a zukatan wasu daga cikin al'umma,
7. Wani lokacin daga yarinyar ne, ta zama mai ruwan ido da hange- hange ta na son wannan tana hangen waccan, ta tare wani tana jiran wani wanda ya fishi,
8. Wani lokacin daga shi mai nan auran ne, yayi magana da iyalan ta sun amince ya ci gaba da neman aure, amma yana hangen wata, ƴar masu kuɗi,
9. Wani lokacin daga iyaye ne masu magana biyu, sun bawa wani izni ya fara nema sai wanda ya fishi kuɗi ko ilmi ko muƙami ya fito a bayan sa sai a raba musu hankali, suga wa ya kamata su bawa daga ciki, sai a raba musu hankali,
Rashin cika alkawari, yaro yana son yarinya sun ɗauki tsawon lokaci suna tare, sai rana ɗaya wani yazo da kuɗi ko wata alfarma sai a yi watsi da wanda ya daɗe yana wahala da ita, ba dole aga musifa iri-iri ba?
10. Wani lokacin har matar aure tana iya neman idan wani mai hali zai aure ta, ta kashe auranta, don Kwadayi.
Akwai wacce sai da suka gama yarjejeniya da wanda zai aure ta, har sai da ya bata kuɗin siyo kayan aure sannan ta nemi mijin ta ya sake ta.
Duk wanda ya nemi aure akan neman auran wani har ya nuna masa fin karfi ya auri matar, wannan auran akwai alamar tambaya akan sa?
Allah ya sawwaƙe wannan hali na Kwadayi da rashin cika alkawari da ake fama da shi.
0 Comments