Mu Farka Mata: Dogaro Da Kai A Tsakanin Mata Sana’a:



Mu Farka Mata: Dogaro Da Kai A Tsakanin Mata Sana’a:


Sana’a
Mecece sana’a?

 
Sana’a ita ce dogaro da kai, neman na halal ta hanyar saya da sayarwa, ko kerawa ko sarrafa wani abu a aikace da hannu a biya ki.


Shin dole sai ki na da babban jari ko babban kanti kafin ki fara sana’a?
 

A a da karamin jari za ki iya fara yin sana’a, haka ko babu jari ma za ki iya fara sana’a. Kananan sana’oi ga matan da su ke zaune a cikin gida har ma da mata ma’aikata da su ke fita aiki ta na taimakawa matuka. Sana’oi sun kasu kashi uku akwai wacce sai kin sami jari kin saro sannan ki sayar misali: barkono, man ja, man gyada, gishiri , maggi, goro da sauransu. Kashi na bityu kuma ita ce wacce za ki yi da hannunki ba kya bukatar neman jari. Misalin: Kitso, kunshi. Sannan ta uku ita ce wacce za ki nemo kudi kadan don fara sana’a sannan ki hada da aikin da hannunki su ne kamar : dinki, dinkin hula , saka, zobo, kunun tsamiya, kosai da sauransu.

Ba kowacce mace ba ce ta sami damar yin karatun zamani ko da ta yi karatun ba kowanne miji ba ne zai bar ta ta yi aiki ba. Kowacce mace Allah Ya hore mata hannaye biyu da lafiya da za ta iya yin sana’ar hannu ko ta yi amfani da dan karamin jari ta yi sana’a.



Me ya ke hana mata yin sana’a?

 
Baban abin shine girman kai da rainuwa akan riba kadan, daga in da aka sami haka dole akwai mutuwar zuciya dan sai kin jiran miji ya yi miki komai . Duk lokacin da ki ka kasance babu wani kudi da ya ke shigo miki komai kankantarsa tabbas za ki tsinci kanki kin zama marokiya, in ba a ci sa’a ba ki fara lalube aljihun miji. Za ki tsinci kanki da gagarumin samun bacin rai saboda duk sanda ki ka roka za a baki din amma za ki ga canji a fuska kafin a ida gajiya da ke ayi miki tsawa. Ma su daukar albashi ba lallai ya na isar su ba kafin karshen wata, sai su buge da karbar bashi amma idan ki ka hada aikin da sana’ar ba za ki taba rasawa ba.

 

Matan da su ke zaune a cikin lunguna su na sana’ar sayar da danwake, wake da shinkafa ko tuwon dawa su na iya hada adashin da ake yin zubi a kowacce rana, za ku sha mamaki idan ku ka ga da nawa su ke tashi a karshen wata. Allah Ya na sakawa masu sana’a albarka a dalilin dogaro da kai da su ka yi na neman halaliyarsu.

 

Ina mafita?

Ita ce kowacce mace ta tashi ta yi tunanin abin da za ta yi ta rufawa kanta da yaranta da iyaye da shi kansa mai gida asiri. Da wahala a ce dan mijinki ya dauki nauyin ki a komai ya zamanto ba ki da wata bukata ta ki ta daban wacce ba za ki jira ko ki so wani ya ji ba. Idan ma babu jari ki yi kokarin ki koyi kera wani abu da hannunki yadda ko ba ki da jari za ki iya yi a biya ki . Ki koyi sarrafa wani abu da kudi kadan ya kawo miki kudi da yawa.

Ya kamata iyaye mata su karanci ‘ya’yansu sosai tun su na kanana su ga a ina su ka fi karfi, ina su ka dosa, me su ka fi sha’awar kerawa?

Ya na da kyau a koya wa yara sana’a da zarar sun fara tasowa, ba lallai sai yarinya ta fita ta yi talla ba, ta na zaune a cikin gida za ta iya sarrafa wani abu a zo har gida a saya.

Ya kamata mazaje su bawa batansu karfin guiwa su yi sana’a su taimaka musu da jari da shawarwari, in akwai makarantar da za su kai su su ko yi sana’a su yarje musu su je su koya. Maza a rage bakin ciki ka da dan ka ga matarka ta na da dan jari ka sakar mata komai na wahalar gida yadda jarin zai lalace.

Mata a junanmu mu rage kyashi mu taimakawa ‘yan uwanmu mata da ba su da sana’a, a koya mu su, ka da ki yi tunanin idan ta gane irin sana’arki za ta zo ta fi ki daukaka. Allah ke ba da daukaka kuma rabon bawa baya wuce shi sai ya biyo shi har in da ya ke. 

Post a Comment

0 Comments