Maganin ciwon mara na maza harda mata



Maganin ciwon mara na maza harda mata:


Matsalar ciwon mara ba iya mata ke damu ba,amma su mata sunfi yi ne a lokacin period wato Al'ada(menstruation) amma maza suna yi ne saboda matsalar infection da suke dashi a prostate.

Wannan nauyin infection ana kiran sa prostate infection, prostate wani karamin abu ne da yake kadan bladder (mafitsara) wanda shine yake control na fitsarin ka kuma shine hanya wacce fitsari da maniy suke bi ta cikin sa.

 
Hakan ne yasa fitsari da maniyy basa fita lokaci daya,saboda lokacin da maniyy zai fita prostate yana rufe hanyar fitsari ya hana shi fita koda kuwa kana jin sa.

 
A lokacin da infection yakai ga prostate naka akwai alamomi da zaka rika ji kamar:

1. Zafin fitsari.
2. Dawowar fitsari bayan an gama.
3. Rashin iya gama fitsari.
4. Jin zafi bayan fitar maniy.

Da sauran su.



Yadda zaa magance wannan matsala:

1. Ruwan kaninfari,idan ana jika kaninfari na kwana 2 ana shan wannan ruwa yana magance wannan matsala idan aka sha tsawon sati 1.

2. Lemon tsami da ruwan dumi,idan ana matsa lemon tsami a ruwan zafi ana sha kullum sau 1 na sati daya shima yana magance wannan matsala.

 
3. Antibiotics na asibiti suma idan ana sha yadda likita yayi bayani shima yana kawar da wannan matsala.

 
Idan akai wadan nan na wani lokaci ba'a samu sauyi ba aje ga likita.

Allah ne masani.

Post a Comment

0 Comments