Illolin Yin Sakace Ga Lafiyar Dan Adam



Illolin Yin Sakace Ga Lafiyar Dan Adam


Abdullahi Abubakar Umar


Wani babban likitan hakori, ya bayyana illolin da ke tattare da yin sakace musamman da tsinke da wasu daga cikin mutane ke yi.

Dakta Basil Ojuku, wanda babban masani ne a harkar lafiyar hakori kuma babban jami’i ne a Hukumar Lafiyar Harkora ta Kasa da Kasa a Afirka da ke Jos, ya bayyana cewa yin sakace da tsinke na haifar da babbar illa ga hakori da kuma dasashi.


Ya bayyana cewa yin sakace na haifar da rauni a hakori da dasashi; Yana kuma haifar da ramuka da kwararo a tsakanin hakora da dasashi.

Ya kara da cewa hakan na haifar da cutar ‘periodontitis’, wacce ke lalata dasashi, wani lokacin ma har ta taba kashin haba.


Har ila yau ya ce yin amfani da hakori wajen bude lemon kwalba na iya haifar da karyewar hakori.

A karshe ya shawarci jama’a da su rika amfani da zaren sakace wanda a likitance aka yarda da ingancinsa.

Post a Comment

0 Comments