Hanyoyin Maganin ‘Infection’ Cikin Sauki
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Da farko Lallai ya kamata ku gane cewa infection yanada wuyan magani domin maganine da se andauki lokaci anayi kamin ya warke gaba daya,inda sansamune ku dauki lokaci kaman wata 6 ajere koma fiye shine zakiga kin maganceshi gabadaya amma in zaki fara ki bari to lallai zaki dade kina magani baki maganceshi gabadayaba. kuma lallai wacce take da miji sai sunyi magani su biyu amma intasah magani ita kadai kamar tayi a bandane don suna kara saduwa da mijin ata kara daukar ciwon_
Mu na rokon da Allah ya baku lafiya ingantatta kuma yasa kaffarane.
A gwada daya daga cikin wadannan:
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
1- A samu Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
2- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.
3- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima.
4- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.
5- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima.
6- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta na sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
7- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki dauki sala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku.
8- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi.
Ni’ima Ba Sassauci:
Da farko daki samu kadarki wadda ba ta fara kwai ba. Sai ki dare hanjinta ta cikin dunbutu tunda ba a bukatar a yi mata gunduwa-gunduwa. Sai ki gyara ridinki (kantu) ki shanya ya bushe sai ki daka shi. Kina iya tafasa kadar sannan sai ki duba ridin ta cikin dunbutun kadar. Sai ki samu abu ki daure dumbutun; sannan ki hada kayan miya kadan sai ki kara duba nonon rakumi a cikin kayan miyar ki hada ki dafa har sai sun dahu sai ki sauke. Sannan a ranar ki jika kanumfari ya jiku sosai. Ya dama ruwan shanki.
Kunun Zakin Dabino:
Za ki sami dabino mai kyau ki cire ki tsabtace shi, saiki jika har sai yayi taushi sosai sai ki markada a blander , kisaka zuma ko suga kadan da madarar ruwa, asa yayi sanyi sai ki sha.
💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
Jan Hankali Ga Mai Matsalar Bushewar Farji
Sirrin Bushewar Farji
’Yar’uwa ga dama ta samu, idan ki na fama da bushewar farji, a koda yaushe to sai ki sami man zaitun da man habbatussauda, sai ki hada su wajen daya, ki dinga shafawa a cikin farjinki insha Allah Zaki ga biyan bukata, domin kowace cuta tana da magani, sai dai in baki nema ba, amma in kika nema Zaki samu.
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
Allah Ya sa mu dace.
0 Comments