Dalilai 6 da ya sa jima’i ke da mahimmanci wajen inganta lafiyar namiji – Binciken Kwararru
Jima’i na daya daga cikin abubuwan dake gamsar da mutum a rayuwa da idan babu shi wasu da dama ba za su iya gudanar da harkokin rayuwa kamar yadda ya kamata ba.
Baya ga haihuwa iima’i na kara dankon soyayya tsakanin masoya, samar wa wasu kariya daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, kawar da damuwa da tsananin tunani.
Ga namiji jima’i abune dake taimakawa wajen inganta lafiyar sa da rayuwarsa inda ko da yana yi kulum ba zai cika samun matsala ba.
Ga wasu hanyoyi da jima’i ke inganta lafiya da rayuwar namiji:
1. Kare namiji daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.
2. Kaifafa kwakwalwar namiji musamman wajen bashi damar yin zurfin tunani.
Jima’i na taimakawa namiji wajen yin tunani mai zurfin da rashin sa kan sa namiji yawan mantuwa da rashin iya fahimtar abubuwa.
3. Inganta bugawar numfashi a zuciya da kare namiji daka kamuwa da cututtukan zuciya.
Jima’i kamar motsa jiki yake sannan motsa jiki na taimakawa wajen rage kitse a jiki musamman Wanda ke zuciya wanda hakan ke inganta bugawar numfashi a zuciya.zuciya.
4. Taimakawa namiji wajen samun hutu, nishadi da gamusuwa kuma ya sa a yi barci yadda ya kamata.
Duk namijin da baya jima’i akai-akai ko Kuma ma kwata-kwata mutum ne da zai zamo cikin damuwa.
Jima’i na kwantar wa namiji hankali matuka.
5. Jima’i na kawar da damuwa da ciwon jiki da ciwon kai.
6. Kara wa namiji tsawon rai da karfi a jiki
Binciken Kimiya ya nuna cewa jima’i na hana saurin tsufa a maza inda ko da shekarun su na da yawa za a ga namiji na nan da karfinsa.
💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏
0 Comments