Amfanin Zogale Guda 25 Ga Lafiya Da Ba Kowa Ya Sani Ba:
SHARE 🌿🌿🌿
Zogale wata bishiya ce mai matukar amfani ga lafiyar dan-adam. Shekaeu aru-aru da su ka gabata, al'ummomi daban-daban a sassan duniya ke amfani da zogale wajen gamanin matsaloli lafiya.
Zogale ya shahara wajen maganin wasu cututtuka, kuma jama'a na samun wannan fa'ida ta zogale ta hanyar yin amfani da ganyensa, saiwarsa 'yayansa, sassakensa da sauransu.
Wani abin farin ciki shine, a wannan zamani an samu ci gaba wajen kara nazari da bincike kan zogale da kuma amfaninsa ga lafiyarmu. Binciken baya-bayan nan ya nuna yadda zogale ya kasance wata bishiya mai matukar tasiri wajen inganta lafiya.
Binciken wannan zamani ya nuna cewa, baya ga amfanin ganye da 'ya'ya da saiwa da sassaken zogale ga lafiyar dan-adam, hakanan masana sun gano yadda ake sarrafa zogale ta wasu hanyoyi daban don samun waraka. Bincike ya yi nisa, har masana'antun da ke samar da magungunan zamani kan yi amfani da zogale don samar da magungunan zamani, wadanda ke taimaka wa wajen kiwon lafiya kwarai da gaske.
1. Zogale Na Kara Karfin Garkuwar Jiki:
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Mutum ya samu ganye zogale ya shanya, idan ya bushe sai ya nika ko daka shi don ya samu garinsa, ya ke zubawa cikin abinci, ya ke ci, ko shakka babu hakan na kara ingantawa tare da kara karfin garkuwar jiki.
2. Zogale Na Taimakawa Wajen Kara Ruwan Nono:
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Idan mace mai shayarwa na fama da karancin ruwan nono sai ta yi amfani da zogale don samun maganin matsalarta. Yadda za ta yi shine ta samu fure ko hudar zogalen ta hada da zuma ta ke sha.
3. Zogale Na Maganin Kurajen Jiki:
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Idan mutum ya na fama da kuraje a jikinsa, sai ya samu ganyen zogale ya shanya shi ya bushe, sannan ya daka shi don ya samu garinsa. Wannan garin zogalen zai hada da man zaitun ya ke shafawa, bayan ya tsaftace wajen da kurajen su ka fito ma sa.
4. Zogale Na Taimakawa Wajen Saurin Warkewar Rauni:
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Kamar yadda bayani ya gabata cewa, zogale na warkar da kuraje, kuma ya na taimakawa wajen tsayar da jini idan an ji ciwo, to haka kuma ya ke taimakawa wajen warkewar rauni cikin sauri. Garin zogale mutum zai samu ya ke zubawa a kan raunin, zai warke da gaggawa.
5. Zogale Na Maganin Shawara. Don mutum ya samu fa'idar zogale dangane da maganin shawara, sai ya juri shan ruwan dafaffen zogale.
6. Maganin Ciwon Kunne: Ga mutumin da ke fama da ciwon kunne, sai ya samu danyen ganyen zogale, ya kirba ko dandaka, sai ya zuba ruwa kadan ya matse sannan ya tace, don ya samu ruwansa, to wannan ruwan ze ke diga wa a kunnen, zai samu sauki idan Allah Ya lamunce.
7. Zogale na maganin ciwon kai: Yadda mutum zai yi amfani da zogale don maganin ciwon kan da ya ke fama da shi, shine ya samu danyen ganyen zogale ya dandaka ko ya kirba sannan sai ya shafa a goshinsa, in sha Allahu zai samu saukin ciwon kan da ya ke fama da shi.
8. Zogale Na Taimaka wa Wajen Kewayawar Jini Cikin Jijiyoyin Jiki: Mutum ya samu ganye zogale ya shanya, idan ya bushe sai ya nika ko daka shi don ya samu garinsa, ya ke zubawa cikin abinci, ya ke ci, ko shakka babu hakan na taimaka wa wajen zagayawar jini cikin jiki kwarai da gaske.
9. Zogale Na Maganin ciwon Ido: Idan mutum na fama da ciwon ido, sai ya samu danyen ganyen zogale, ya kirba ko dandaka don ya samu ruwansa kamar yadda mu ka ambata a sama dangane da ciwon kunne, to wannan ruwan ze ke diga wa a idon, zai samu sauki idan Allah ya lamunce.
10. Zogale Na Karawa Mutum Kuzari: Mutum ya samu ganye zogale ya shanya, idan ya bushe sai ya nika ko daka shi don ya samu garinsa, ya ke zubawa cikin abinci, zai samu karin kazar-kazar.
11. Zogale na Tsayar Da Jini Idan Aka Yi Rauni: Idan mutum ya yanke ko ya sare da wani ma'aikaci da ya ke aiki da shi, sai ya samu danyen ganyen zogale, ya sarrafa shi kamar yadda mu ka fada a sama lamba ta 4 ya shafa a wajen, da sannu jinin zai tsaya.
12. Zogale Na Maganin Mura: Ga duk mai fama da mura, sai ya samu fure ko hudar zogale ya hada da albasa ya ke dafa shayi da su ya na sha, yin hakan na maganin mura kwarai da gaske.
13. Zogale Na Maganin Olsa (Ulcer) :
Yadda mutum zai yi domin ya samu wannan fa'idar zogale game da olsa shine, ya samu danyen ganyen zogale ya ke hadawa da zuma ya ke dafawa kamar shayi, ya ke sha, ba shakka wannan hadi maganin Olsa ne sadidan.
Ko kuma ya samu danyen ganyen zogale ya shanya shi, amma a inuwa don gudun kar wasu muhimman sanadarai su kone idan ya shanya shi a rana. Idan ya bushe sai ya daka ya ke sha da madarar 'Peak' ta ruwa.
14. Zogale Na Maganin Shawara: Yadda zai yi shine yake dafa ganyen zogale, sai ya sanya kanwa 'yar kadan domin maganin shawara.
15. Maganin Tsutsar Ciki: Idan ana tsammani yaro na da tsutsar ciki, sai ake ba shi danyen zogale ya na ci, idan Allah Madaukaki ya amince zai rabu da tsutsar ciki.
16. Zogale Na Maganin Sanyin Kashi: Ga wanda ke fama da wannan matsala sai ya samu 'ya'yan zogale ya soya sannan ya daka ya hada da man ja ya cakuda ya ke shafawa, ba shakka hakan na maganin sanyin kashi.
17. Zogale Na Maganin Basur: Don mutum ya samu fa'idar zogale dangane da maganin basir, sai ya juri shan ruwan dafaffen zogale.
18. Zogale Na Taimaka wa Ma Su Fama Da Hawan Jini: Ga wanda ke fama da hawan jini kuma ya ke fatan saukar sa, sai ya samu garin zogale ya ke zubawa cikin abinci ya na ci, in sha Allahu zai samu sauki.
19. Zogale Na Taimakawa Wajen Saurin Narkar Da Abinci: Cin dafaffen zogale na taimakawa kwarai da gaske wajen saurin narkar da abinci.
20. Zogale Na Maganin Cushewar Ciki.
21. Zogale Na Da Tasiri Wajen Wankin ciki.
22. Zogale na taimakawa wajen rage kiba.
23. Zogale na samarwa jiki sanadaran gina jiki, wanda hakan ke maganin karancin abinci mai gina jiki. Wannan ku wa ya shafi manya da yara gaba daya.
24. Zogale na taimakawa ma su cutar sikila, kuma za su samu wannan amfani ta hanyar yawan amfani da zogalen.
25. Zogale Na Taimakawa wajen samun karfin gani.
SHARE 🔔
0 Comments