Amfani 15 da ganyen itaciyar gwaiba yake yi a jikin dan adam:
Abubuwan da ke ciki:
Ga dai wasu amfani guda 15 da ganyen itaciyar gwaiba yake yi a jikin dan adam da kuma dalilin da zai sanya ku fara shan shayin ganyen gwaiba:
1. Maganin Gudawa
2. Rage Mai (Kitse)
3. Rage Ciwon Suga
4. Taimakawa wajen rage kiba
5. Maganin cutar daji (Cancer)
6. Maganin sanyi da tari
7. Yana rage kurajen fuska
8. Yana kara karfin fata
9. Yana hana gashi zubewa
10. Maganin ciwon hakori
11. Taimakawa wajen samun bacci cikin nutsuwa
12. Bunkasa garkuwar jiki
13. Maganin cututtuka na ciki
14. Taimakawa wajen samun lafiyar zuciya
15. Taimakawa kwakwalwa
Sinadarin Potassium dake jikin ganyen itaciyar gwaiba yana taimakawa wajen daidaita yanayin jinin jikin dan adam. Saboda yana dauke da kusan kashi 80% na ruwa yana kuma dauke da wadataccen sinadarin fibers, sannan yana taimakawa wajen rage kiba.
Amma shin kun san cewa ganyen gwaiba yana da matukar muhimmanci ga lafiyar jikin dan adam shi ma? Za a iya dafa ganyen itaciyar ta gwaiba don yin shayi, wannan shayi ya zama tamkar shayi na gargajiya a kasar Mexico da wasu bangarori na Kudancin Amurka.
“Wadannan ganyayyaki suna da sinadarin antioxidants kamar irinsu bitamin C, da flavonoids, da quercetin,” cewar wani masani a bangaren ganyayyaki na birnin Delhi, Anshul Jaibharat.
Idan kuna son yin shayin ganyen gwaiba, abinda kawai zaku yi shine, ku jika ganyen gwaiba din a cikin kofi da ruwa mai zafi ku sha.
Ga dai wasu amfani guda 15 da ganyen itaciyar gwaiba yake yi a jikin dan adam da kuma dalilin da zai sanya ku fara shan shayin ganyen gwaiba:
1. Maganin Gudawa:
A yadda wani bincike da aka wallafa a Revista do Instituto de Medicina Tropical de Sao Paulo, ganyen gwaiba yana maganin cutar staphylococcus aureus, wacce ita ce gudawa take samo asali daga jikinta. Mutanen dake fama da gudawa kuma suke shan shayin ganyen gwaiba, ka iya fuskantar karancin ciwon ciki, sannan kuma yana kawo waraka idan ana fama da gudawa aka sha, a cewar Drugs.com. Ku zuba ganyen da jijiyar gwaibar a cikin kofi mai dauke da tafasashen ruwa, a tace ruwan sai mutum ya sha kafin ya ci komai.
2. Rage Mai (Kitse)
Wani sinadari da ake kira da LDL ko kuma Low-density lipoprotein suna daya daga cikin manyan abubuwa guda biyar da suke jigilar kwayoyiyin kitse a jikin mutum. Yawaitar wannan kwayoyi na kitse ne ke haifar da tarin matsaloli na lafiya musamman ga zuciya. A cewar wani rubutu da aka wallafa a Nutrition and Metabolism, masanan sun bayyana cewa mutanen da suke shan shayin ganyen gwaiba suna samun raguwar kitse bayan makonni takwas.
3. Rage Ciwon Suga
Kasar Japan ta amince da shayin ganyen gwaiba a matsayin daya daga cikin abinci da suke amfani dashi wajen maganin cutar ciwon suga. Sinadaran dake jikin wannan shayi suna taimakawa wajen rage suga a jikin mutum bayan cin abinci. A cewar wani rubutu da aka wallafa a Nutrition and Metabolism, shayin ganyen gwaiba yana hana kwayoyin cuta daban-daban da suka canjawa zuwa carbohydrate ta hanyar narkewa su zama glucose.
4. Taimakawa wajen rage kiba
Shin kuna neman yadda zaku rage kibar jikinku? Ku sha shayin ganyen gwaiba. Ganyen gwaiba yana taimakawa wajen hana wasu kwayoyi na jikin dan adam su koma suga, sannan yana taimakawa wajen rage kiba, Ku sha ruwan shayin gwaiba domin samun wadannan amfanoni.
5. Maganin cutar daji (Cancer)
Dr. Anju Sood ya ce: “Ganyen gwaiba yana rage kamuwa da cutar daji,” musamman ma ta nono, da kuma ta dubura, saboda wadataccen sinadarin antioxidant lycopene. Bincike da dama sun nuna cewa sinadarin lycopene yana taimakawa sosai wajen rage kamuwa da cutar daji.
6. Maganin sanyi da tari
Ganyen gwaiba yana dauke da sinadarin bitamin C da Iron, ganyen gwaiba yana matukar taimakawa wajen magance tari da sanyi, saboda yana taimakawa wajen kawar da dattin ciki. Haka kuma yana lalata duk wani datti da ya taru a wajen numfashi, da suka hada da makogwaro da hunhu.
7. Yana rage kurajen fuska
Saboda wadataccen sinadarin bitamin C da ganyen gwaiba yake da shi, ya sanya yake taimakawa wajen kawar da kurajen fuska, idan aka daka aka sanya a wajen da kurajen suke.
8. Yana kara karfin fata
Gwaiba na da isasshen sinadarin astringent, bincike ya nuna ganyen gwaiba din ma yafi wannan sinadari. Idan aka daka ganyen aka sanya a wajen da ake so yayi aiki zai taimaka wajen gyara fatar da kuma kara karfinta.
9. Yana hana gashi zubewa
Shin kuna fama da zubewar gashi? Ganyen gwaiba zai kawo karshen duka matsalolin ku na gashi. Za a tafasa ganyen ayi amfani da ruwan wajen wanke gashin. Gwaiba na dauke da sinadarin antioxidants, wanda zai taimaka wajen karin gashi. Sai dai kuma: A tabbatar da ruwan yayi sanyi kafin ayi amfani da shi a gashin.
10. Maganin ciwon hakori
Anshul Jaibharat masani a fannin abinci mai gina jiki a birnin Delhi na kasar Indiya, ya ce ganyen gwaiba yana taimakawa matuka wajen lafiyar baki. Shayin ganyen gwaiba yana taimakawa wajen maganin ciwon hakori. Haka kuma za a daka ganyen a dinga sanya garin a wajen da hakorin yake ciwon domin magani.
11. Taimakawa wajen samun bacci cikin
nutsuwa
“Shan shayin ganyen gwaiba akai-akai yana taimakawa wajen samun bacci cikin nutsuwa,” cewar Dr. Ashutosh Gautam, wani masanin lafiya a Baidyanath. Shayin na kwantarwa da mutane hankali, inda yake taimakawa wajen samun wadataccen bacci.
12. Bunkasa garkuwar jiki
A cewar masanin ilimin abinci mai gina jiki na Bangalore Dr. Anju Sood, ya ce: “shayin ganyen gwaiba na taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki,” hakan ya sanya yake rage barazanar kamuwa da cututtuka daban-daban.
13. Maganin cututtuka na ciki
Ganyen gwaiba na da amfani wajen magance cututtuka na ciki, haka kuma yana taimakawa wajen rage dattin ciki da yake sanya narkewar abinci, sannan kuma yana hana samun kwayar cuta a cikin hanjin mutum.
14. Taimakawa wajen samun lafiyar zuciya
“Shayin ganyen gwaiba yana kuma iya taimakawa zuciyarku wajen yin aiki cikin koshin lafiya,” cewar Anshul Jaibharat.
15. Taimakawa kwakwalwa
“Ganyen gwaiba yana dauke da sinadarin bitamin B3 (niacin) da bitamin B6 (pyridoxine), wadanda ke taimakawa wajen inganta yaduwar jini zuwa kwakwalwa, kara kuzari da kuma kwantar da jijiyoyi,” cewar Dr. Manoj K. Ahuja.
0 Comments