YANDA ZA KI MAGANCE CIWON MARA A LOKACIN AL'ADA:
SHARE 🔔
1. TSAMIYA
A samu sabuwar Tsamiya a jika aruwa tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan tun kwana biyu kafin zuwa haila, har lokacin da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da dama sun jarraba kuma sun dace.
2. MAN ZAITUN:
A sami man zaitun sai a Karanta ayoyin Alqur'ani acikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta.
Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al'aurarta saboda ayoyin da aka tofa). Shima wannan idan anyi shi za'a dace. Koda Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke sanya mata ciwon jikin to zata samu waraka.
3. KUSTUL HINDI:
Idan an jikashi a ruwa ana shansa safe da yamma shima yakan Magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al'ada. Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.
Allah ya sa mu dace
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
0 Comments