YADDA ZAA MAGANCE MATSALOLIN FATA DA MAN KADANYA CIKIN SAUKI:


YADDA ZAA MAGANCE MATSALOLIN FATA DA MAN KADANYA CIKIN SAUKI.

Ka daure kayi share don Annabi sallallahu Alaihi wasallam.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu,yan uwa na barkan mu da warhaka a yau muna dauka da bayani ne akan amfanin man kadanya wanda da dama wasu basu san amfani mn sa ba,gani suke kawai kamar magance kaushin kafa yake.

Eh! Haka ne yana magance kaushin kafa mma amfanin sa ya wuce nan don man kadanya bincike ya nuna ya dauke da Bitamin A da E don haka yana taimakawa fata sosai wajen hana ta kamuwa da kuna warkar da cututtukan da suke fitowa a tare da ita.

YADDA ZA'A MAGANCE MAKERO:

1. Man kadanya.
2. Man zaitun.

Ana hada man kadanya da man zaitun a kwaba sosai a rika shafa shi a duk inda makero ya fito.

YADDA ZA'A MAGANCE KYASBI:

1. Man kadanya.
2. Man Habbatussauda.
3. Man kwakwa.

Duk a hada waje guda a kwaba a rika shafawa a duk inda suka fito sfima wannan yana magance natsalar kyasbi a jikin mutum .

YADDA ZA'A MAGANCE KURAJEN ASKI:

1. Man kadanya.
2. Man ik'lil jabal (Roseberry). 
3. Man kwakwa.

Shima a hade su waje guda a rika shafawa a inda kurajen suka fito,bayab kashe su da sinadaran zasuyi har kyau baki da laushi zasu sa gashin wajen yayi.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanin man kadanya.



LIKE AND SHARE:

Post a Comment

0 Comments