Yadda za a magance tabo koh kurajen fuska cikin sauki
Assalamu Alaikum
Matsalar kuraje da tabon fuska sun shafi bangaren matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar.magance.kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa. Rashin bacewar tabo a fuska na bata. kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon. Da yawan mutane sun gwada.mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.
daga Duniyar fasaha A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a.san cewa daya za.a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.
1- A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.
2- Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan yana.hana su sake fitowa.
3- A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
4- a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
5- A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.
Insha Allah za,a dace
in kasamu wannan post da ban sha,awa taimaka ka turawa yan uwa da abokan arziki dan su karu.
0 Comments