Wasu Dalilan Da Suke Sa Gaban Namiji Ƙankancewa:
#Bincike
Gaban namiji da aka fi sani da suna azzakari.
Ɓangare ne na jikin namiji mai matukar mahimmanci a rayuwarsa. Duk kuwa da amfaninsa bai wuce yin Jima'i, samar da haihuwa da kuma fitar da ruwan da jikin mutum baya buƙata.
Mazan da suke da ƙaramin gaba suna shiga cikin damuwa matuka duk kuwa da ƙankantar gaba da girmansa bai da tasiri a waɗannan aiyukan da gaban namiji yake yi.
Sai dai duk da hakan da akwai tsawon da ya kamata kada gaban namiji ya gaza kaiwa kamar yadda masana suka ce gaban namiji yana so ya kasance 9.16 a ma'aunin centimeters. Wato inci 3.6. Idan a mike yake kuma ya kasance 13.24 na cm. Kamar inci 5.3 kenan.
Shi dai tsawo ko kaurin gaban namiji bai da nasaba da fatarsa, kabilansa. Kawai baiwa ne da kuma halitta.
#Tsangayarmalamtonga
Akwai wasu mazan da bayan wani lokaci sai suga gabansu ya ƙankance ba kamar yadda yake a baya ba. Hakan kuma na sasu damuwa da kuma zullumin rashin sanin abunda ya jawo hakan.
Tabbas da akwai wasu abubuwan da suke jawowa gaban namiji ya ƙankance kamar yadda binciken masana ya tabbatar. Waɗannan abubuwan kuwa sun hada da:
#Bincike
1: Shekaru- Shekaru na jawo gaban namiji ya ƙankance. A lokacin da girma ya soma cimma namiji, ana samun raguwar gudanar jini yadda ya kamata zuwa gaban namijin da girma ya soma kamashi. Hakan sai ya jawo gabansa ya ƙankance ya ragu ba yadda yake a baya ba.
2: Girman Jiki: Da zaran mutum ya kara kiɓa, musamman idan yayi tumbi tofa dole gabansa ya ƙankance.
Jijiyoyin gaban na miji yana haɗe ne dana tumbinsa. Don haka da zaran jikinsa ko tumbinsa ya ƙara girma sai kuma gabansa ya ƙankance.
3: Ciwon Mafitsara: Likitocin sun gano ce mafiya yawan mazan da aka musu aiki a mafitsaransu gabansu na ƙankancewa. Duk kuwa da masanan sun kasa gano dalilin dake haifar da hakan. Amma dai akwai tabbacin muddin aka yiwa namiji wannan aikin, sai gabansa ya ragu daga yadda yake a baya.
4: Ciwon Fibrous: Shi wannan ciwon yakan sa gaban namiji ya lanƙwashe, kuma yana masa zafi a lokacin da ya miƙe.
Haka kuma yakan sa gaban namiji ya ragu daga tsawo dama kaurinsa kamar yadda masana suka ce.
5: Ƙwayoyi: Masana sun gano akwai wasu ƙwayoyi na maganin wasu cututtukan da suke iya jawo gaban namiji ya dawo ƙaramin a lokacin da yake amfani dasu. Musamman magungunan Mafitsara, ciwon shuga dss.
6: Taba Sigari: Kamar yadda sigari yake daskarar da ni'imar jikin mace ta zama bata da ni'ima sosai. Haka shi ma namiji sigari ke sa gabansa ya ƙankance amma fa inji masana.
Don haka idan namiji yana shan sigari kuma yaga gabansa yana kankancewa, to ya sani sakamakon sigarin da yake sha ne.
7: Sanyi: Shima yana sa gaban namiji ya dawo ƙaramin.
Idan namiji yana yawan sha ko wanka da ruwan da yake da sanyi sosai hakan na iya sa gabansa ya ƙankance.
Shi yasa ko Jima'i mutum yayi da iyalinsa muddin yana so ya ci gaba, kada yayi tsarki da ruwan sanyi ya samu ruwan dumi. Haka nan idan gaban namiji ya tsaya cak yaki ƙwanciya yana samun ruwan sanyi ya sha ya yayyafa zai ga ya kwanta.
Ga mazan da suke yin istimina da ruwan sanyi, suma gabansu zai iya ƙankancewa saboda yadda suke zubawa gaban nasu ruwan da yake da sanyi.
8: Kayan Zaki Da Maiko: Idan namiji yana yawaita sha ko cin abubuwan da suke da zaƙi ko maiƙo, gabansa na iya rauni, wannan raunin zai sa gaban namiji ya ƙankance.
#tsangayaramalam
Wadannan sune wasu daga cikin dalilan da suke jawo gaban namiji ya ƙankance a binciken da masana suka gudanar. Don haka duk wani namiji daya fahimci gabansa ya ƙankance, sai ya kula ko daga cikin wadannan abubuwan guda 8 da muka jero su akwai wanda ya masa sanadiyar hakan.
A darasi na gaba zamu kawo hanyoyin da namiji zai bi domin gabansa ya dawo yadda yake, girma da kauri. Amma kamin nan. Ga tambaya. Ko akwai magungunan da suke karawa gaban namiji tsawo da kauri?
Mu hadu a darasi na gaba domin amsar wannan tambayar.
0 Comments