Wasu Dabaru Guda 6 Na Sace Zuciyar Masoyi Da Mata Basa Amfani Dasu


Wasu Dabaru Guda 6 Na Sace Zuciyar Masoyi Da Mata Basa Amfani Dasu:

#Tsangayarmalamtonga 
Bisa al'ada, mutum yana saurin gajiya da wanda yake kusa da shi. Mukan yawan maimaita darasin nan ne ganin yadda mata suke bukatar sa.

Haka nan kullum mutum yana kokarin jawo na nesa da shi ne ya kusance shi idan kuma yazo kusa da shin, sai ya ajiye shi ya sake nemo wani.

Wannan shine misalin halin maza. Saura tari mutum yafi sha'awar mutumin da bai cika bashi lokaci ba akan mutumin da kullum yana tare dashi. Shi yasa ake samu namiji na mutuwar son mace amma hankalinta yana wajen wani can da bai ma damu da ita ba. Haka suma mazan da zaran sun ga mace na mutuwar sonsu to itace abun wulakantawa.

Ga wasu dabarun guda 6 nan da zaki gwada idan har kina son yin mutuncin a idanuwan namijin dake sonki da auren.

1: Jinkirin Wajen Daukar Wayarsa Da Tura Masa Sakonnin: Ki rage rawan jiki wajen saurin daukar wayar namijin da kike son cusa masa soyayyar ki a ransa. Haka nan idan ya tura miki text kina gani shareshi ciki gaba da aiyukan gabanki sai can ki amsa.

Koda kice kika kirashi kuna tsakiyar hira katsai wayar ki yi zamanki ya kira kamar sau uku haka kamin ki sake dauka.

Ki daina barin kuna goduwar hira a waya ko a text yadda har sai shi da kansa ya gaji. Ki dauko labari mai dadi sai kawai ki share shi.

2: Ki tabbatar duk safiya Allah kece kike tashinsa ta kira ko Kuma tura masa sakon text na fatan alheri.

Haka nan idan rana tayi, ki kirashi ko masa text domin jin yadda yake a wajen karatu, aiki ko kasuwanci, ko ma sana'a. Kuma da zai kira kada kiyi doguwar labari da shi domin wannan lokacin yanada mahimmanci a rayuwarki ke da shi.

#nasiha 
3: Kada Ki Amsa Gayyatarsa: Matakin farko na zunda mutuncin mace wajen mai sonta da aure shine amsar gayyatarsa zuwa gidansa, yawon shan iska. Duk yadda namiji yake sonki ya fahimci zai iya fita dake duk inda yake so da yadda yake so mutuncinki zai ragu a gunsa duk darajarki. Hakan kuma duk iskancinki kika ki amincewa da hakan zai mutuntaki.

4: Mannewa Namiji: Ku guji mannenwa namiji idan bashi ba rijiya. Ko idan kullum baki ganshi ba bazaki iya bacci ba. 
Ki rika masa tsadar gani da kusanta ta haka ne zai sa kiyi daraja a idanuwansa ba wai manne masa ba.

5: Nuna Masa Matukar So: A duk lokacin da kuke tare ko kuke nesa nuna masa kina kaunarsa. Kuma a shirye kike da ki aureshi. Amma kina iya hakura da shi idan hakan ya kama ba matsala bane. Wannan zai sa ya rika miki rikon mutunci.

6: Guji Abun Hannunsa: Da zaran kin guji abun hannun mai sonki da aure Zaki yi matukar mutuncinsa a idanuwansa. Amma da zaran kin zama mai yawan bani bani da tambaya. Tunnaninsa na kwarai zai iya sauyawa game dake.

#Tsangayarmalamtonga 
Namiji, yana nuna masa soyaya na gaskiya ne bayan aure ba kamin aure ba.
Kamin auren akan daura tunanin namiji ne akan shakku, da zumudin son ganin abunda nan da yake rufe ake kwadaita masa amma ba a mika masa kaf kamin lokacin da zai bukaci abun ba.

Post a Comment

0 Comments