Wasu Abubuwa Guda 10 Da Suke Sa Saurin Namiji Zuwan Kai:
#Bincike
Saurin zuwan kai ga maza matsala ce da muka sha yin bayaninsa a darusan mu da dama.
Matsala ce da magidanta maza da dama suke fuskatarsa wanda hakan na matukar shafar Zamantakewar auren su.
Shi dai wannan matsalar saurin zuwan kai ga maza a lokacin saduwa da matansu. Masana sunce basu gano hakikanin abubuwan da suke haddasa hakan ba. Amma dai a nasu binciken sun gano wasu daga cikin dalilan dake iya sa namiji zubarwa kamin ma ya Kai ga shiga matarsa ko kuma idan ya shiga cikin kasa da mintuna biyu har ya gama.
Ga wasu dalilan da masana suka gano suke jawo saurin zuwan kai ga maza kamar haka:
#bincike
1: Rashin gudanar da Jima'i akai akai.
2: Zakuwa kamin soma Jima'i.
3: Doguwan wasannin motsa sha'awa.
4: Rashin kwanciyar hankali.
5: Gajiya.
6: Rashin Son wacce ake saduwa da ita.
7: Raunin azzakari.
8: Fama da cutuka irinsu, hawan jini, ciwon shuga dss.
9:Abnormal hormone: Rashin daidaito sinadarin hormone a jikin mutum.
10: Yawan Ni'ima a tare da mace
#Tsangayarmalamtonga
Wadannan suna daga cikin abunda nazari da bincike suka gano suke saurin sa maza zuwan kai da wuri.
Ita mace tana bukatan mintuna 5 zuwa 20 karancin lokacinda yake dumama mata jiki kamin tayi zuwan Kai. Don haka duk wani saduwa kasa da wannan mintuna da mace yana da wuya mijinta ya iya gamsar da ita ta shigan azzakari cikin farji.
0 Comments