SLEEP APNEA
MIN SHARI LOKACIN BACCI
SHIN KO KUNSAN MAFI YAWA MASU FAMA DA WANNAN MATSALAR MUTANE NE MASU KIBAR JIKI??
Minshari lokacin bacci ko gurnani kaji mutum na fitar da nushi Mai karfi Wanda mafi yawa masu wannan matsalar basusan suna aikata wannan lokacin baccinsu ba. Matsala ce wacce takeda saukin magancewa Kuma a rabu da ita.
Yin minshari lokacin bacci na daga cikin wasu matsalolin da ake Samu Kuma abun ya damu wasu ko abokan zama kama daga Magidanta, iyali da abokan aiki, musamman idan aka samu Kai cikin tsoro. Ba kowane abokin zama kejin dadin zama da Mai wannan matsalar ba.
Ga kadan daga cikin ababen dake haifar da wannan matsalar ta Minshari lokacin bacci.
1- Weight Loss: YAWAN KIBA, daga lokacin da MUTUM jiki yazo Masa zai iya haduwa da wannan matsalar ta Minshari lokacin bacci. Yawan kina Yana sa mutane yin minshari.
2- Stop Smoking: Shan Hayaki Anfani da taba sigari da duk wani abun Hayaki ka iya haifar da wannan matsalar ta Minshari lokacin bacci sanadiyar accumulation na fluid a throat mafi yawa Yana haifar da inflammation in the upper airways daga karshe lokacin bacci mutum yayita gurnani
3- Avoid the Intake of Alcohol and Sedatives: Shan Giya ko anfani da kayan maye, idan mutum ya hadu da muguwar dabi'ar Shan Giya ko kayan maye Lokacin bacci zai iya samun matsala wajen fitar da iska da Kuma shakar sa ya zama mutum na gurani ko Minsharin bacci.
4- Avoid Drinking Caffeinated Beverages: Anfani da duk wasu drinks wadanda suke dauke da Caffeine na daga cikin ababen da zasu iya haifar da wannan matsalar ta zama mutum yakasa yin bacci daidai daga karshe ayita gurnani lokacin bacci.
5- Avoid Heavy Meals: Yawan cin abinci ko cimaka, daga anci abinci a kwanta Yana taimakawa wajen sanin wannan matsalar ta Minshari lokacin bacci, Dan Haka ba a bukatan mugun ci lokacin bacci Yana Hana samun inagantaccen bacci.
Stick to a Sleep Schedule: Samun yin bacci lokacin daya dace, idan mutum baya bacci lokacin da ya kamata Yana taimakawa mutum idan yazo baccin ya rika Gurgani ko Minsharin bacci, Dan Haka wajibi ne kowa ya Samar da schedule na bacci wa kansa akan kowane aiki da mutum yake.
Allah yasa mudace
Kabir Yusuf Danwurin Dutsi
0 Comments