Mata Zallah : Maganin Ciwon Mara Na Mata

Mata Zallah : Maganin Ciwon Mara Na Mata
Kamar yadda nayi rubutu dazu game da wadannan magunguna da muke kawowa da kuma wanda ake so mu kawo wasu sunyi tambaya game da na ciwon mara na mata to gashi nan.

   Wannan ciwo kusan yana addabar mata da yawa ‘yan mata da matan Aure kusan wasu duk lokacin Al’ada idan zata zo suna yawan samun ciwon mara wasu ma Al’adar tasu tana rikicewa ko jinin ya rika zuwa kadan kadan ko yazo yaki tsayawa.

To duk mai fama da irin wannan damuwa insha Allah indai aka bi wannan hanya insha Allah zaa samu waraka.

ABINDA ZAA NEMA:

1. Garin Habbatussauda 🥬
2.Garin Tafarnuwa 🧄
3. Garin Zogale 🌿
4. Garin Kusdul hindi 🍵

YADDA ZA'A HADA:

Zaa samu gatin kowanne kamar chokali 5 sai a hade waje daya a rika diban chokali 1 ana dafawa da ruwa kofi 2 idan ya dawu sai a sauke a tace a sha kofi daya safe daya yamma,zaa iya saka zuma ko sukari kafin a shah.

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN PERIOD
MATA KUNA YAWAN YIMAN COMPLAIN AKAN CIWON MARA LOKACIN PERIOD. GA MAGANIN.
🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉

Mafiya yawa daga cikin mata na kuka da ciwon mara wanda kan hanawa wasu rawar gaban hantsi. So dayawa xakaga mace na xullumin tsayuwar wata domin tasan irin axabar datakesha duk adalilin ciwon mara. Ciwone dakan tsananta agurin wasu yakuma galabaitar dasu wasuma har amai xakaga sunayi yayin da wasu numfashinsu ke dauke yakaisu ga suma.

 La'akari dahakan yasa nima nafadada bincike domin kawo ma 'yan uwa mata wasu daga cikin hanyoyin daxasubi dan ganin Allah yasauwake yakuma basu lafia. 

1.kisamu dabino masu kyau sabbin tsinka guda bakwai, kici dasafe kafin kici komai.

🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯

2.kisamu xogale kadan da tsamiya kisa akofi, sannan kisamu tafasashen ruwa kixuba akofin idan yadan huce kishanye a lokacin.

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
 Kiyi haka har sau uku. Insha Allahu xaki samu sauki.

3.kisamu dauwa kamar rabin mudu kijikata akwano natsawon kwana biyu sannan ki mutssiketa kitace sannan kisha.

 Yana maganin ciwon mara sosai yanakuma tsinka jini gawadda ciwon yadameta jini baixoba idan dai tai hakan jinin xaixo
ciwon yayi sauki. Allah yabama masu fama da wannan matsalar lafiya ameen. Domin Karin bayani zaa iya nemanmu tawannan number

FA’IDODIN HABBATUS SAUDA (3)
**********************************
💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
12). Binciken Manyan Likitocin zamani ya tabbatar da cewar: Habbatus Sauda tana Qarfafa Garkuwar Jiki. don haka ana kyakyawan zaton cewar masu fama da chutar AIDS idan suna amfani da ita (mai ko gari) zasu samu Qarin lafiya sosai ajikinsu.

Asamu zuma mai yawa (kamar kofi 3) asanya garin H/sauda cokali 7 garin Zaitun cokali 4. Garin zogale cokali 3. Asanya citta da kayan Kamshi aciki. sannan agauraya arika shan cokali 2 safe da rana da yamma kafin cin abinci.

Wannan fa’ida zatayi amfani ga masu fama da cutar AIDS, cutar SIKILA, TYPOID FEVER, etc.

13. Habbatus Sauda tana maganin kurarrajin Baki dana Makogoro idan ana kurkura bakin da ita kuma ana hadiyanta bayan an dumamata kadan.

14. HABBATUS SAUDA tana maganin matsalar TSAKUWAR MARA, APPENDITIXS, da sauransu. idan ana shanta da zuma.

15. Habbatus sauda tana magance matsalar rashin haihuwa. Matar da take da wannan matsalar, ta rika soya ‘ya’yan Habbatus sauda tana gaurayawa da zuma tana taunasu tana cinyewa. Kamar cokali biyu safe da yamma kullum.

In sha Allahu koda tana da dattin mahaifa ko rikicewar jinin Al’ada, komai zai daidaita.

16. Habbatus Sauda tana maganin basur. Idan aka hadata (garinta) da garin ganyen sabara, ana tafasawa ana shan ruwan, Kofi guda kullum da safe.
🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉🧉

Post a Comment

0 Comments