KULA DA FATA A LOKACIN SANYI


Kula da fata a kowane lokaci yana da matukar muhimmanci, sai dai a lokacin sanyi fata tana bukatar kulawa ta musamman saboda yaushi ko yamutsewa da tsattsagewar da fatar kan yi sakamakon busawar iskar hunturu. Ga wasu hanyoyi wadanda za su taimaka wajen kare fata daga tsattsagewa a lokacin sanyi:­-

KULA DA FATA A LOKACIN SANYI

1.==> Shan ruwa mai yawa. Amfanin shan ruwa ga jikin dan adam yana da yawan gaske. Duk da cewa a lokacin sanyi mutane ba su fiye son shan ruwa ba, amma hakan babbar hanya ce wajen taimaka wa fatarsu ta kasance tana sheki tsawon lokacin hunturu. An so mutum ya sha ruwa kimanin lita biyu zuwa uku a rana. Sai dai wannan bai hada da shan shayi ba, a maimakon haka an so mutum ya yawaita shan lemo.

2.==> A yawaita shan kayan itatuwa da kuma ganyayyaki wannan zai sa fata shekki da walwali.

3.==> Idan an tashi wanka a yi da ruwan dumi. Duk da an san cewa a lokacin hunturu ana bukatar ruwa mai zafi musamman idan da safe za a yi wankan, sai dai ya zama wajibi anan a kaucewa yin amfani da ruwan zafi saboda yana haifar da yamutsewar fata da kuma kaikayi. An so mutum ya yi wanka da ruwa marar zafi sosai kuma wanka ya kasance na dan takaitaccen lokaci, ma’ana kada ya wuce tsawon mintuna biyar zuwa goma wajen wanka.

4.==> Ana so a rika yawaita goge jiki ‘scrubbing’ wannan shi zai sa duk wata matacciya da busasshiyar fata ta fita tare da ba wa sabuwar fata wuri don tofowa.
5.==> Shafa mai akan lokaci, mun san yadda jiki yake saurin bushewa saboda kadawar iska. A duk lokacin da aka yi wanka yana da kyau a shafa ma tun a bandaki lokacin da dan ragowar danshi a jikin fatar.

6.==> A zabi mai da ya dace da lokacin sanyi, ma’ana mai wanda ke da maiko wanda zai sa fata ta kasance cikin danshi na tsawon lokaci. Duk wani mai da zai zama ya sa fata tauri ba shi da amfani a wannan lokaci na sanyi. A wannan lokaci amfani da man kadanya ko man zaitun yana taimakawa fata kwarai da gaske.


7.==> Haka kuma akwai bukatar mutum kada ya manta da labbansa da kuma hannuwansa, kasancewar wadannan wurare suna da muhimmaci a jikin dan’adam kuma sanyi yakan yi musu illa don haka akwai bukatar koda yaushe mutum ya kasance yana tare da man lebe da kuma wani mai na hannu mai ruwa-­ruwa.

Post a Comment

0 Comments