Ki Guji Yiwa Gabanki Wadannan Abubuwan Idan Kina son Tsufa Da Lafiyan Farjinki:



Ki Guji Yiwa Gabanki Wadannan Abubuwan Idan Kina son Tsufa Da Lafiyan Farjinki:
💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
#Bincike 🔔
SHARE 📑
A wani darasin a baya mun yiwa mata bayanin ruwan dake fitowa a gabansu akai akai ba abun da zai damesu bane lafiya ne.

Sai dai akwai wasu abubuwan da yawancin mata suke yiwa gabansu da yake musu illa ba tare da sun fahimci hakan ba.

Mata su kula da yin wadannan abubuwan mudin suna son su tsufa suna morar halittarsu.

 
1: Duk mace nason ganin gabanta cikin tsafta. Da kuma kauda wari ko doyin dake iya fitowa a gaban mace.

Hakan yasa wasu matan suke amfani da sabulun dake sauya lauyin fata wajen wanke gabansu da shi. Daga bisani kuma su fesawa gabansu turare ko kuma foda.
Duk macen datake yiwa gabanta hakan, ta sani zata rika jawowa kanta cuta a kullum.

 Hakan kuma zai yiwa gabanta illa inji masana al'uran mata.

Kada ki wanke gabanki da duk wani sabulun da kikasan yanada sinadari mai karfi a jikinsa. Akwai sabulu na musamman da ake sayarwa na wanke gaba na mata.

 Idan kuma baki da halin saye, sabulai marasa sinadari masu karfi zasu iya tsaftace gaban mace ba tare da cutar da kanta ba.

Gaban mace baya bukatar a masa feshin turare ko foda, domin wadannan abubuwan suna kunshe ne da sanadarin da zai yiwa mace illa a gabanta maimakon ya sata kamshi kamar yadda take bukata.

 Don haka ki guji fesa turare ko foda a gabanki domin samawa gabanki kamshi.

 Maimakon hakan kina iya amfani da man zaitun domin shafawa a shatin gabanki ba a cikin gabanki ba. Domin cikin gabanki wannan ruwan shike tsaftace shi ya kuma kare duk wata cuta samun zama a ciki.

2: Jimawa Da Jikenken Wandon: Wasu matan sukan jima da Wandon da sukayi aiki suka yi gumi har gabansu ya jike. Ko kuma suka yi motsa jikin da suka jika gabansu.

Yana da kyau da zaran mace taji wandon dake jikinta ya jike saboda gumi, ko jikewa da ruwa, tayi maza ta cire Wandon domin zama da irin wannan kayan a jikin mace yakansa ta harbu da infection cikin sauki.

3:Yawan Shan Zaki: Mata da dama basusan zaki Yana musu illa a gabansu ba.

Wasu matan sugar da kansa suke zubawa da yawa idan zasu yi amfani da shi. Haka nan wasu matan kamar sha zumamu suke inada zaki.

Yawan shan zaki ga mace yakan sata tusan gaba kamar yadda masa suka tabbatar. Wanda kwayar cutar fungus candida take haifarwa.

Wannan ya nuna idan mace tana yawan shan zaki gabanta yana iya kara fadi da girma yadda idan mijinta na saduwa da ita iska zai rika shiga da fita kamar tusa.

 Hakan na ragewa ma'aurata jin dadin Jima'i da kuma kunyata mace.

4: Wuda Gaba: Akwai matan da suke huda gabansu kamar yadda suke yiwa kunnuwansu, hancinsu da bakunansu domin sakawa gabansu zobe.

Wannan dabi'ar da mata da dama suke yi yakan haifarwa gabansu matsalar kamuwa da cutuka cikin sauki. Bugu da kari kuma fatan wajen ba a yisa domin irin wannan abun ba.

Yana da kyau mata su gujewa huda fatan ganasu domin sawa wajen dankunne.

 Akasarin mata 'yan Madugo da kadan daga cikin wasu matan aure suna sha'awar hakan.

5: Taba Gabanki Da Abu Mai Dauda: Muddin mace tana burin ganin ta tsufa da lafiyan farjinta ta kiyaye taba gabanta idan hannunta bai da tsafta, ko kuma amfani da tsumma mara tsafta domin gyara gabansu. 

6: Saka Matsantsun Wanduna: Ki guji amfani da wandon da yake matsai miki gabanki yadda iska baya samun shiganki da kyau.

Da zaran kayan sun matsai suna iya jikewa saboda gumi. Wanda wannan gumin zai iya jawo miki shigan cuta a cikin gabanki.
Haka mata masu yawan saka wandunan jeans 👖 Matsantsun na iya jawo musu matsala.

Shi wannan wajen naki yana bukatar iska a kowani lokaci ba matsi ba. 

7: Turara Gaban Ki: Mata da dama sunada al'adar turara gabansu da hayaki. Wannan dabi'ar ba karamin yiwa gaban mace illa yake yi.

Mata da dama da suke da matsalar bushewar gaba, na rashin ni'ima na faruwa ne a sakamakon raunana sinadarin dake sakon ruwa a gaban mace kamar yadda ya dace. 

Gaban mace baiwa yake dashi na tsaftace kansa da kansa da kuna yiwa kansa kariya. Duk wani hayaki da zaki turarawa gabanki illa ne a wajenki amma babu wani amfani mai dorewa da zaki samu na aikata hakan.

8: Yawan Canza Kunzugu: Ki tabbatar da cewa kina yawan sauya kunzugunki akai akai a lokacin al'adar ki.

Hakan yakan hana cututtuka shigan gaban mace cikin sauki.

#Tsangayarmalamtonga 
Wadannan wasu abubuwa ne da mata suke yawan aikatasu da suke musu illa a rayuwansu.

Ya kamata mata su fahimci cewa, lafiyan farjinsu shine lafiyan zaman Aurensu.
Da fatan za a kiyaye.
👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗👗

Post a Comment

0 Comments