Illar Rashin Koya Wa ‘Ya’ya Mata Girki Tun Daga Gida:



 

Illar Rashin Koya Wa ‘Ya’ya Mata Girki Tun Daga Gida:

Har yau dai shafin namu zai tabo batun rashin iya girki ne da mafi aksarin mata ke tafiya da shi har gidan miji. Wasu iyaye mata kan kyale yara mata ba tare da nuna musu shiga kitchen ba, wanda har ayi auren yarinya bata iya komai da ya shafi girki ba, hakan babbar matsala ce dake iya rikidewa ya koma kalubale a rayuwar aurenta.

Yana da kyau iyaye mata su dora yara mata akan dai-dai a komai na rayuwa, domin a samu cigaba a cikin al’umma. Idan uwa ba ta iya ba to haka ‘ya ma za ta tashi ba ta iya ba, da haka za ayi ta tafiya matsaloli na kara yawa cikin rayuwar aure. Iyaye mata su koya wa yara duk wani aiki da ya shafi harkar girki tun suna da kananun shekaru daga shekaru sha biyu a takaice, akwai wadanda ke fara koyawa yaransu kasa da wannan shekaru.

Idan yarinya tana makarantar boko a koya mata, shiga kitchen yin wasu ayyuka bayan ta dawo kamar dora miya, dora tuwo da sauransu. Wasu iyaye mata kan ba da hankali wurin sana’ar yara mata wanda bai shafi dafa abinci ba, hakan kansa har ayi auren yarinya bata iya komai ba. Saboda haka ko da a ce yarinya tana zuwa makaranta, wurin koyon sana’a, da ma wani wuri dabam to yana da kyau a ware mata lokacin shiga kitchen don ta koyi girke-girke da abin sha, wanda ya kama da kalolin juices da kuma kalolin yadda ake dama kunu, ba ta koyi dafa abinci ba, bata iya abin sha ba, yana da kyau koyarwar ya tafi duka bangarorin.



An sha samun matsaloli, ana kuma cigaba da samun matsala a ko da yaushe musamman a fannin girki wanda har yana jawo mutuwar aure ko karin auren maigida saboda rashin iya girki. Iyaye mata a kula sosai wurin kulawa da bangaren girki ga yara mata. Tsabtace kitchen kafin fara dora abinci, saboda gujewa datti ko wani abu shiga cikin girkin. Musamman ranakun asabar da lahadi iyaye mata su kasance tare da yaransu mata akan dukkanin ayyukan abinci da za su yi, idan yarinya ta shiga gidan miji ba tare da ta iya girki ba, to wannan tabbas laifin mahaifiyarta ne.

Mata mu kula.


Post a Comment

0 Comments