Wasu Dalilan Dake Sa Wasu Mazan Karin Aure:


Wasu Dalilan Dake Sa Wasu Mazan Karin Aure:


 
Duk da halalcin da yin mata fiye da biyu yake da shi a tsari na addinin islama, ba duk maza Musulmai bane suke da sha'awar auren mace fiye da guda ba. Wasu mazan karin auren yakan zo musu ne a babu yadda suka iya, yayin da wasu kuwa suna maida aure abun wasa. Wasu mazan sun tsani yin aure su saka, mai makon hakan sai kawai su kara wani auren idan suka fahimci wanda suke dashi a yanzu akwai takura ko cutarwa. Kamin ka zargi namiji akan karin aure, ka fara sanin dalilin daya sa zai kara ko ya Kara tukun. Ga wasu dalilan da ke sa wasu mazan suke kara aure domin zama da mace fiye da guda. 


1: Rashin Godiya:

Akwai wasu matan duk abunda mazansu zasu musu na kyautatawa bazasu taba nuna godiyarsu da kokarin mazan ba. Sai ma nuna musu gazawarsu ta nuna abunda akayi da ba hakan aka yi musu ba.

Nunawa mutum godiya yana daya daga cikin rukunin abunda Allah Yake so a masa a lokacin da yayiwa mutum wani kyauta. Hakan shi ma mutum yana so a duk lokacin da yayi abun bajinta a yaba masa domin gaba yaji dadin kara yin fiye da hakan.

Wasu mazan ta hanyar da suke ganin zasu huce takaicin rashin godiyan da matansu ke masu shi ne ta hanyar kara wata matan.

2: Almunbazzaranci:

Akwai matan da duk irin tanadin da maigida zai yi a gidansa na kudi, kayan abinci da sauran abubuwan sai sun wulakanta su wasu ma ktautarwa suke yi ba tare da amincewar miji ba.

 Tabbas irin wadannan matan na matukar hasala mazansu su har daga bisani suka mafi sauki shine sake auro wata da zata kular masa da abubuwan da zai bari a karkashin kulawar ta. 

3: Tsiwa:

Akwai matan da muddin kana tare dasu bakada kwanciyar hankali har sai lokacin da ka baro gida. Haka idan zaka koma gida gabanka na faduwa saboda yawan masifansu, tsiwa da mita. 

Hakan yake sa mazan da suka samu kansu tsumdum da auren irin wadannan matan dole yake sa su kara wani auren domin samawa kansu lafiya. 

4: Rashin Sirri:

Akwai matan da duk halin da miji yake ciki na walwala ko kunci basa iya sirrantawa. Ko wani ajiya aka basu na magana ko kudi sai sun yayata. Wannan ke sa mazansu su yanke shawaran karo wani aron da zasu rika adana sirrukansu na yau da kullum anan.
 
5: Tara Abokan Banza:

Akwai matan auren da suka gwammace da su rabu da kawayensu gara aurensu ya mutu. Irin Wadannan matan duk yadda ka tsara gidanka wadannan kawayen sune zasu rusa ta hanyar nunawa matarka yadda ya kamata tayi. Irin wannan sau tari na tunzura wasu mazan su karo wani auren kamin daukan mataki na gaba.

6: Rashin Lokaci:

Akwai matan da basu da lokacin mazansu bare ma na yaransu. Irin wadannan matan aiyukansu ko sanaoin su kawai sune suka saka a gaba amma ba kula da miji ko gida ba. 

Hakan shima dalili ne dake sa wasu mazan suke kara wani auren domin ganin sun samun matar da zata rika kula da bukatunsu na gida.

7: Neman Haihuwa:

Akwai matan da Allah bai basu haihuwa ba. Ta dalilin rashin lafiya ko kuma dai haka nan. Ganin matan da suke tare bazata haihu ba, sai su yanke shawaran karo wani auren ko zata haifa masa yara.

8: Rashin Tsafta Ko Iya Girki:

Duk kokarin da ake yi domin ganin sun gyara basa gyrawa. Akwai matan da mazansu kunya suke ji su kai abokansu gida domin cin abinci saboda kazantar matar gidan da kuma rashin iya girkinta.
Hakan daga karshe idan mazan suka fahimci mafita shine karo wata macen, sai aga sun kara wani auren saboda wadannan dalilan.

9: Rashin Mutunta Mutane:

Maza sun sha kara aure saboda yadda matan da suke aure basa iya mutunta 'yan uwa, abokansu a duk lokacin da suka kawo musu ziyara.

Wannan dalilin yasa maza da daman gaske sunyiwa matansu kishi ya domin amfani da lokacin amarya ko gidan wacce aka karo wajen inda zasu rika kai yan uwansu ko abokan huldarsu.

10: Rashin Gamsarwa:

Maza suna iya kara aure a lokacin da suka fahimci macen da suke aure bata iya gamsar dasu ko kuma bata ma iya kwanciyar auren ba.

#tsangayarmallamtonga 
Da fatan mata zasu gyara domin su takaita sa wasu mazan kara aure basu shirya ba.

Post a Comment

0 Comments