LOKACIN BINCIKE DANGANE DA MAGANAR AURE:



Bincike ginshiki ne mai muhimmanci dangane da maganar aure, musamman ma a irin wannan zamanin namu da lamarin mutane sai a hankali, rashin gaskiya, cin amana, sukurkucewar tarbiyya duk sun yi katutu a tsakanin al`umma.

Ga shi kuma al`ummar sun yi yawa, hanyoyin kulluwar alaka rututu, duniyar kuma an dunkule ta a hannu, don haka za ka ga an kulla alakar soyaiya tsakanin mutanen da suke rayuwa a nisan duniya, wurare mabanbanta.

Irin wadannan dalilai na dada karfafar bukatar yin kyakkywan binciken kwakkwafi kafin a amince a ba wa namiji auren `ya, kamar kuma yadda shima namijin yake da bukatar yin cikakken bincike game da yarinyar da yake son aura, domin kada ya dakko kara da kiyashi, ko ya kwaso ruwan dafa kansa, ko alakakai.

Da yawa muna jin labarai cewa wadansu mazan an ba su `ya aure, sai bayan sun hayaiyafa da ita, sannan sai su gudu, ko sama ko kasa, ba a san inda suka yi ba, kuma daman ba a san garinsu ko danginsu ba. Akan kuma samu wani namijin yana auren mata fiye da daya, ya saka su a gidaje daban daban, ko wacce ba ta san da zaman `yar uwarta ba, ko ka samu mutumin da aka ba wa `yar aure auri-saki ne. Ashe irin wadannan labarai kadai ba su isa su nuna mana muhimmancin tsananta bincike kafin a aurar wa da mutum `ya ba ? Ashe ba suna nuna yadda wasu iyayen suke yin sakaci wajen ba da `ya`yansu aure ba? Ko kuma dai iyaye neman kai suke yi da `ya`yansu mata ne ?

Ni ina ga da in ba da `yata aure a samu irin wadannan matsaloli da na zaiyana, ko a samar min da `yar karamar bazawara a gidana sakin wawa, gara a bar min `yata a gabana, ko ba komai tana gaban uwarta da ubanta da suka san kimarta ne, kuma ta cigaba da neman ilmin addini, da koya wa kananan yara karatun islamiyya.

Duk da kasancewar wadansu iyaye sukan yi iya nasu kokarin wajen yin bincike kafin su bada `ya`yansu aure, abin tambaya a nan shine: Wane lokaci ne ya kamata a yi binciken ? Me da me ya kamata a bincika ? Wanene zai yi binciken ? Wane bangare za a bincika; macen ko namijin ? Da wane ma`auni ya kamata ayi binciken ?

Irin wadannan tambayoyin su za mu yi kokarin amsawa a kashi na gaba insha`allah !

Wane lokaci ne ya kamata a yi binciken ? Me da me ya kamata a bincika ? Wanene zai yi binciken ? Wane bangare za a bincika; macen ko namijin ? Da wane ma`auni ya kamata ayi binciken ?

TAMBAYA (1) WANE LOKACI NE YA KAMATA A YI BINCIKEN ?

AMSA:- 

Da farko dai kafin amsa tambayar, ya kamata mu fara duba dalilin da ya sa ake bukatar yin bincike kafin a yi aure, ina ga kuma ba zan zama na yi karya ba, idan na ce manufar ita ce a kauce wa fadawa halin nadama, da sanin cancantar wanda yake son kasancewa abokin zama ga kai kanka, ko ga wani naka, ko kuma kai kanka kake so ya kasance abokin zama gare ka.

Idan kuwa wannan dalilin da na ambata ya samu shiga, to babu lokacin da ya kamata a yi bincike irin tun kafin a ba wa mutum damar zuwa neman yardar yarinya, idan kuma kai ne mai nema kafin ka gabatar da kanka gare ta, idan kuma ke ce yake neman yardarki, kafin ki ba shi dama ya fara zuwa wajenki.

Daukar irin wannan mataki shi zai sa idan har ba a gamsu ba, shikenan daman ba a samu shakuwa ba, ballantana har a shiga kakanikayin neman yadda za a yi a dakatar da shi, ko kuma a cire shi daga zuciya, ko ka gamsar da nakan rashin cancantarsa gare shi, ko kuma yunkurin fita daga komarsa.

Idan kuma binciken ya ba da kyakkyawar natija, ya zama ke nan an fahimci muhimmancin mutumin, da nagartarsa, da kuma cancantarsa gare ka, ko gare ki, ko ga abin walicin naka, ko makusancinka, za kuma a rike shi kam-kam, a kuma fahimci cewa ba a yi zaben tumun dare ba, sannan hakan ya saka nutsuwa a zukatan juna, da waliyyansu, da ma duk wani makusancinsu, ko mai kaunarsu.
Jinkirta yin bincike har zuwa lokacin da mutum ya nemi turo magabatansa, shi yake sa wa ko an gano matsaloli za ka ga ana ta tataburza da yarinya, ta shiga yin fito-na-fito da iyayenta, tunda namijin ya riga ya samu gindin zama a zuciyarta, ko macen ce ta samu gindin zama a zuciyarka.

 Shi kuwa so idan har ya kutsa cikin zuciya, ya samu zama, to wannan zuciyar za ta koma ne kurma, bebiya, makauniya game da wanda ta kamu da son nasa, sai dai fa wacce Allah ya ketarar, ita ce takan dan samu kanta a cikin haiyacinta, irin kuma wadannan zukatan kadan ne. Ina ga kuma wanda bai fahimci dangantakar soyaiya da zuciya ta yadda na zaiyana din nan ba, to bai san mecece soyaiya ba, sunanta kawai yake ji. 

Don haka shi so matukar ana son yakar sa, a kuma samu nasara a kansa, to kada a bari ya samu gurbi a inda bai dace ba. Babu kuma yadda hakan zai yiwu sai idan an yi kyakkyawan bincike a lokacin da ya dace, watau tun kafin a bude masa kofa, har ya kutso kai cikin zuciyar da ya nufa.

Hakan kuma zai taimaka wajen rage yawan mayaudara, masu bata `yanmata, da samari `yan lobaiya babu sisin yin aure, da zawarawa masu yin aure domin su samu kayan sallah da hidimomin azumi, kamar kuma yadda zai kare iyaye da `ya`yansu daga fadawa tarkon mazaje masu auri saki, insha`allahu.

A kashi na gaba kuma za mu yin kokarin amsa tambaya ta biyu insha`allahu !



:WANE LOKACI NE YA KAMATA AYI BINCIKEN ?

 A wannan kashin insha`allhu za mu yi kokarin amsa wadannan tambayoyin ne na gaba, kamar haka:-

Me da me ya kamata a bincika ? Wanene zai yi binciken ? Wane bangare za a bincika; macen ko namijin ? Da wane ma`auni ya kamata ayi binciken ?

Sai dai kuma a jerin wadannan tambayoyin kamata ya yi a gabatar da wacce ta ke cewa:-

WANE BANGARE ZA A A BINCIKA: MACEN KO NAMIJIN ?

AMSA:-
Duk bangarori biyun za a bincika !
HUJJA:-

Saboda mace da namiji ne za su zauna, kuma dukkaninsu ba wanda ya ke fatan zama cikin matsala, ba wanda ba ya son jindadin zamantakecewar aure, ba wanda ba ya burin abokin zaman da ya cancanta da shi. `Ya`yan da za a haifa suna bukatar iyaye abin alfahari. Iyaye suna son samun surukai na gani na fada, zurriyya tsarkakka. Al`umma tana bukatar iyalai lafiyaiyu, rage sake-saken aure, rage yawan `yan mata da zawarawa. Addini yana bukatar `ya`yan da Manzo(saw) zai yi alfahari da su.

TAMBAYA:-
ME DA ME YA KAMATA A BINCIKA ?
AMSA:-

Abubuwan da za a bincika sune:-
- Addini da aqida.
- Dangi.
- Sana`a.
- Tarbiyya.
- Waliyyai.
- Idan kuma mai mata ne: yanayin zamansa da iyalinsa.
- Idan bazawari ne/ bazawara ce ta dalilin saki : abin da ya raba shi/ta da tsohuwar matarsa/tsohon mijinta.
- Idan bazawari ne/bazawara ce ta dalilin mutuwa: dalilin rasuwar tsohuwar matarsa/tsohon mijinta.

FASHIN BAKI:-

- Addini: Akwai bukatar a san menene addininsa da kuma yadda yake gudanar da shi, domin za a iya fadawa hannun kirista da ya yi ungulu da kan zabo, ko musulmi wanda yake yi wa addininsa rikon sakainar kashi, ko mai gurbatacciyar akida, ko akidar da hukuncinta ridda ce, da dai abubuwan da ba su dace ba masu kama da wadannan. Yin bincike ne zai taimaka wajen tsira daga fadawa hannun wadanda aka lissafa a sama.

- Dangi: Za a yi bincike ne game da: su wanene dangin mutum, domin zai iya zama mai gurbatacciyar nasaba, ko kuma idan ba a san su ba, ya iya guduwa ya bar matarsa da `ya`ya, ko a samu afkuwar mutuwar katsahan, wanda idan abu mai kama da haka ya faru, kuma ba a san danginsa ba, ya zama ke nan yara ba su da dangin uba, ko kuma a ce ba a san su ba, kuma hakan wata rana bayan sun girma, na iya zama abin gori gare su, ko wani abu mai kama da haka, musamman ma idan sun je neman aure, ko aka zo neman aurensu.

- Sana`a: Akwai bukatar sanin sana`ar mutum, domin wata kila dan buge-buge ne, babu wata takamaimai din sana`a, ya kukuta ne ya yi aure, daga baya kuma ya kasa rike yarinya cikin dan karamin lokaci, ko sana`arsa ta haramunce, a addinance, ko a dokar kasa, ko ma duk biyun, ko daman ma ya gina komai ne akan karya, rigar da yake sawowa da abin hawan da yake zuwa da shi duk na aro ne, idan haka ne kuwa matukar an yi bincike lokacin da ya dace, tuni za a harbo jirginsa.

- Tarbiyya: Ita ce jagoran mutum a rayuwa, ta yadda idan kyakkyawa ce, za ta tsare faruwar da yawa daga matsalolin da aka lissafo a sama. Ma`ana mai ita, za a same shi da riko da addini, da wuya ya boye su wanene danginsa, zai yi wahala ya gudu ya bar iyalinsa, zai yi sana`a ne tsaftatta, ya kuma tsaya iya matayinsa, ba karya, ko ungulu da kan zabo. Amma idan har babu tarbiyya ba zai damu da rabe halal da haram ba. Ita kuma mace mai tarbiyya ita za ta zamo uwa tagari, ta samar da zurriyya tsarkakka, saliha, abar buga misali, sannan kuma ta taimaka wa namiji wajen cin ma nasara a rayuwa, idan kuwa babu tarbiyya, to komai ba zai tafi daidai ba.

Waliyyai: Akwai bukatar sanin su waye waliyyan mutum ? ya suke da shi ? Su kansu ya dattakunsu ya ke ? Sun isa da shi, ko ba sa gabansa ? Dukkan wadannan tambayoyi sun shafi mace da namiji, kuma tasirinsu zai baiyana ne lokacin da aka samu sabani tsakanin ma`aurata, domin harshe da hakori ma ana samun sabani, ina ga wadanda suka tashi daga wurare mabanbanta, to a wannan lokaci ne kyakkyawan zabi na surukai zai baiyana, kuma dai kamar yadda muka sani a musulunce, walici na maza ne, idan ya fada hannun mata kuwa, tafiyar za ta iya samun cikas, ko wani tasgaro.

- Idan mai mata ne: Wanda ya zo neman aure, aka kuma yi sa`a daman yana da mata, to abin ya fi zuwa da sauki, domin komai nasa a baiyane ya ke, sai dai kuma idan an yi sakacin yin bincike game da shi, ta a nan kuma laifin wadanda nauyin yake kansu ne. Kamata ya yi a bincika yadda yake tafiyar da gidansa, idan an gamsu a yi da shi, idan ba a gamsu ba, ya kama gabansa. Amma matukar ba ya kyautata wa iyalinsa, to ko ma ku ya nuna muku kirkinsa, to gaskiya na jabu ne, idan kuma aka fada komarsa, to nadama ce za ta biyo baya, sai dai ko idan an tabbatar cewa rashin kirkin daga iyalin ne, ba kuma ta hanyarsa za a gano hakan ba.

- Bazawari/Bazawara wanda saki ne dalili: Su wadannan za a bincika abinda ya kawo rabuwarsu da abokanan zamansu ne, domin gano cewa ko suna da wani mugun hali ne, ko laifin na wancan abokin zaman ne, ko kuma kuskuren fahimta aka samu, ko dai sanadin kaddara ne, ko kissar abokiyar zama, ko tsana daga uwar miji, ko zafin kishi, ko dai dalilai da dama da ka iya kawo rabuwa.

- Bazawari/Bazawara ta dalilin mutuwa: Suma wadannan za a binka bangarori biyu ne; sanadiyyar mutuwar abokin zamansu, da kuma halinsa lokacin da suke tare da abokin zaman. Na farko don a sani mutuwar ta sanadin hadari ne, ko kuma rashin lafiya ? Idan rashin lafiya ne, ciwon wanda ake dauka ne, ko kuma ba a daukar sa ?.

 Na biyun kuma za a yi bincike ne game da zamantakewarsa da abokin zaman lokacin da yake raye, wata kila daman zaman hakuri abokin zaman nasa ya ke yi da shi, sai kuma ta Allah ta kasance, wata kila ma takaicinsa ne ya haddasa mutuwar abokin zaman nasa.

Duk da kasancewar shi aure yana tare da kaddara, amma wata kaddarar an rataya ta ne da zabinka, ko kuma yanayin yunkurin da kai ka yi daga bangarenka. Amma dai ko ba komai bincika abubuwan da muka zaiyano, ka iya raga fadawa ni `yasun da yawancin wasu ma`auratan ko rayuwar auren suke samun kansu a ciki.

Insha`allahu a kashi na gaba za mu dora amsoshin tambayoyin da suka rage.

ARASHI:-

Ina cikin yin wannan rubutun ne, yau din nan Laraba 18/1/2017, da kimanin karfe 9:00 na safe, sai na ji wani rahoto a filin ``KU KARKADE KUNNUWANKU `` na Rahama Radio da ke birnin Kano. Yadda rahoton ya ke shine: ``Wata amarya ce aka sako muryarta tana kuka, wai angon da ta aura ya saka mata cutar alakakai.( HIV ) Sai kuma masu rahotan suka ce: daga baya ma sun samu rahoton cewa, angon mai dabi`ar auri-saki ne, kawai saboda giyar kudi``.

Shine a raina nake cewa: wannan rahotan ya zama arashi, domin yana karfafar abinda muke magana a kansa; yin kyakkyawan bincike kafin a ma ba wa mutum damar neman amnicewar yarinya.

Sai kuma wani abu da rahoton ya dada jaddada mana:

 MUHIMMANCIN YIN GWAJI(TEST) KAFIN AURE.

 Wata kila da wadannan mutanen sun yi, da amarya ba ta gamu alakakai din ba


(i) WANE BANGARE ZA A A BINCIKA: MACEN KO NAMIJIN ?

(ii) ME DA ME YA KAMATA A BINCIKA ?

A wannan kashin kuma insha`allahu za mu amsa ragowar tambayoyi biyu da suka rage mana game da wannan batun. Tambayoyin sune:

Wanene zai yi binciken ? Da wane ma`auni ya kamata ayi binciken ?

AMSA TA DAYA:-

Ina ganin amsar wannan tambayar a baiyane take, sai dai kawai a yi domin tunatarwa.

Game da wanda zai yi bincike za a iya raba abin gida uku kamar haka:-

1. Namiji mai neman auren.
2. Budurwa wacce ake neman auren nata.
3. Bazawara da ake neman aurenta.

1. Namiji shine jagoran gida, igiya da linzami a hannunsa suke, kuma yana da damar shiga da fita ko da yaushe, kamar yadda ya ke da damar kutsawa duk sako da lungun da yake so, don haka, game da bincike akan matar da yake burin aura aikinsa ne, shi zai tashi kafa da kafa ya je inda yake zaton zai samu bayanan da yake son sani game da ita. Ba laifi idan ya wakilta wani aminin nasa domin ya tattaro masa bayanai, sannan kuma wajen neman bayanan ya tabbatar da cewa ya san dangantakar mai ba shi bayanin da wanda yake neman bayanin a kansa, saboda hakan ne zai ba shi damar nazarin bayanan da ya tattara, da kuma irin karbar da zai yi musu. Abinda ya sa na fadi haka saboda a wannan zamanin namu harkar jama`a sai an yi hattara, wani ka iya ba da bayanai na son zuciya, duk da dai cewa saka Allah a gaba, da tsarkake niyya ka iya shiryar da mutum zuwa ga mutanen da suka dace, da kuma ingantattun bayanan da ake bukata, don haka sai a kara da addu`a.

2. Budurwa wacce ake neman auren nata: Ita wannan saboda yanayin zamani za a iya raba su gida biyu dangane da shekarunsu:

a. Daga shekara 0 har zuwa 24.
b. Daga shekara 25 zuwa sama.

Abinda ya sa ita ta farko aka fara da kasa da shekara 1, saboda a al`ada wata yarinyar tun ba ta yi shekara ba iyaye suke kulla alkawarin hada ta auren zumunta da wani dan nasu, to dangane da wannan kason, akwai dalilai biyu da za su sa a ce waliyyanta ne za su yi wo mata binciken da duk ya dace game da mai neman aurenta, ko wanda ake son hada su tare da shi:-

(i) Rashin gogaiyar rayuwa.
(ii) Kasancewarsu mata.

Dalili na farko yana tabbatar da cewa kuruciya da rashin gogaiya ba za su ba su damar hango nesa yadda ya dace ba, don haka su zakin soyaiya, sha`awa, tashen balaga, da dokin yin aure sune za su rufe idanuwansu, zuciyarsu da tunaninsu, ba za su fahimci manufar aure, da abinda zaman yake bukata ba yadda ya dace, sai fa ana kama hannunsu domin dora shi inda ya cancanta.

Dalili na biyu kuwa yana nuna cewa, kasancewarsu mata, ba ko ina za su iya tunkara ba domin lalubo bayanan da suka dace.

Sai dai kuma a nan kawai za a ce, ya kamata waliyyan su ji tsoran Allah, su dubi maslahar yarinyar, ba maslahar kawunansu ba, tunda akwai wasu waliyyan da su ke gabatar da abin duniya akan komai a yayin da za su aurar da abar walicinsu, wanda hakan ya kan jefa rayuwar auren yaran cikin kunci da rashin jindadi, Allah dai ya kyauta !

b. Ita wannan duk da ba ta taba yin aure ba, shekarunta sun kai ta tantance baki da fari a zamantakewar aure, tana da hangen nesa, ta san abinda zai fi zama maslaha gare ta. Wannan ne ya sa a lokacin da, sanda auren ba ya jinkiri kamar yanzu, irin matan da su ka kai wadannan shekaru ba su fiye sauraron saurayi ba idan ya zo neman aurensu, sun fi fifita mai shekaru da yawa, ko mai mata, sai yanzu ne da auren yake yi wa maza da matan tsauri, har irin wadannan matan suke burin mara aure, amma duk da haka za ka ga sun fi fifita tuzuru ne, ba matashin saurayi ba. Budurwar da take wannan ajin ita ce ya kamata ta jibinci shugabancin lamarin bincike akan mijin da za ta aura, ta hanyar baiyana wa waliyyanta irin suffofin da ta ke so mijinta ya cika, su kuma sai su dauki dawainiyar binciko mata, su kuma rika gabatar mata da bayanan da suka tattaro kai tsaye domin ta tace su, ta kuma dauki matsayi gini a kansu. Dalili shine ita wacce ta kai wannan shekaru, tana da gogaiyar da za ta iya dorar da bayanai akan zamantakewar aure, tunda kusan kawayenta ba adadi sun riga sun yi aure, wata kila ma tana taimakawa wajen warware matsalar wasu ma`auratan. Gini akan wannan ilmi nata, shi ya sa ta cancanci a rika zama ana shawara da ita, domin jin ra`ayinta, abin kuma da aka binciko, a baje mata a fefe, zabi kuma ya rage nata.

3. Bazawara da ake neman aurenta:- Ita wannan wuka da nama na hannunta, na waliyyanta jibintar daurin aure da ba da ita, amma bincike nata ne, ita ta san wanda za ta nada ya tattaro mata bayanan da take son ji, sai dai waliyyan nata na da damar ba ta shawara, ko kuma bayan ta taro bayanenta ta gabatar ga abokan shawararta daga cikin dangi, ko aminai domin jin ra`ayinsu. Ko ba komai dai ita ta dandana rayuwar aure, ta ji yadda zaman gida yake a kwanakin zawarci, don haka da wuya ta dauki matsayin Allah ya maimaita mana, sai dai ko hukuncin kaddara, ko kuma wacce ta zamo mai kunnen kashi, wannan kuwa yau da gobe ma ta isa ta hora ta.

Ina ga ya kamata mu dan dakata a nan saboda gudun kosawa, insha`allahu a kashi na gaba za mu amsa ragowar tambaya dayar da ta rage !


A wannan kashin za mu amsa tambaya dayan da ta rage ne a wannan batun na sama insha`allahu ! Tambayar dai ita ce:-

DA WANE MA`AUNIN YA KAMATA A YI BINCIKEN ?
AMSA:-

Ma`aunin da ya kamata a yi binciken da shi dai guda biyu ne:-

(1) Shari`ah.
(2) Al`ada.

1. SHARI`AH: Za a bincika komai ne da idon shari`ah, domin duk binciken da bai hau kan wannan ma`auni ba, to ba za a taba samun daidai ba, ba kuma zai taba haifar da kyakkywar natija ba, domin shari`ah ita ce ma`aunin rayuwar duk wani musulmi nagari. Idan abubuwan da aka tattaro game da mutum ba su ci jarrabawa a idon shari`ah ba, hakura da wannan mutumin shi ya fi zamowa alkhairi, idan kuma sun ci jarrabawar aka saka son zuciya, to ba za a taba ganin daidai ba.

2. AL`ADA: Shari`ah tana la`akari da al`adar ko wace al`umma, ta karbi wacce ba ta saba mata ba, ta kuma yi watsi da wacce ta saba mata. Manufa a nan ita ce, ko wace al`umma tana da kyawawan al`adunta, kuma duk abinda ya saba wa kyawawan al`adun ba karamin ta`addanci ba ne wanda ya ke rayuwa a cikin wannan al`ummar ya rika aikata shi, tunda dai al`adar ba ta saba wa shari`ah ba.

Gini akan wannan, ya zama daga cikin ma`aunin da za a yi amfani da shi a binciken da za a kaddamar; kula da cewa shin mutumin nan yana da wata gazawa wajen aiwatar da kyawawan al`adunmu na tsarin zamantakewar yau da kullum ko kuma ta rayuwar aure ? Idan har an samu gazawar, sai a duba; shin hakan ka iya kawo cikas cikin jindadin zaman aure ? Ko hakan ba zai kawo wani cikas ba ? Idan hakan ka iya kawo rashin jindadin zaman aure ne, sai a yi watsi da mutumin. Idan kuma armashi zai rage, sai a fahimci cewa daman ba ka taba samun abinda kake so a duniya 100%, sai a yi hakuri da abinda ya sauwaka.

KAMMALAWA:

A fahimtata, ina ga idan aka bi matakan da aka baiyana a rubututtuka biyar din nan da muka yi game da bincike dangane da maganar aure, za a samu ragi mai yawa a matsalolin aure da muke cin karo da su, sake-saken aure ma ka iya raguwa.
Ina mai tabbatar wa da `yan uwa cewa duk wani binciken da za a yi, ba zai zama mai tasiri ba, sai ya kunshi abubuwa hudu:-

1.Tsarkake niyya tsakani da Allah.
2. Dagewa da addu`a da neman taimako da budi daga Allah.
3. Cire dogon buri da son duniya.
4. Kauce wa bidi`o`i da ganin kyashi.
Daga karshe nake cewa bayanaina ba nassi bane, wani na iya hango sabaninsu. Abinda na yi daidai daga Allah ne, abinda na yi kuskure daga ni ne, ina rokon Allah ya yi min afuwa akan hakan !

ALLAH YA DATAR DA MU ALKHAIRI !
NA SADAUKAR DA BAYANAN NAN GA DUK WANI NAMIJI MAI NEMAN AURE NA FARKO NE KO KUMA KARI, DA KUMA DUK WATA MACE DA BA TA DA AURE TAKE KUMA DA NIYYAR YI, DA KUMA DUK WASU IYAYE DA SUKE SON AURAR DA `YA`YANSU MAZA KO MATA !

Post a Comment

0 Comments