ISTIMNAI (WASA DA AL'AURA)


Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2OJXVQKUUPOKO1

ISTIMNAI (WASA DA AL'AURA) 

Mal.Aminu Ibrahim Daurawa 

Masturbation: shi ne Wasa da Al’aura, wanda a larabce aka kira da “Istimna’i” Wannan baƙar al'ada ta yaɗu yanzu tsakanin samari da ƴan mata, waɗanda suke ganin haka kariya ne daga faɗawa zina,
Sheɗan yana ƙara an giza wannan muguwar al'ada har tsakanin wasu matan aure da mazajan su suke ƙaurace musu,
Suna yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima’i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko namiji, ga mace. 

Wasa da Al’aura ga maza, sukan yi amfani da Sabulu ko Mai ko wani abu mai yauki da santsi ta hanyar mulmula Azzakarinsu har su biya bukatar su. Amma mata, suna amfani da yatsa ko kyandir ko kokwanba ko wani abunda za su tura cikin gabansu, har su biya bukatar su. 

 wannan matsala ta Wasa da Al’aura, dabi’a ce abar kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan addini, da na al’ada, da kuma na lafiya. 

Mafi yawan Malaman Musulunce sun tafi akan HARAMCIN Wasa da Al’aura don biyan bukata, dalilin su fadan Allah (SWT): ‘Da wadanda suke, ga farjojinsu, masu tsarewa ne. Sai fa akan matansu…ko abinda damar su ta mallaka na (kuyangi) To, anan ba a zargin su. Amma duk wanda ya nemi abinda yake a bayan wannan, to, wadannan su ne masu ketare iyaka’ (Mara’rij 29 – 31, Muminun 2- 4), Kuma wadannan da ba su samu aure ba, sukame 
kansu har Allah ya wadatar da su daga falalarsa… (Annur 33) 
Haramcin wannan dabi’a ta Wasa da Al’aura, fahimta ce ta manyan malaman duniya, kamar Malikiyya, Shafi’iyya, Hambaliyya, Ibn Taimiyya, Ibn Kayyim, Ibn Baz, Usaimin… 

Dukkan Musulmi an umurce shi da ya yi aure, in ba zai iya ba, yayi Azumi, Kuma ya tsare idonsa da kunninsa da ga kallo ko sauraren batsa da al-fasha. Musulunci ya yi umurni da haka ne tare da karanta cin abinci don rage sha’awa. 

Lokacin da bawa ya bi dukkanin hanyoyin da muka ambata don tsare kansa da ga zina, amma ya kasa samun saukin sha’awar sa, to, wasu daga cikin Malamai suna ganin idan yayi Wasa da Al’aurar sa don gudun fadawa ga halakar Zina, to, ba bu laifi akan sa, sabo da lalura. Amma gaskiya wannan maganar ta na da rauni sosai, kuma bai kamata ayi aiki da ita ba. 

Binciken masanan kimiyyar lafiya ya nuna cewa YAWAN WASA DA AL’AURA (excessive masturbation) nada illa ga lafiya. Kuma ya zama matsala ga magidanta, don wasu har bayan aure ma suna yi, don ba su samun gamsuwa, sai sun yi abinan da suka saba da shi, wato, Wasa da Al’aura (istimna’i). 

Duk wanda bashi da halin yin aure to ya kiyaye yawan kallon batsa da zama gurin da ake yawan maganar mata, ya shagaltar da kansa da Karatun Alkur'ani da azkar da yawan azumi, da karanta tarihin magabata da zama cikin mutanen kirki da kwanciya da alwala, da gaggauta yin aure da zarar an sami dama.

Allah ya kiyaye masa samarin mu da ƴan mata daga faɗawa tarkon sheɗan.


Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2OJXVQKUUPOKO1

Post a Comment

0 Comments