Illar Rashin kunya ga rayuwar malam bahaushe . Kamar yadda ya gabata, kunya a al’adar Bahaushe musamman ga mace tamkar gishiri ne a miya, domin kuwa ta shafi kowane Bangare na rayuwa.
Ita ce ado ga mutane, ita ce farin wata mai haskaka al’umma, ita ke sanyawa a so mutum, kamar yadda rashin ta kan sanya a guje mutum. Duk abin da aka ce yana da muhimmanci babu shakka rashin yin sa wata illa ce babba ga mutum. Tun da dai har Musulunci ya nuna fa’idar kunya, lallai akwai wata hikimar yin hakan. Akwai illolin da rashin kunya kan haifar kamar haka:
Lalacewar tarbiyya
Rashin kunya a wurin mace illa ce babba domin ita kadai tana iya zame mata babbar matsala a rayuwa. Kunya ce ke sa mace ta tsaya matsayinta na mace tare da kyakkyawar tarbiyya. A da idan aka ga mace tana yawan mu’amala da maza, akan yi mata waka cewa Mai wasa da maza karya
tun da na gan ta na rena ta Saboda lalacewar tarbiyya a yanzu, mata sun manta su mata ne, domin sun dauki cudanya da maza wayewa kuma duk wadda ba ta yi, wai ba ta waye ba. Idan dai har mace wadda ita ce mai bayar da tarbiyya, ta rasa ta, lallai al’amari ya lalace. Irin wannan mu’amala ta rashin tarbiyya kan sa su faɗa cikin aikata aikin assh’ wanda hakan kan kawo dimbin matsaloli ga al’umma, irin zinace-zinace da cututtukan da hakan kan haifar, uwa-uba da haihuwar ‘ya’ya ba tare da aure ba.
Rashin biyayya
Wata illa da rashin kunya kan haifar musamman ga mace, ita ce rashin biyayya. Idan mace tana da kunya, babu shakka tana yi wa duk wani wanda ya dace biyayya, musamman iyayenta da yayyanta da mijinta da kuma surukanta. Ana samun akasin haka ne idan kunya ta yi rauni a Bangarenta, domin ba za ta ga darajar iyayenta ba, wani lokaci ma za ta iya fadi masu duk abin da ta ga dama, to, balle kuma yaya abokin dambe. Shi kuwa miji, ai tamkar ya auro wutar dafa shi ne, tunda kuwa ba ta ga darajar iyayenta ba, yaya za a yi ta ga ta surukanta? Ai abin da wuya, wai gurguwa da aure nesa.
Bayyanar da tsiraici
Sutura dai ita ce mutuncin mutum domin irin shigar da mutum ya yi, haka mutane ke ɗaukarsa. Duk wanda ya yi shigar mutunci, a wajen jama’a shi mai mutunci ne, kamar yadda idan mutum ya yi shigar da ta saɓa wa hakan. A al’ada da dabi’a irin ta Bahaushe, mace na jin kunyar bayyanar da tsiraicinta ga duk wani wanda ba muharraminta ba, musamman yadda a wannan zamanin da ilimin addinin Musulunci ya yawaita (Rabi 2009:10). Rashin kunya kan jefa mace yin shiga mummuna wadda za ta jawo mata matsala tare da al’umma baki daya. ldan aka dubi yadda kunya ta yi karanci a wannan zamanin da kuma irin shigar da mata ke yi, za a san lallai ana cikin wani hali na tashin hankali. Irin wannan shiga ta tsiraici kan jawo wa mata fitinu iri-iri, misali, yadda ake yi wa wasu fyade da yadda wasu mazan za su samu damar jefa su tarkon shedan, wato aikata ɓarna. Har ila yau, idan mace ba ta yi shigar kirki ba, to, tamkar tana tallata kanta ne, wanda mace mai kunya ba za ta yi hakan ba. Duk bayan wannan bala’in, ga kuma rashin bin dokar Allah, wanda shi ne ya umurce ta da rufe jikinta. Ai ko kasuwa mutum ya je sayen nama, babu yadda zai sayi wanda yake bude, kuma kuda na bin sa, alhali ga wanda yake a rufe. To, haka ma al’amarin yake dangane da mace mai suturta jikinta da kuma wadda ba ta yin hakan.
Wani al’amarin da ya kamata a kira da cigaban mai shiga rijiya, shi ne yadda mace mai hali na kunya a waiman zamanin, wasu kan dauke ta a matsayin wadda ba ta waye ba. Duk da haka duk mai hankali da kuma zurfin tunani, ya san cewa “kunya marin da ce”, kuma har kasa ta nade mai ita na tare da cin nasara duniya da lahira.
Ashe ke nan kunya na ɗaga daraja da kimar mutum, tana kuma sa a kasance mai tarbiyya da biyayya da da’a da kuma kamala. Duk da haka, ya dace mutane musamman mata su nemi ilimi domin ta haka ne za su gane irin kunyar da ta dace da shari’a, don kada “wajen neman gira, a rasa ido”. Idan dai har mutane musamman mata za su yi hakan, su kuma masu karancin kunya, su wadatu da ita, babu shakka mutane musamman matan Hausawa za suƙara zama abin koyi ga sauran wasu al’ummomi, domin ai dama Musulunci ya koyar da mu cewa “babu abin da kunya ke haifarwa sai alheri”
0 Comments