*YADDA AKE KULA DA LAFIYAR JARIRAI*
Anan idan nace jariri ina nufin yaro karami daga haihuwa zuwa lokocin da za'a yaye shi...
*Da zaran an haifi yaro me yakamata ayi masa ?*
Zan kawo wannan bayani ne sabida wassu matan zun zabi su haihu a gidajen su fiye da zuwa asibity duk da hatsarin dake cikin haihuwa a gida.
1- Da zaran an haifi yaro abu nafarko da yakamata a duba shine:
- *A duba aga ko yaro yana numfashi daidai* :
Yin hakan gaskiya zai taaimaka wajen ceton rayuwar jarirai.
Mafi yawa jarirai suna samun matsalar numfashi lokocin da aka haifesu, rashin duba lafiyar numfashi a wannan lokocin yana aika jarirai zuwa Lahira...
Zai dai kiji ance ta haifi yaron da rai daga baya ya koma ga ALLAH...
Abin tambaya idan jariri baya numfashi mekyeu ko baiyi kuka ba me yakamata ayi ?
A daidai wannan lokocin diyawa daga cikin ungozoma da ma'aikatan lafiya zai kiga suyi ta dukan bayan jariri, wanda hakan ba daidai bane, masana kiwon lafiya sun hana...
Maimaikon a daki jariri to ayi haka:
- A share majinar dake bakin jariri, a bude bakin jariri as yatsa ko sirinji a share majinar dake bakin sa.
- A ringa shafa bayan jariri a hakankali, hakan zai dumama jikin jariri har yasamu yaji garau..
- a lokaci guda a rika k shafa ƙarƙashin ƙafar jariri, hakan zai taimaka wajen saka jariri yaja ƙaƙƙarfan numfashi.
Bayan anyi haka idan jariri bai kawo wuta yadda akeso ba, to dole ayi masa Busar Numfashin Ceto, wanda babu bukatar bayani domin aikin ma'aikacin lafiya ne...
Idan kuma akayi sa'a aka samu numfashin yaro kalaw yake..
2- Abu na biyu shine dole a kifa yaro a kirjin mamar sa ( skin to skin contact):
Diyawa daga cikin mutanen mu da zaran an haifi jariri abu nafarko da sukeyi shine suyiwa jariri wanka, wanda hankan shine hanyace ta zuwa lahira ga jariri..
Sabida a daidai wannan lokocin wanka zai iya sa ya kamu da matsanacin sanyi.
Jariri baya buƙatar wanka bayan haihuwa nan take, abinda yake bukata shine waje mai dumi...
3- Bayan hakan abu na uku shine..
A taimaka a saka jariri a nono da zaran angama wadannan abubuwa guda biyu domin Ya samu nonon farko mai dauke da maiko..
Sabida fa nonon farko Yana dauke da sinadaran bada kariya ga jarirai..
4- Abu na hudu shine: Allurar rigakafin BCG Da Hepatitis B Vaccine.
Da zaran sun fita a labor room ayiwa jarirai rigakafin tarin fuka TB da kuma ciwon hanta kafin suje gida.
Dalilin yin hakan idan fa suka fita daga asibity zuwa gida anan ne mutane za sufara barka kuma kowa burin sa yadauki jaririn wanda sabon mutum ne babu ishesshen garkuwar jiki a garesa, ta nan zai iya daukan wadannan cututtukan idan ba'a masa riga kafin ba.
5- Abu na biyar shine: A karbawa yaro maganin ciwon ido na tetracycline eye ointment a inda saka masa.
Dalili kuwa shine yanzu cutar sanyi irinsu gonorrhea da chlamydia sa sauran infection yayi yawa.
Wanda idan macce tana dauke da wannan matsalar zai iya shaifar idon jaririn ta, shine dalilin bada maganin.
6- Abu na shidda shine : A tsaftace jariri a goge duk wani jini dakuma kashin farko na jaririn, amma kada ayi masa wanka a ranar da aka haife shi.
Bayan an goge shi a samu kaya mai kauri a saka masa, idan babu kauri za a iya saka masa riga biyu a lokoci guda.
Sayan kwana biyu ko uku sai aringa yiwa jaririn wanka akai akai, domin gusarda nono, yawu, da kuma sauran datti.
Ina bayani ko rabi banzo ba lokocin da na daukawo kaina ya cika.
Insha Allah zamu ci gaba da bayani zuwa wani lokocin.
Idan da mai tambaya ina sauraron sa.
Lafiya Uwar Jiki WhatsApp group
📝 Zannah Mustapha Wakil
0 Comments