Wasu Kurakurai Guda 10 Da Mata Suke Tafkawa A Lokacin Soyayya:


Wasu Kurakurai Guda 10 Da Mata Suke Tafkawa A Lokacin Soyayya
:
 
Mata kalilan ne zaki samesu sun tsunduma kogin soyayya basu rika tafka kurakure ba.

Su mata a duk lokacinda suka fada soyayya ba kasafai suke amfani da hankalinsu ba, hakan yasa sai suyi ta tafka kuskure ba tare da sun sani ba. Wasu ma koda sun sani son rai yakan hanasu gyarawa.
Ga wasu Kurakuren da akasarin mata suke tafkawa a lokacin da suke soyayya.
 
1: Turawa Samarin Da Suke Soyayya Dasu Hotuna Da Bidiyon Tsiraicinsu-Wannan ya zama ruwan dare ga mata a yanzu. Wasu koda saurayi bai bukaci hotunan ba da kansu suke turawa.

Bayan hotuna da bidiyon batsa. Wani kuskuren da matan ke tafkawa shine kiran bidiyon kai tsaye yayin da take tsirara.

A gaskiya wannan ba karamin kuskure bane. Ki sani duk saurayin da kike masa hakan ba zai daukeki da mahimmanci musamman kananan samarin nan masu karancin shekaru. Wasu ma da wannnan zasu dawo suna miki barazana na yadawa duniya idan kika ki amincewa da bukatar su. Don haka ayi hattara.

2: Zama Da Saurayi Ba Tare Da Aure Ba:

Wani kuskuren da wasu matan suke tafkawa shine yadda suke tarewa su zauna da mai sonsu da aure tun kamin su daura auren.
A gaskiya hakan bai dace ba kuma zubda mutunci ne. Kuma nan gaba hakan yana iya zama hujjar da zai ki aurenki.


Idan ma kina zaman kannki ne mai makon ku zau

na tare gara ya samamiki wajen da zaki zauna daban da inda yake kamin lokacin da kuka yi niyar daura auren naku.
Amma zama waje guda da wanda yake da niyar aurenki kuskure ne babba. Sai a kiyaye, kada garin soyaya ki rasa masoyin.

3: Kwashe Sirrin Gidanku Ki Fadamasa:

Kada soyayya yasa ki kwashe sirrin gidanku ko na iyalanku ki fadawa saurayi musamman ma wanda baku jima da shi ba.
Sirrin gidanku sirrinku ne. Yawan kawo zancen ga wanda ba cikin iyalanku ba, zubda mutunci ne. Da fatan mata zasu kiyaye.

4: Fada Da Wasu Matan Akan Saurayi: Shi ma dai kuskure ne. Ba sai kin yi fada da wacce kike zargin tana son saurayinki sannan zaki nuna masa kina sonshi ba. Nuna masa bacin ta ki ke dashi ba kawai ya isa ki nuna masa bacin ranki.

Don haka kuskure ne babba kije kinata dambe akan saurayin da bai aureki ba.

5: Rabuwa Da Wani Abunda Zai Taimakamiki Saboda Soyayya: Akwai matan da suke sadaukar da rayuwarsu saboda saurayin da zata aura. 
Mata na barin karatunsu, kasuwancin su da kuma aiyukansu kawai saboda wanda zasu aura yace baya so. Wannan gangancine da kuma wauta.
Kada ki sake wani ya sa ki daina yin wani abunda kika san zai taimaki rayuwarki ko yana taimakon rayuwarki saboda kawai ki dadadamasa.
 
6: Sakar Miki Jikinki Yayi Abunda Yake So A Lokacin Da Yake So: Wasu matan yadda suke sakarwa wanda zasu aura jikinsu yadda ko auren akayi sai haka.

Gabanki shine darajarki, shine mutuncinki. Muddin namiji yace zai aureki, bashi gabanki tamkar kunyi aure zai sa nan gaba ki rasa shi. Ki kula.

7: Ci Gaba Da Soyayya Danamiji Bayan Kinsan Yana Kula Wasu Matan: Wasu Matan suna sane da samarinsu na soyayya da wasu matan amma saboda son rai sai kiki hakura da shi.

Babu yadda saurayi da yake sonki da gaske zai rika kula wasu matan bayan bai gama da nake alkawarin auren ba.
Kada ki kasance cikin masu aikata irin wannan kuskuren saboda kina son sa.

8: Nunawa Namiji Shine Autan Maza: Da zaran kin nunawa saurayinki idan ba shi ba rijiya kuskure ne.

Maza musamman masu karancin shekaru sukan yi amfani da wannan damar na yadda mace ke musu kuka saboda su auresu.
Ki nunawa namiji ko yanzu kuka rabu zaki iya ci gaba da rayuwar ki. 

9: Yin Soyayya Mai Tsawo Babu Zancen Aure: Akwai matan da yansu hakan sun haura shekaru 5 suna soyayya da wani da yace zai auresu amma har yanzu shuru.

Ki tabbatar da cewa wannan da kike soyayya da shi bai bata miki lokacin da daga baya zai watsar dake ba. 

10: Auren Namijin Daya Tsofemiki-Wasu matan soyayya ko zakuwa na son yin aure yakan sasu suje su auri mazan da suka yi jika dasu.
Ba haramun bane, amma a dabi'ance bai dace ba. Kinada takaitancen lokaci ne na more miji muddin kika aure Namijin da shekarunsa ya ninka naki 3.

#tsangayarmallamtonga 
Yana da kyau mata ku fahimci cewa. Tsananin soyayyar da kike yiwa namiji na kauda kai a was kurakuren da kike tafkawa kina sane ko a rashin sani, na iya jawo miki matsalar rasa shi abunda kike kauna.

Da fatan 'yan uwa mata zaku gyara domin mutuncin kanku.

Post a Comment

0 Comments