RUBUTU NA BIYU AKAN YADDA AKE KULA DA LAFIYAR JARIRI:


*RUBUTU NA BIYU AKAN YADDA AKE KULA DA LAFIYAR JARIRI*

Mahaifiya da jaririn suna da bukatar kulawa ta musamman bayan haihuwa.

Yana da kyeu mahaifiya da jaririn ta sudinga xuwa *Postnatal* , ana a duba jariri da mahaifar sa :

- Kwana daya da haihuwa
- Kwanaki uku da haihuwa
- Kwanaki bakwai da haihuwa

Dalili wannan zuwa shine domin a gane da wuri idan da akoi wata matsalar kuma ayi maganin ta ( early diagnosis and treatment).

Kusan dai yawan zuwa asibiti ita ce mafi kyawun hanyar gano matsalolin lafiya kafin su zamo hatsari, Ba a tsaya ana tambaya ta Facebook ko WhatsApp...

Ga wassu daga cikin alamomin da idan aka gani kada a tsaya a gida a gaggauta zuwa asibiti domin neman shawarar likita:

1- Numfashi da sauri da sauri
2- Numfashi Dakkyer
3- Zazzabi
4- Kin cin Abinci
5- Fita daga hayyaci
6- Amai da Gudawa

Wadannan su muke kira da *danger sign* ma'ana alamomi masu hatsari ga jariri, sabida yanxu zai aika jariri zuwa kabari..
Idan aka ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomin hakan na nufin bashi da lafiya. 

Idan jaririn yana da alamomi samada alama ɗaya, to yana cikin babban hatsari kuma yana buƙatar ganin likita da gaggawa.
Mu ma'aikatan lafiya matsalar da akafi zuwa da shi wajen mu shine:

1- Yawan kuka
2- Amar da Nono
3 Rashin Bushewar Cibiya
4- Kumburin ciki

1- Yawan kuka:

Waɗansu jariran sukanyi kuka sama da wasu. Jaririn dake kuka wataƙila lafiyarsa ƙalau idan har wani alamar rashin lafiya bai bayyana a jikin sa ba.

Amma duk sanda aka ga yaro yafiye kuka kuma babu sauran alamomin rashin lafiya a duba ko yana numfashi dai dai alokacin da baya kuka.

Akoi yawan kuka da muke Kira da *Colic* amma shi mafi yawa yaro daddare yake yawan kukan, kuma yaro yana dainawa bayan watanni uku.

2- Amar da ruwan nono:

Jarirai sukan yi tunbiɗin nono. Wani lokacin dayawa har yakan fito ta baki ko hanci. Tunbiɗin nono ba matsala bace matuƙar jaririn yana yawan shan nono, kuma yana ƙara nauyi. Yi ƙoƙarin riƙe shi a tsaye bayan yasha. Wannan zai hana nonon ya fito.

Amai Wanda take bukatar zuwa asibiti sune:

- Amai ba ƙaƙƙautawa, ko kuma ya kasa riƙe komai acikinsa.
- Aman jini.
- Kuraje

3- Rashin Bushewar Cibiya:

Bayan an yanke cibiya kada a dinga rufeta.

Kada a saka kashin shanu, ko gawayi, kada rufe ta da kaya ko kunzugu. Kada a rika taba ta, kuma idan ya zama dole a taba to a wanke hannaye da sabulu da ruwa kafin a taba. 

Idan cibiyar ko cikin yayi datti, ko kuma busashshen jinni ya makalkale a jiki, sai a wanke da sabulu a kuma goge da kyalle mai tsafta.

Idan mahaifiya tanaso ta rufe cibiyar to a tabbatar abin da za a rufe din mai tsafta ne, kuma a rika canjawa duk bayan lokaci-lokaci a kowacce rana.

Idan aka bi wannan tsarin to Cibiyar zata bushe ta faɗi a cikin sati.

Idan kewayen cibiyar yayi ja ko zafi ko yana wari ko yana fitar da ruwa, to wataƙila ta kamu da cuta ya kamata aje asibity.

4- Kumburin Ciki:

Mafiyawan matsalar kumburin ciki, ba matsala ce da take bukatar magani ba, shawarwari kawai ta wadatar.

Mafi yawa mata basa barin bakin nono ya Shiga bakin yaro sosai ba, hakan zai sa yaro ya tsotsi iska, Kuma wannan iskan yana taruwa ne a ciki har ya kumburar da cikin.

Idan aka gyera yanayin shayarwa bai daina ba aje asibity domin bincike.

5- Kuraje

Sababbin haihuwa suna yin ƙuraje, ruɗi-ruɗi dakuma banbancin launin fata wanda sau dayawa basa cutarwa kuma suna washewa da kansu. 

Ƙuraje a ɗuwawun jariri yana faruwa ne saboda kasancewar su cikin danshin fitsari da kashi. A riƙa goge wurin akai-akai. A riƙa canja wando akai akai . Za a iya shafa Dustin powder zai taimakawa. Idan bai warke ba acikin 'yan kwanaki to ya kamata aje asibity.
Lokoci yayi anan zan saya Insha ALLAH zamuci gaba wani Lokocin...

Idan da tambaya ina sauraro...

📝 Zannah Mustapha Wakil
Lafiya Uwar Jiki WhatsApp group.

Post a Comment

0 Comments