Matsalolin Matasa akan Kasuwanci:


Matsalolin Matasa akan Kasuwanci

Babu shakka a halin yanzu ana fama da rashin kudaden fara sana’a, musamman idan ana bukatar shago da kayan aiki. Babu komai, za ka iya farawa ko a gida ne, sannan idan ka samu karbuwa, kuma mutane suka fara jin dadin yadda kake gabatar da sana’arka, to sai ka tara ribar ka, ka bude shago. Sai dai ko ka ga yadda kasuwancin naka zai kasance ne bai dace da gida ba to a nan a kan iya chanja dabara. Bayan wadannan akwai wasu matsaloli da suke hana yawancin matasa shiga harkar kasuwanci da gina kamfani a wannan yanki namu.

Matsala ta 1: Tsoro –a mafi yawancin lokuta tsoro yana kasancewa a matakin farko ko na biyu a fara kasuwanci musamman ga matasa. Wasu suna tsoron asara ko faduwa ba su san da cewa tsoron shine mafi munin abun gudu ba.

Mafita: Cire tsoro a rai ta hanyar mamaye zuciya da kuzarin jarumta da juriya.

Matsala ta 2: Rashin sanin madogaran farawa –idan mutum bai san yadda zai fara kasuwanci ba hakika hakan ya na zama babbar matsalar da ke hana shi aikata katabus. 

Mafita: Dole mutum zai nemi sanin madafun fara kasuwanci, cigabansa, kalubalan da ake fuskanta da kuma yadda za a bunkasa shi. 

Matsala ta 3: Saurin sarewa –wasu lokutan ko bayan an fara kasuwanci to ba ya jumiri matukar mutum bai jure ya jajirce ba ya dauki hanyar sarewa. Ba ko da yaushe ba ne kasuwancin mutum zai yi nasara, ba kuma a lokaci daya ake samun daukaka da bunkasa a kasuwanci ba. A yayinda mutum ya gaza fahimtar wannan kuma ya fadi kamar sau daya ko sau biyu sai yayi kuskuren sarewa.

Mafita: Juriya da jajircewa akan abunda aka sanya a gaba ba tare da tunanin sarewa ba.

Matsala ta 4: Rashin samun kwarin gwiwwa –haka kuma wani lokaci a yankin da mutum yake idan ya fara kasuwanci to yana iya samun tangarda ta wajen al’ummar yankin saboda rashin samun kwarin gwiwwarsu. Wasu lokutan sai su kasance masu kushe sana’ar mutum ko suna masa dariya. A irin wannan lokaci kuma sai mutum ya sare ya rusa kasuwancinsa ko kuma ya kasa bunkasa shi.

Mafita: Kau da kai daga abunda wasu za su ce akan kasuwancin mutum ta hanyar jajircewa don kai wa ga ci.

Matsala ta 5: Rashin kayan aiki –wannan ma ba karamin illa yake yi wa matasa ba. Ko mutum ya samu ilimin fara kasuwanci ba lalle ba ne ya samu jari har ya iya sayen kayan da zai fara aiki da su. Misali idan mutum ya koyi sana’ar fenti ko gyaran mota da makamancinsa ba lalle ba ne ya iya samun kayan aiki na zamani.

Mafita: Samun kudade ko kadan ne don sayan kayan aiki. Wasu muhimman hanyoyin da mutum zai samu kudade sun hada da tarunsa ko karbar bashi daga wajen wani.

Matsala ta 6: Rashin jari da wurin kasuwanci –kamar yadda yake a sama, babbar matsalar matashi a yau ko da zai fara kasuwanci shine rashin jari ko wurin yin kasuwanci. Sau tari matasa suna samun dama amma haka take subucewa ba tare da sun amfana da ita ba saboda rashin jari.

Mafita: Kadan daga cikin muhimman hanyoyin da mutum zai samu jari ko kadan ne ya fara da shi sun hada da karbar bashi daga wajen wani, ko kuma mutum ya tara kudadensa kadan-kadan.

Matsala ta 7: Rashin sanin muhimmanci kasuwanci –wani lokaci kuma wasu rashin sanin muhimmancin kasuwancin ne yake damunsu. Wata jimlar Hausa ta na cewa ko min gatan yaro ya koyi sana’a. Hakika wannan ba karamar barazana ba ce ace mutum bai san muhimmancin abunda ya kamata ya rayu yana yi ba. Dole matukar za a fara abu to sai an san muhimmancinsa. 

Mafita: Dole mutum ya san muhimmancin kasuwanci kafin ya fara shi domin hakan ne kawai zai bashi damar rike shi da dajara idan ya fara

Matsala ta 8: Gurguwar fahimta ko damulallen tunani –idan tunanin mutum ya riga ya dulmiye ko kuma ya kasance mai gurguwar fahimta akan kasuwanci to ba lalle ba ne ya iya gina kasuwancinsa da kansa matukar bai cire dulmiyayyan tunanin nan ba. Hakika falsafar mutum ta na tafiya ne da yanayin tunaninsa –idan ya gina shi a kan turba mai kyau sai ya kasance mai tafiya akan daidai, haka idan ya gina shi a sabanin haka ma abunda zai gani bai wuce sabanin daidai din ba.

Mafita: Gina falsafar tunanin mutum akan daidai ta yadda ba zai yi tunanin faduwa ba da yin kyakkyawan zato akan kasuwancinsa.

Daga cikin littafin Zo Mu Gina Kamfani
#ZoMuGinaKamfani

- Mohiddeen Ahmad

Post a Comment

0 Comments