Amfanin Man Ridi A Jikin Dan’adam DA man aduwa:
Man Ridi yana daya daga cikin iri-irin Man da aka sani, an dai dade ana amfani da man ridi wajen yin magungunan gargajiya, bincike ya nuna ana amafani da man ridi tun wajen shekaru dubu da suka wuce domin kariya daga cututtuka da suka shafi abubuwan da kan iya kawo cutar fatar jiki ko kuma cutauttuka da suka yi karfi kamar su ciwon suga, hawan jini da sauransu. A wani Bincike da aka yi a makarantar Maharishi International College Fairfield Lowa a kasar Amurika an gano cewa dalibai na yin amfani da man ridi wajen wanke baki domin ba su kariya ta musamman wajen kare cutar dake fito wa a dasashin mutum wanda kansa gurin ya yi ta zafi har ya janyo asarar hakora.
Amfanin man ridi bai tsaya a nan ba domin ana amfani da shi wajen wanke kai don kashe kwarkwata ko amosanin kai. Ana kuma shafawa yara man ridi a jikisu don gyaran fatar jiki.
Ga Dai Wasu Cututtuka Da Man Ridi Ke Warkarwa
– Gyara fata da inganta lafiyar ta.
– Kara girman gashi da launin bakinsa.
– Kariya daga ciwon-daji.
– Gyara fatar jarirai da sanya su natsuwa a bacci.
– Hana rubewar hakori, kogon hakori da sauransu.
– Kariya daga ciwon asma da cututtukan numfasa.
– Rage hawan jini.
– Rage yawan sinadarin “Cholesterol”.
– Kariya daga ciwon suga.
– Inganta lafiyar kwakwalwa da sauransu.
-Domin samun lafiyayyar fata kuma, ana hada Man Zaitun da Man Ridi a mayar da shi abin shafawa a wata daya fatar jikin mutum za ta yi kyau kuma ta samu kariya daga cututtukan fata.
-Ciwon mara, ana shan cokali 2 safe da rana da kuma dare dan maganin ciwon mara.
– Ciwon cikin da baya jin magani da kuraje musamman na kazwa, a samu sabulun Zaitun a rika wanka da ita idan aka bushe sai a shafa man ridi a kalla a yi haka sau 2 a rana tsawon sati daya.
– Ciwon sikila, ana hada man ridi da Zuma a rika bawa mai matsalar yana shan cokali biyu safe da rana da dare har tsawon wata 2.
-Basir mai tsiro, a samu sassaken bagaruwa da ‘ya’yan ta a tafasa da ruwa idan suka tafasa in sun rage zafi sai a zauna cikin ruwan tsawon minti 15, idan aka fita a shafa man ridi a yi haka sau 2 ko wace rana tsawon kwana 10.
-Ashma, a rika shan cokali 2 safe da rana tsawon sati 3.
-Ulcer, a samu man ridi a hada da madara a rika sha da safe kafin a ci komai haka da dare bayan an ci komai sai a sha awa daya kafin a kwanta.
-Kumburin Jiki, ana shafa man ridi duk bayan an yi wanka da kuma in za a kwanta bacci.
–Soshe-soshe saboda yawaitar majina ko mataccen jin, sai a saka cokali 2 duk lokacin da za a ci abinci sannan kuma a shafe jiki da shi amma wajen shafawar dole sai an hada da man Zaitun.
-Ciwon mara lokacin fara al’ada, ana hada cokali daya na garin ridi da cokali daya na man Ridi da madarar gari a sha sau 3 kullum In sha Allahu za a samu sauki.
-Wanda yake da hawan jini ko matccen jini da sauransu sai ya rinka amfani da man ridi safe da yamma.
-Ri-ga-kafin hawan jini da shan inna, wanda ya dauki man ridi a matsayin abokin rayuwarsa wato kullum zai yi amfani dashi koda cokali daya ne zai samu kariya daga wadannan cututtuka kuma koda wace irin matsala ya samu kansa ciki.
Dimbin Amfanin Aduwa Ga Jikin Dan’adam
Zaman birni ya yi tasiri ko ya bata wannan al’umma fiye da yadda ake zato. Ko shakka babu a wannan lokaci yara da dama ba su san mecece aduwa ba, ballantana su san cewa tana da matukar amfani wajen lafiyar dan’Adam. Baya ga shan aduwa da muke yi saboda dan zakin da take da shi, tana da kuma amfani a jikin bil Adama. Kadan daga cikin amfanin ta, kamar yadda masana suka yi bincike a kai sun tabbatar da cewa tana maganin shawara, tsutsar ciki, gyambon ciki, farfadiya, ciwon asma, zawayi, attini da dai sauran su.
Ana samun bishiyar aduwa a kasashen Afrika da Indiya da wasu kasashen kudancin Asiya da kuma na Larabawa. Mutanen Habasha na kiran aduwa da Kudkuda, larabawa na kiran ta da Zachun, Indiya na kiran ta Enguwa yayin da mutanen Swahili na gabashin Afrika ke kiranta Mjunju.
Man Aduwa
-Idan aka matse kwallon aduwa, ana iya samun man girki da ya kai kashi 45 cikin dari, wannan mai na kwallon aduwa na da matukar amfani idan ana dafa abinci da shi. Yana kuma taimakawa wajen magance yawan kitse dake kawo toshewar hanyoyin jini da Asma da sauran cututtukan da muka ambata a baya.
-Asma, ana iya nika kwallon aduwa a mayar da shi gari sai a rika dibar garin kimanin cokali goma ana zubawa a ruwa kimanin cikin kofi guda, ana sha da safe har na tsawon kwanaki goma.
-Tsutsar ciki, a nan busar da kwallon aduwa ake yi a daka shi har sai ya zama gari sannan a rika zubawa a kunun gero ana sha lokaci bayan lokaci. In Allah ya yarda za a rabu da tsutsar cikin kowace iri ce dake cikin hanjin mutum ko kuma yara.
-Gyambo, a bangaren masu fama da gyambo kuma sai su samo ganyen aduwa dakakke ko kuma a daka shi a danyensa a rika wanke gyambon da shi, cikin dan kankanin lokaci in sha Allahu gyambon zai kame ko ya bushe ba tare da wani bata lokaci ba.
-Ciwon fatar jiki, a nan kuma sai a samu man da aka fitar daga jikin ‘ya’yan aduwa a rika shafawa a jiki baki daya, yana maganin kurajen jiki sosai, kazalika yana maganin sanyin kashi.
– Fitsarin jini, a kan daka bawon aduwa har sai ya zama gari, sannan a sanya a cikin ruwan da yara kan yi wanka da shi, misali kamar kududdufi domin kashe kwayoyin dake haddasa fitsarin jini da sauran wasu kwayoyin cututtuka irin su kurkunu da sauran su. Sai dai kuma wannan yana iya kashe kifaye da su dodon kodi dake cikin ruwan ko kududdufin.
-Tinjere, bayan an dafa bawon itacen aduwa, ana shan sa ne kadan-kadan don kuwa yana maganin cutar tinjere kwarai da gaske.
-Kunburin sawu ko na jiki, domin maganin wannan cuta ta kumburin sawu ko jiki, sai a dafa saiwar aduwa a cikin miya a rika sha. Kazalika yana maganin ciwon ciki.
0 Comments