Abubuwan Dake Haifar Da Raunin Mazakuta.
1. Hawan Jini; Wannan jinya ce dake haifar da illoli ga lafiyar mutum daga ciki har da raunata da namiji.
2. Ciwon Siga; Hakanan shi ma wannan ciwo idan ba ai da gaske ba yana iya kashe mazakuta gaba daya.
3. Ciwon Sanyi; Ciwo ne da ake dauka yayin jima'i ko bayan gida maras tsafta, kuma yana shafar al'aura ne, saboda haka ya na iya raunata mutum kwarai da gaske.
4. Basir; Hakazalika wannan ciwo ba karamar illa ya ke yi wa maza ma'aurata ba.
5. Matsananciyar Damuwa; Matukar mutum na cikin irin wannan yanayi, akwai matukar wahala sha'awarsa ta motsa ballantana ya samu mikewar azzakari.
6. Shan Taba; Ta na haifar da matsalolin lafiya ga dan-adam daga ciki har da illata hanyoyin jini da sauran gabobi da ke da matukar tasiri wajen mikewar gaban mutum.
7. Shan Giya; Khamru uwar laifi, ta na kan gaba wajen illata lafiyar dan adam gami da kashe ma sa azzakari.
8. Rashin Isasshen Abinci Mai Gina Jiki; Abincin da mu ke ci na da kyakkyawar alaka da lafiyarmu, saboda haka rashin sa na nakasa lafiyar jikinmu har da sha'awa da karfin mazakuta.
9. Rashin Motsa Jiki; Ba shakka rashin motsa jiki kan iya illata mutum ta fuskar gamsar da iyali, wannan ya hada da rashin karfi da saurin kawowa.
10. Wasu Magunguna; Abin nufi anan shine wasu magungunan cutar da mutum ke sha ka iya haifar da raunin mazakuta, misali daga cikin magungunan da ake bai wa ma su hawan jini akwai ma su wannan illar.
11. Hadari; Idan hadari ya rutsa da mutum kuma ya shafi al'aura ko hanyoyin jima'i, kamar 'ya'yan maraina, azzakari, ko jijiyoyin da su ke da alaka da jima'i hakan kan haddasa rauni ga namiji.
13. Wasu Nau'ikan Abinci; Akwai wasu nau'ikan abinci da ke ragewa namiji sha'awa da kuzari yayin jima'i.
14. Shan Miyagun Kwayoyi; Shan miyagun kwayoyi ko kuma shan kwayoyin barkatai ba bisa ka'ida ba kamar yadda mu ka ambata a sama, ko da kuwa kwayoyin na magani ne.
15. Rashin Isasshen Barci; Ya na da matukar tasiri wajen ragewa namiji kuzari yayin saduwar aure, ya na da kyuu mtum ya samu isasshen barci a kullum, akalla awoyi 7-8.
16. Kallon Fina-finan Batsa; Masana sun gudanar da bincike na zamani kuma sun gano tare da tabbatar da gagarumar illar da hakan ke haifarwa maza musamman ta bangaren jima'i.
Alamomin Raunin Mazakuta:
Wadanne alamomi ne mutum zai ji ya fara tunanin yana da matsalar raunin mazakuta ?.
a. Rashin Mikewar Azzakari; Haka na faruwa ko da an yi tunanin jima'i ko kuma ma an samu haduwar jikin mace da shi mai matsalar.
b. Saurin Kwantawar Azzakari; Abin nufi anan azzakarin zai mike sai dai ba da jimawa ba, sai ya kwanta, tun kafin aje ga saduwa ko kuma da zarar an fara. A lura wannan na da banbanci da saurin kawowa, saboda anan za ta kwanta ne ba tare da mai matsalar ya kawo ba.
c. Rashin Sha'awa; Mai wannan matsala zai ji ba ya sha'awar saduwa da iyali. Ma'ana gaba daya sha'awarsa ta gushe.
Maganin Karfin Maza.
Kamar yadda mu ka ambata tun da farko duk mai fama da daya ko wasu daga matsalolin can da mu ka zana a sama magance su shine warakarsa da ikon Allah. Duk da haka Hausawa kan ce, idan kana da kyau ka kara da wanka bayan magance kalubalen lafiya da ake fama da ita/su za a iya amfani da wadannan hade-hade da zamu zana a kasa.
Hakanan, ko da mutum ba ya fama da daya daga cikin wadancan matsaloli, masana na ba da shwarar yawaita motsa jiki da kuma lura da nau'in abincin da ake ci. Domin samun cikakken bayani karanta makalarmu mai kanun "Nau'ikan Abinci Ma Su Karawa Namiji Sha'awa Da Kuzari Yayin Jima'i" Da kuma "Nau'ikan Abinci Ma Su ragewa Ma'aurata Sha'awa Yayin Jima'i" za su taimaka ma ka kwarai gaya.
Hakika Allah Madaukakin sarki Y halicci gangar jikinmu daban-daban, sakamakon haka ya sa, maganin karin kuzarin namiji da sauran magunguna, su kan bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Ba lallai ne maganin da wani ya sha ya yi ma sa aiki, kuma wani mutum ya sha ya dace ba. Wannan dalilin ya sa mu ka ga dacewar kawo nau'i daban-daban, idan ka gwada ba ka dace ba, za ka iya dacewa a wani.
1. Dabino; Yadda ake amfani da shi, shine, ka samu dabinonka mai kyau guda 13 ko 15 sai ka wanke, ka zuba a mazubi mai tsafta sai ka zuba ruwa ya sha kansa, ka bar shi tsawon awa uku sannan ka cinye. Idan da hali ayi safe da yamma, amma idan ba hali sai aci da yamma kadai.
Karanta: Amfanin Dabino Ga Lafiyar Dan-adam
Sai dai ba a son aci wannan hadi da zarar an kammala cin abinci, idan son samu ne ana son aci lokacin da ake jin yunwa, sai a jira mintuna 20 zuwa 30 kafin aci wani abinci.
2. Kwai; Za a samu kwan kaza guda 2, babban cokali 1 na garin habbatus sauda, sai a cakuda su sosai sannan a soya sama-sama kar ya kone, sannan a cinye.
3. KANKANA ; Kankana na kunshe da wasu sinadarai dake aiki kwatankwacin maganin karfin maza na zamani da ake kira 'Viagra' a turance. Don haka tana kara karfin maza sosai.
Don a samu amfaninta sosai za a sha mintuna 30 kafin fara jima'i. Ana bukatar a cinye har wannan farar tsokar da kuma 'ya'yan. kuma kar a sha lokacin ciki na cike, amfi son a sha kafin cin abinci kuma a saurara bayan an sha zuwa mintuna 20 zuwa 30 kafin a bi ta da abinci.
Karanta: Amfanin Kankana ga lafiyar Dan-adam
4. Ayaba; Ta na da sanadarai dake karawa namiji kuzari, sai a ci guda uku ko biyu kafin jima'i da mintuna 30. Kamar kankana ba a son cin ta da zarar an kammala cin abinci.
5. Man Kanumfari; shi kuma za'a samu mai kyau wanda ba shi da hadi sai a shafe azzakari gaba daya mintuna 30 kafin jima'i.
6. Namijin Goro; Cin namijin goro akalla guda biyu a rana ya kan dawowa namiji kuzarinsa. An jarraba an tabbatar da hakan sakamakon wasu sanadarai dake cikinsa mai matukar fa'ida wajen samar da karsashi ga maza.
Fadakarwa: Akwai bukatar mu kauracewa amfani da maganin karin karfin maza na nasara ba tare da shawarar likita ba, saboda illolinsu ga lafiya.
0 Comments