Matan banza sune matan da suka watsar da mutuncinsu domin amfani da halittansu na mace su nemi kudi da shi.
Matan banza dai suna da nau'ika daban daban. Sai dai nau'in da maza musamman matasa suka fi mu'amala dasu sune matan da ake biyansu domin biyan bukata ta hanyar zina dasu. Irin wadannan matan babu aure a gabansu, basu da kunya bare tsoron Allah a tare dasu. Haka nan duk namijin da zai biyewa irin wadannan mata yana cikin hadari.
Haka kuma akasarin mazan da suke biye biyen matan banza sun somawa ne tun daga lokacin kurunciyarsu har zuwa manyantansu. Kason mazan da suke neman matan banza bayan sun girma ko bayan sun yi aure ana samunsu amna basu wuce kaso 15 cikin 100 ba.
A wannan darasin zamu kawo muku wasu dalilan da suka kamata mutum ya kauracewa mu'amala da irin wadannan matan.
1: Zubar Da Mutunci- duk wani namijin da yake neman matan banza har hakan ya bayyana ana daukarsa a matsayin mutumin da bai da mutunci a idanuwa mutane.
Mutunci wani abu ne babba ga bil Adam, duk abunda mutum yake yi a wannan duniya yana so mutane su daukeshi kuma su ganshi da mutunci. Amma neman matan banza yakan zubarwa mutum mutunci ko shi wanene.
2: Babu Yarda- Duk namijin da yake neman matan banza baya samun yarda daga wajen mutane. Baya ga rashin mutuncin da mutane suke kallonsa da shi, haka nan babu wanda yake son yin wata mu'amala da shi a zahiri.
3:Bata Lokaci- Maza masu neman matan banza da damansu basu fahimci cewa bata lokacinsu a banza suke yi ba.
Cikin mintuna ko awannin da namiji zai bata wajen neman matan banza, idan da zai yi amfani da lokacin wajen yin wani abun da zai amfaneshi sai yafi masa.
4: Barnan Kudi- Duk namijin da yasaka neman matan banza a gaba a kullum sai an sameshi da barnan kudi. Hakan yasa duk mai neman mata sai an sameshi da shiga matsala na kudi idan bai da hanyar samun kudi. Idan kuma namijin da yake da hanyar samun kudi za a sameshi wajen kashewa matan na banza kudin da zai sakasu a wasu hanyoyin zasu jawo masa riba ne.
Babu komai a neman matan banza sai tsabar asaran kudi.
5: Hadarin Kamuwa Da Cuta- Ba duk manema matan banza bane suke kare kai a lokacin da suke aikata zina da matan ba. Don haka duk namiji mai neman matan banza zai iya kamuwa da cututtukan da ake dauka ta Jima'i.
Har su kansu masu kokarin amfani da makari idan zasu yi zina, ana samun wasu lokutan da makarin yake fashewa. Wannan zai iya sawa su kamu da cuta.
6: Gurbata Al'uma- Shi namiji mai neman matan banza a kullum burinsa ya rika cin karo da matan banza da zai yi mu'amala da su.
Haka kuma mazan da suka shahara a neman matan banza cikin sauki suke lalata kananan yara mata har suma su soma sha'awar wannan harkar.
Haka nan shi namijin da ya rika a wannan harkar babu wata alaka da ke taka masa burkin na kin yin iskanci da mace komai kankantarta muddin dai tana da kwadayin kudi.
Mai neman matan banza bai damu ya baiwa abokinsa mai irin wannan harkar macen dayasan jininsu guda bazata yarda da shi ba.
Don haka maza masu neman matan banza ba karamin illa bane a cikin al'uma ba.
7: Karya- Duk namiji mai neman matan banza sai an sameshi da dankaren karya a tare dashi.
Da wuya kuyi wata mu'amala ta gaskiya da gaskiya da namiji mai neman matan banza bai maka karya ko ya yaudareka ba.
Su kansu matan ba kowacce bace kudi yake sa ta amince da namiji ba har sai ya hada da karya. Don haka shi mai neman matan banza shi da karya a hade suke.
8: Rashin Nastuwa- Duk wani mai neman matan daya shahara ka dubeshi da kyau babu natsuwa a tare dashi. Hakan kuwa yana faruwa ne saboda kodai kudin da ya ciwo bashi ya kashe wa matan banza. Ko kuma ya sadu da wata yana zullumin kamuwa da cuta. Ko kuma yana gudun kada wadanda yake ganin girmansu sun san abunda yake yi.
Don haka a kullum mai neman matan banza bai da natsuwa na hakika a tare da shi.
9: Zai Iya Shafar Abunda Zaka Haifa- Akasarin mazan da suka shahara wajen neman mata ana samun wasu daga cikin abunda suka haifa sun tashi da hakan.
Ga waɗanda kuma basu da auren da wuya suke samun gidan mutunci da suka san mutuncin kansu su amince su basu 'ya'yansu su aura.
10: Nisanta Mutum Da Allah- Da zaran namiji ya shahara a wannan fannin na neman matan banza to fa baya zabar irin macen da zai yi muaamala da ita. Budurwace, bazawara ce, matar aurece babu wacce yake bari muddin na shigo cikin 18 din sa.
Wadannan abubuwan da yake aikatawa a kullum yana kara nisanta kansa da kansa daga mahaliccinsa na kokarin fidda tsammanin yafiya daga Allah SWT. Don haka a kullum ba zai nemi tuba ba sai dai ya kara nisanta kansa da Allah.
Wasu kuwa wannan abun yakan sa su raina zunubin da suke yi su daina ganin wani laifi ne da Allah zai tambayesu idan sun mutum. Ta hanyar la'akari da wasu mutane masu aikata manyan laifuka, sai su rika ganin nasu ba laifi bane hakan sai yasa suna Kara nisanta kansu da Allah.
Wadannnan sune wasu daga cikin illar da suke tattare da neman matan banza da yakamata duk namijin dake fatan haduwarsa da Allah zai guje su.
Wannan na masu neman matan banza kenan. A darasi na gaba kuma zamu kawo hadarin dake cikin lalata budurwar da aka yaudara da sunan za a aureta. Ko macen da ta yaudari namiji ta kowa masa fasikanci.
#Tsangayarmalamtonga
Allah Ya shiryar damu hanya madaidaiciya, Ya kuma shiryar da zuriyar mu da dukkanin Musulmai masu nema shiriya.
0 Comments