Kasuwanci ya kasance gwagwarmaya, kuma faɗa da wasa ne kamar yadda wani masani ya faɗa. Duk wani mataki da dan kasuwa zai bi ya kokari ne don ganin ya samu riba da hanyar ɓillewa a kasuwancinsa. Yana amfani da ƙwazonsa da kuma dabaru don inganta kayansa da kuma hanyoyin faɗaɗa kasuwancinsa.
Amma duk da wannan ƙoƙari da yake yi, akwai wasu kura-kurai da za a iya samun shi da su, waɗannan kura-kurai kuwa sun zama ruwan dare a wajen yawancin ‘yan kasuwa walau sabon-shiga ko kuwa tsoho. Faɗawa cikin waɗannan kura-kurai kan iya janyo rushewar kasuwanci, ko nasabar mutum a matsayinshi na ɗan kasuwa.
Watakila a cikin waɗannan kura-kurai 12 da na zakulo za a iya samun wani wanda kake yi, ko kuma ɗan uwanka, maigidanka ko abokin kasuwancinka.
Na farko: ɗaukan waɗanda ba su cancanta ba a matsayin ma’aikata
Matasa da dama suna so a ɗauke su aiki musamman da zaran sun kammala karatu, babu ruwansu da aikin ya shafe ko sun cancanta ko saɓanin haka. Sannan su ma kamfanin ba sa duba cancanta ta ƙwarewa a wajen ɗaukan ma’aikata, kawai za su yi amfani da damar ‘yan’uwantaka ko sanayya ne su ɗauki mutane aiki. Haƙiƙa wannan kuskure ne babba domin ya na janyo rushewar kamfani ko min girmansa. Dole a yi la’akari da waɗanda suka cancanta domin samun damar gudanar da aiki yadda ya dace.
Na biyu: ƙoƙarin yin komai da ka
Cikakken ɗan kasuwa ya kasance wanda zai tsara yadda lamuran kasuwancinsa za su gudana, da kuma yadda suke gudana a kullum. Kuskure ne matuƙa rashin tsara yadda lamuran kasuwanci za su ke gudana. Misali, wasu suna riƙe yanayin samun ribarsu a ka ba tare da rubutawa ba. Ko kuma rashin rubuta wasu cinikayya, cigaba, faɗuwa da kuma darussan da akan ɗauka a sakamakon duk wani lamari da ya faru.
Na uku: rashin sauraron kwastoma
Babban kuskuren da ɗan kasuwa zai yi shi ne kore kwastomominsa. Rashin sauraron su ko biya musu buƙatu na daga cikin abubuwan da ke korarsu. Dole ɗan kasuwa zai rinƙa bibiyar kwastomominsa don sanin buƙatunsu, da kuma ɗaura ɗamarar biya musu su.
Na hudu: wuce gona da iri
Bai kamata ɗan kasuwa ya rinƙa wuce gona da iri a kasuwancinsa ba. Misali, akwai waɗanda suke bin wani tsari da Malam Bahaushe ya ke ƙira “sana’a goma maganin mai gasa”, wanda wataƙila kan iya kai wa ga rushewar kasuwancin mutum. Kwastomomi ko sauran mutane za su kasa sanin haƙiƙanin kasuwancin mutum, dan haka sai su tafi wani wuri. Shi kuma kasuwanci ba samun kuɗi ba ne kawai, nasara a kasuwanci (ko ina ma) ita ce ginuwa da kai. Idan mutum ya ginu da kansa da abunda ya ke yi, to daga nan duniya za ta san a me ya ginu, kuma ga ƙoƙarin da yayi waje kawo cigaba. Amma matuƙar ɗan kasuwa ya raba kasuwancinsa to ba zai san wanne zai inganta ba kuma daga nan akan iya samun matsala.
Na biyar: tsoron ɗaukar kasada
Ɗaukar kasada, kamar yadda aka cewa shi ne gwada sa’a a kasuwanci. Ko da mutum ya kasance sabo a kasuwanci ko tsohon ɗan kasuwa, to dole zai riƙi halayyar gwada sa’a domin gwabzawa a harkar kasuwanci. Ba zai yiwu wani ya gujewa ɗaukar kasada a kasuwanci kuma ya tsira ba. ko da zuba hannun jari, ko zuba jari ko makamancin haka da mutum zai yi ya danganta da gwada sa’a ne.
Na shida: saurin sarewa/yin kasa a gwiwwa
Mafi yawan mutane da sun fara kasuwanci sai su sare. Kuma ba kasuwanci kaɗai ba, yawancin sha’anonin rayuwa mutane sun kasance masu yin kasa a gwiwwa musamman a lokacin da suka fuskanci wata barazana, ko wahala, ko tangarɗa, ko kuma faɗuwa. Babu yadda za a yi wani ya iya shiga harkar duniya kuma ya kasance mai saurin sarewa a lokaicn da yake tunanin faɗaɗa ko samun nasara a harkarsa.
Na bakwai: rashin tsara kasuwanci
Tsarin kasuwanci shi ya kamata ya zo a mataki mai ƙarfi a lokacin da ake so a fara kasuwanci. Yana taimakawa wajen bunƙasa harkar tun kafin ya kasantu, rashin mayar da hankali kan wannan ya janyo rushewar dubunnan kananun sana’o’i har da manyan kamfanoni. Dole ɗan kasuwa zai kasance mai tsara lamuran kasuwancinsa da yadda abubuwan ciki za su kasance.
Na takwas: rashin mayar da hankali wajen dabarun kasuwanci
Dabarun kasuwanci, kamar yadda bature ya ƙira su “business strategies” su ne muhimman hanyoyin da ɗan kasuwa ya tsara ta hanyar bincike, nazari da tunani a karan-kansa da kuma tambayar ma’abota sani don cigaba da faɗaɗa harkar kasuwancinsa. Ba kowaɗanne irin dabarun kasuwanci ne masu aiki a ko ina ba, wataƙila wata dabarar kasuwanci da tayi aiki wa wani ba za tayi maka aiki a kasuwancinka ba, don haka ɗan kasuwan zai ɗauki ɗamarar yin nazari, tunani da bincike don gano waɗanne dabaru ne za su dace da kasuwancinsa.
Na tara: rashin lokaci
Mafi yawan ‘yan kasuwa suna samun matsala ne a lokacin da suka rasa isashshen lokacin gudanar da lamuransu. Wasu suna rufe kasuwancinsu a lokacin da mutane suke buƙata, don haka mutane sai su bi wata hanya don samun maslaha ga buƙatunsu. Wannan lamari yana janye kwastomomi ne gaba ɗayansu ko min yawansu, domin kullum za su yi tunanin ba ka da lokacin gudanar musu da buƙatunsu.
Na goma: rashin rungumar cigaban zamani
Akwai wasu ‘yan kasuwa da ba sa mayar da hankali kan bunƙasa harkokin kasuwancinsu da fasahohi da dabarun zamani. A yau yadda bunƙasa kasuwanci yayi sauƙi ta hanyar fasahohin zamani kamar yanar gizo, amma sai wasu suke gudun faɗawa harkar, ba don tsoron wani abu ba sai don kasancewarsu ‘yan kasuwan gargajiya.
A zahirin gaskiya duk wani kuskure a nan babba ne da kan iya janyo rushewar kasuwanci ko koma-bayansa dungurungum, don haka ya kamata ka yi nazari kuma ka zakulo wanne kake yi daga ciki ko kamfanin da kake aiki don sanin hanyoyin da za ka ware don guje musu.
Rubutawa: Mohiddeen Ahmad
#ZoMuGinaKamfani #maimaici
0 Comments