Idan Kana Son Rike Ragamar Ikon Gidanka Ka Guji Yin Wadannan Abubuwan:





Sau tari magidanta maza suke jawowa matan da suke aure su ji sune suke da iko akan mazajensu ba mazajen ne ke da Iko dasu ba.

A zamantakewan aure, dole ne namiji ya tabbatar bai yi sakaci da ikon da Allah Ya daura masa ba, wanda duk namijin daya kasa kula dasu dole ne gidansa yafi karfinsa.

Ga wasu abubuwan da suka kamata maza magidanta su tabbatar basu sakaci da su ba game da matansu.


1: Kada ka sake ka bar matarka ta rika shiga mara kyau a duk lokacinda zata fita.

2: Duk rintsi kada ka bari matarka ta zama itake daukan dawainiyar gidan naku koda kuwa ta fika samu.

3: Kada ka sake ka rika sa matarka aikin kashe kudi ba tare da ka bata kudin yin hidimar ba.

4: Kada ka rika takura matarka ta rika ji tamkar a gidan yari take ba a gidan masoyinta ba.

5: Kada ka sake ka bari matarka na karban bashi a wajen 'yan uwanka idan ba kasuwanci ne a tsakaninsu ba.

5: Kada ka sabawa matarka bata ko yi mata abunda take so a kuma lokacin datake so.
Zamu ci gaba....

#tsangayarmalam

Post a Comment

0 Comments