Idan Kana Son Budurwarka Ta Rika Kewarka:




 Daure Ka Rika Mata Wadannan Abubuwan
 
☞ Cikin darusan dabarun da muke kawowa samari da ma mazan da suke soayya na yadda zasu cusa soyayar su cikin zukatan wacce suke sonta da aure taji kamar ta daurawa kanta aure da wannan. Wanna karon ma zamu ci gaba.

 
❑ Idan kana son mace ta rika kewarka to ka tabbata kaine mutum na farko da zata rika karanta sakon soyayyar sa da fatan alherinsa gareta a duk safiya.

❑ Haka kuma ka zama kaine mutum na karshe da take karanta kalaman sakon soyayarsa kamin tayi bacci.

❑ Muddin ka saba yiwa budurwarka haka duk randa ba kayi ba sai ta nemi dalili saboda sabo da kamata da su.

❑ Idan kana son budurwarka ta rika kewarka ka tabbatar kana da lokacinta a duk lokacin da take bukatar ganinka.

❑ Bata lokaci a lokacin da ita take son ganinka yakan yiwa budurwa tasiri fiye da kaine kake son ka ganta.

❑ Don haka da zaran tace tana bukatar ganinka, to ka tabbatar ka bata lokacin da kasan zaka iya zuwa domin sauraronta.

❑ Matan da suke samun irin wannan kulawar a wajen samarinsu suna matukar son samarin nasu yadda idan suka bukace su basu gansu ba sukan shiga damuwa.

❑ Idan kana son budurwarka ta rika kewarka ka tabbatar duk lokacin da kuke tare kana tarairayenta kamar kwai. Kana kula da ita.

❑ Kalaman da kake furta mata masu ratsatane. Kana bayyana mata irin yadda darajarta yafi na duk wasu mata.

❑ Macen da take samun wannan kulawar wajen mai sonta nan take yake shiga ranta kuma ya mamaye mata zuciya da zata ji idan bashi ba maza suke kare.

❑ Idan kana son mace ta rika kewarka ka tabbata cewa kana mutunta iyayen ta da duk wani na kusa da shi.

❑ Mata suna son wanda yake daraja nasu. Matukan kana daraja iyayen budurwarka zaka shiga ranta kuma ta rika kewarka a kullum saboda yadda na kusa da ita zasu rika zancenka.

#itsangayaramalamtonga

Post a Comment

0 Comments