HATTARA GAME DA CUTAR KWALARA :




Mecece cutar kwalara? cutar kwalara cutace da take saurin kashe Al'umma, wanda kuma tasamo asaline daga wata kwayar cuta wadda ake kira da (VIBRIO CHOLARAE)  

Alamomin cutar kwalara:
*Ciwon kai (Headache)
*Zazza6i mai zafi (Fever)
*ciwon ciki (Abdominal pain)
*Gudawa (Diarrhea)
*Kasala (Weaknesses)
*Amai (Vomiting)

Yaya ake kamuwa da cutar kwalara? Ita dai cutar kwalara ana kamuwa da itane Sakamakon cin abinci gur6atacce (MARA TSAFTA) dakuma ruwan sha. Musamman idan ba a tsaftace wajen d'iban ruwa dakuma wajen sarrafa abinci da kuma na sha.

Matakan kariya daga cutar kwalara sun had'a da:

1_Nesanta mai d'auke da wannan cuta daga cikin jama'a (ISOLATION)

2-Wanke hannu kafin da kuma bayan cin abinci (Washing hands before and after food)

3-tsaftace wajen d'iban Ruwan sha(proper sanitising the water source)
4-Tsaftace kayan lambu(fruit and vegetables) kafin amfani dashi

5-Wayarwa da Al'umma kai akan muhimmancin lafiya (publicHealth awareness)

6_Nesanta wajen d'iban Ruwan sha da Bandaki (Distancing water source from self conviniancies)

7-tsaftar muhalli da tsaftar jiki (proper Environmental sanitation and hygiene )

8-Zubar da shara inda ya dace (Proper waste disposal)

9- A tabbar an dafa Abinci ya dahu sosae domin kashe qwayoyin cuta ( prolonged cooking)

10-idan anga mai dauke da alamar cutar a hanzarta sanar da hukuma ( Notify the appropriate authority)

11- Ziyar tar Asibiti mafi kusa damu domin duba lafiyar mu,(visit Nearest healthcare centre for medical investigation)

Lafiyar ku abar alfaharinmu!
You're Health is our concern!!!

NADABO H,H


Post a Comment

0 Comments