HAKURI A ZAMAN AURE (‘YAN UWA MATA):







HAKURI yana da matukar riba a rayuwa (bama a zamantakewar aure kadai ba) abun da yake damun wasu ma’auratan shine gaggawa da rashin hakuri, zaka ga mutum yana fadin cewa yana cikin matsala amma kuma abun mamaki shine bazai iya hakuri akan matsalar ba. Musamman a banganen mata ki sani cewa wani abun fah dole take kamawa idan kika kasa hakuri na kankanin lokaci wallahi hakan sai ya jawo miki shiga matsalar da sai kin dauki tsawon lokaci bki fita a ciki ba. 

‘YAR UWA kiyi tunani ki gani lokacin da za’a kawo ki gidan ki kowa idan ya gama miki huduba a bun da yake cike hudubar dashi shine a rinqa hakuri, kada kiyi zaton dan su basu samu soyayyar mijinsu bane (su wadanda suke miki nasihar) a’ah wallahi wata a cikinsu soyayyar da mijinta ke gwada mata ke koh rabinta bazaki samu ba, amma da zaki tambaye ta meye jagoran wannan zaman nasu sai tace miki hakuri, haka shima ta bangaren mijin.

GIDAN MIJINKI guri ne wanda kike bakuwa a cikinsa, kin bar inda aka sanki aka san matsalar ki, kinje inda ba’a san ko daya daga ciki bah, a da nauyinki ake dauka amma a yanzu dole ke kike daukan nauyin wasu (wanann shine girman) hakuri da kawaici kuma su zasu jagorance ki matukar kina son samun sauki a cikin al’amuranki.

*KADA ZAKIN SOYAYYA TA KWASHE KI* har kiyi zaton kin tsira daga barazana koh fadan mijinki a’a wallahi sai kin yi hattara ke zaki fi kowa shan fadansa (domin kin fi kowa kusanci dashi) (a halin da kuka kasance a karkashin inuwar aure) matukar baza ki rinqa kiyaye abun da baya so ba.

*WATA YAR’UWA* ana auranta aka kirata ana mata nasiha sai tace nidai kun dameni da nayi hakuri nayi hakuri, tunda yana sona ina sonshi kam ai shikenan, wallahi koh shekara daya ba’ayi ba rannan nakai mata ziyara sai take cewa Aminah ashe da ake cewa nayi hakuri nake ganin an dameni da gaskiyar su yanzu wallahi har gani nake hakurin da aka ce nayi ma yayi kadan.



Share this:

Post a Comment

0 Comments