DUNIYAR MA’AURATA
Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Yau kuma ga bayani kan dabaru, hikimomi da sirrin da ya kamata magidanci ya yi amfani da su don ganin ya zauna lafiya da matansa kuma ya wanzar da cikakken adalci a tsakaninsu:
Assalamu Alaikum,
Na karanta dukkan bayananki a kan ladubban karin aure kuma na gamsu. Don Allah ki yi mana karin bayani a kan dabaru ko wasu hikimomin zama da mata sama da daya, domin zama da mace daya gami da yin adalci gare ta ba karamin abu ba ne, to ina kuma ga an tara har 4, kuma kowacce halinta daban, bukatunta daban; ya maigida zai bi don ya kasance ya zauna da kowaccensu lafiya kuma ya ba kowacce cikakken hakkinta na rayuwar aure?
-Baban Muhd, Kaduna
Dubara ta 1:Bin umarnin Allah Madaukaki
Babban abin da zai taimaki magidanci ya zauna da matarsa ko matansa lafiya shi ne, bin umarnin Allah Madaukakin Sarki kan yadda ya kamata ya yi zamantakewa da matansa. Alkur’ani ya kasance dauke da kyawawan bayanai ga magidanta kan yadda za su yi hulda da matansu. Za mu kawo wasu daga ciki hade da yin bayani kan yadda za a aiwatar da su don cin ribar rayuwar aure duniya da lahira.
1. Alheri da kyautatawa: Allah SWT Ya yi umarni mai karfi ga magidanta cikin suratul Nisa’i Aya ta 19 cewa:
“….Kuma ku yi zamantakewa da su (mata) da alheri…”
Sannan idan muka dubi ayoyin cikin Suratul Bakara da suka yi bayani kan saki da sauran hanyoyin rabuwar aure (228-241), kusan kowace aya sai an yi umarni da aikata alheri da kyautatawa ga mata a cikinta; to a maganar saki ma ke nan, ina ga shi zaman auren kuma?
Don haka sai magidanci ya daure ya huldanci dukkan matansa da alheri da kyautatawa, ya sa wannan niyya a zuciyarsa, ya tabbatar da ita kuma ya karfafa ta; ya kasance a kowane lokaci; na dadi ko na rashinsa; na wahala ko na kwanciyar hankali, alheri da kyautatawa su ne za su yi wa maigida jagoranci wajen hulda da matansa; indai maigida ya rike wannan kuma ya dage da aikata shi, to da wuya ya samu matsala cikin rayuwar aure da matansa, dama abin da ke kawo matsala ga rayuwar dan Adam shi ne, kin bin umarnin Allah Madaukakin Sarki da bin son zuciya da zugar shaidan.
2. Su tufa ne gare ku
Allah Madaukaki ya bayyana ga magidanta a cikin aya ta 187 cikin Suratul Bakara cewa: “Lallai ku tufa ne gare su, su ma tufa ne gare ku.”
To ya mutum yake wa tufarsa in har yana son ta yi masa amfanin da ya kamata; Watau ta suturta shi, ta kawata shi, ta ba shi kariya daga sanyi ko kura ko ta fito da kimarsa ko ta daga darajarsa? Ai dole sai ya kula da ita sosai, daga ta yi dauda ya wanke ta ya goge, ya feshe ta da turare, sannan ya ajiye ta a wuri mai kyau inda kura ko wani datti ba za su iske ta ba ballanta su bata ta; to haka ya kamata a ce maigida ya aikata ga matansa; ya kula da su ta hanyar samar da duk wani abubuwan bukatar rayuwa gare su; ya karrama su ta hanyar kyautatawa gare su da yin kyakkyawar zamantakewa da su; ya tattala su ta hanyar ba su kariya daga duk wani abu da ka iya cutar da su a rayuwarsu ta duniya da lahira.
Kuma ya aikata haka ga duk matan da yake aure ba wai ya zabi wata ko wasu ya kyale sauran ba, domin in tufa daya mutum yake tattalawa da adanawa, to ita kadai za ta yi masa amfanin da ya kamata lokacin da ya sanya ta, amma sauran da ya bari da dauda ko wata yagar da ba dinke ba, ko a yamutse ba guga, duk lokacin da ya sanya su ba za su yi amfani gare shi ba, sai dai su rage masa kima da daraja ko su munanta masa kamanni. Kowace irin tufa ana sanyata ne da irin yanayinta ko siffarta, to haka ko wace mace sai a zauna da ita da irin yanayinta ko halayyarta, don samun sauki da dadin rayuwar aure.
3. Matanku gonakinku ne…
Haka kuma a cikin aya ta 223 cikin Suratul Bakara dai, Allah Ya ce:
“Matanku gonakinku ne, (don haka) ku je ga gonakinku ta inda ranku ya yi muku, kuma ku gabatar da alheri domin kawunanku.”
To yaya manomi ya kamata ya yi wa gonarsa idan har yana son ta ba da amfani mai kyau? Sai ya kula da ita sosai ta kowane fannin da take bukatar kulawa; ta hanyar nome ta da yin kaibe; sa mata takin da ya dace da ita; wata sa’in ma har da tsaronta don kare ta daga dabbobi da ka iya shiga su yi barna a cikinta.
Kuma a ce manomin da ke da gona hudu, ai in yana son dukkansu su yi masa amfani; su ba da yabanya mai kyau, ai dole sai ya kula da su ta hanyar da ta dace- kasar wata gonar ta fi bukatar taki don ta ba da amfani mai kyau, wata gonar kuma ita ta fi bukatar isasshen ruwa sama da takin, wata kuma yawan kaibe take so sama da komai, to kowacce sai a yi mata abin da ta fi bukata don a samu amfani mai yawa daga gare ta. Kowace gona yakan kasance akwai inda manomi kan samu matsala da ita, amma saboda alheran da za ta kawo masa sai ya yi ta hakuri haka nan ya yi ta noma abinsa; to kamar haka magidanci ya kamata ya huldanci matansa; kamar yadda Madaukakin Sarki Yake cewa:
“Sa’annan idan kun ki su, akwai tsammanin ku ki wani abu alhali Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa.” Nisaa’i, 19.
Don haka sai a yi ta hakuri da raunin mata da karkacewarsu don fatan samun irin wannan alheri da Allah Madaukakin Sarki Ya ambata.
0 Comments