Dalilan dake kawo mutuwar aure:



Matsalar kuɗi:

idan mutum yana cikin wadata za'a iya yi mashi abubuwa kuma zai iya jurewa ba tare daya fusata ba, amma idan ya samu karayar arziki to cikin sauƙi ran shi zai iya ɓaci. Don haka matsalar kuɗi zata iya kawo rashin fahimta a tsakanin ma'aurata kuma daga bisani ta janyo mutuwar aure.

Yin auran wuri: a lokacin da mutum yake ƙarami zai iya tinanin wani mutum sa'an soyayyar shi ne, amma sai bayan ya girma ne zai fahimci ba haka lamarin yake ba. wannan ne yasa yawancin soyayyar da samari suke yi bata ɗaurewa. idan mutum yayi auran wuri ba tare daya riga ya gama fahimtar kan shi ba to rashin fahimtar juna zata iya tasowa daga bisani.

Yin aure kafin ka fahimci ko kai wanene: Duk wasu abubuwa daka yi imani dasu kayi imani dasu ne sakamakon yawan maimaitawa tare da tabbatar maka dasu, da irin wannan maimatawa tare da tabbatarwar ce yasa wasu yaran da iyayensu Kiristoci ne suke tasowa a matsayin Kiristoci, hakan ne kuma yasa yaran da iyayen su Musulmai ne suke tasowa a matsayin Musulmai. Yawan maimaitawa tare da tabbatar da magana ce yasa yaran da iyayensu mabiya addinin Hindu ne suke tasowa a matsayin mabiya addinin Hindu.

 To yanzu me kake tsammanin zai faru idan mutane suka riƙa rainawa mutum wayo? Lalle babu shakka daga bisani zuciyar shi zata koma ta yadda da cewa shi darajar shi ba ɗaya take dana sauran mutane ba don haka bazai samu wani mutum wanda yasan ciwon kan shi ba da zai yadda ya aure shi. To irin wannan mutumin duk wata macen daya samu zai iya aura amma bayan yayi auran kuma sai ya sake samun wasu abokai waɗanda suke daraja shi kuma ya samu wani aiki ko sana'a mai daraja, daga bisani sai ya fahimci kuma yawancin mutane suna yi mashi kallon mutunci, daga nan sai ya fara tunanin cewa ashe shima yana da kima da daraja kamar sauran mutane, to yanzu bai kamata ace na samu mace wayayyiya ba kamar ni? To anan ne zai fara tunanin sakin wannan matar

Yin aure domin neman yardar mutane: Idan mutum baya son aure amma sai yayi auren bisa tinanin mutane suna yi mashi kallon raini sakamakon rashin yin aure, sai daga bisani ya fahimci ai baya buƙatar yardar mutane kafin jama'a su riƙa yi mashi kallon mutunci. Babu shakka zai saki matar domin zai ga baya buƙatar ta.

Auren mace saboda sha'awa kawai: Idan namiji ya auri mace ne saboda sha'awa ta jima'i kawai, to kuwa son da yake yi mata zai gushe idan kyan jikin ta ya gushe sannan fatan jikin ta ya saki sakamakon tsufa ko haihuwa. Kuma daga nan tinanin sakin ta zai faɗo mashi a rai
Rashin tsafta da gyara jiki: Idan namiji ya auri mace mai tsafta kuma wannan tsaftar da gyaran jikin da take yi sune suka ja hankalin shi ya aure ta amma sai bayan sun yi auren ta zama mara tsafta to anan soyayyar da yake yi mata zai fara dusashewa kuma daga nan zai fara tunanin rabuwa da ita
Yawan kula wasu mazajen tare dayi musu magana.

Idan ya kama matar shi da kwarto ko idan matar ta kama shi da kwartuwa.
Kasancewa namiji ya zama bawan mace: Wato idan namiji ya zama shi ne zai riƙa yiwa mace komai kaman yi mata wanki shara ko kuma ya zama ɗan aiken ta. Wani zai yi mamakin cewa ta yaya za'a yi mata suƙi son namijin da yake kyautata masu? to dalilin kuwa shine yawwncin mata suna son namiji ne mai ƙarfin zuciya (namiji wanda ya yarda da kanshi) sannan basa son namiji mai rauni, kada kuwa kasancewa bawan mace na tabbatar da cewa namiji yana da rauni. Don haka shi yasa idan namiji ya zama bawan mace hakan kenan yana nufin za zama namiji mara ƙarfin zuciya kuma mai rauni domin ya yarda cewa itace ke gaba dashi ba bai shi ke gaba da ita ba.

Idan namiji ya kasance baya jagorancin mace ba ko bashi yake iko da ita ba, to soyayyar da mace ke yiwa irin wannan namijin itama tana dusashewa.

Haka ma idan namiji yana nuna cewa yana jin kunyar mace ko tsoranta shima soyayyar da take yiwa irin wannan namijin tana dusashewa.

Post a Comment

0 Comments