Bysadeek sadboi
Shin ka shirya ko kuma kanaso kadaina shaye shaye?
Ka ci gaba karantawa domin cin moriyar gudun mawarmu.
Wannan guide din namu zai temaka wajen bada gudun mawa domin daina abinda kakeso ka daina.
Halayyar shaye shaye wata irin halayya ce wadda mutum yake bunkasawa kansa da kansa tunda koyonta akeyi.sannan abu ne wanda idan kanaso ka bari dole sai kafi karfin zuciyarka ko kuma abinda ma yafi hakan .domin tana matukar wahalar bari sosai.shan miyagun kwayoyi ko giya ko wiwi da sauransu yana kawo chanji a cikin kwakwalwa.wanda yawan amfani dasu yakan jawo ya zamar maka kamar dole sai ka sha abinda kakesha,kuma wanna abinda yake saka ka kasha koda bakaso shine abu mafi karfi sosai wanda har yafi karfin zuciyarka.kuma har hakan yana iya jaza aringa maka kallon wanda bazai taba yin nasaraba a rayuwa.amma ka sani daina shayeshaye abune wanda zaka iyayi kasi da kanka,ba abu bane wanda bazaka daina iya bariba har abada ko da ace kayi kokarin bari a lokutan da suka wuce kuma baka dainaba ko kuma wani hali da kashiga na tausayin kai.amma idan akace akwai treatment da taimako mai kyau tare da bada hadin kai toh chanji yana yiyuwa.
Mutane da dama da suke dauke da addiction ,lokacin day a dace ka daian shaye shaye shine tun lokacin farko da ka farad a kuma lokacin farko da kayi tunanin bari,saboda lokacin ne zai fadama cewa lallai kanada matsala kuma kanaso ka rabu da ita kuma ka samu chanji a rayuwa.
Yakan jawo chanjin abubuwa kamar:
1-yanda kake yi da gajiyarka
2-wanda yake a cikin rayuwarka
3-abinda kakeyi idan kana free
4-yadda kake daukar kanka da kanka
5-kalolin magungunan da kake shad a kuma yanayin bin dokar likita.
Normal kaji kamar bakason kadaina shaye shaye wasu lokutan,ko da ace kasan cewa yanada hatsari ko kuma yanada il a rayuwarka sosai.daina shaye shaye yana bukatar lokac,temakon kai , kwarin gwiwa da sadaukarwa.idan kanada wadannan suna iya saka ka ka samu chanji a rayuwar ka amma fah idan har ka shairya bari kai da kanka.domin ta hakane zaka iya yakar addction dinka sannan kayi control din sauran rayuwarka.
Ka fara tunanin chanzawa
1=ka fara bibiyar yanayi yanda kake shaye shayenka kamar adadin yawan abinda kake sha,yaushe kakesha,me ke sakaka kana sha.yin hakan zai baka damar sanin wasu bayanai na yanda addiction dinka yake da hanyoyin maganceshi.
2=ka fara fidda list din dalilan da yasa zaka daina shaye shaye da kuma tunanin rashin amfanin yin abinda kakeyi.
3=kayi tunanin abinda suke da amfani sosai a wajenka irinsu yaranka,yan uwanka,iyayenka,makotanka,abokananka,matarka,da aikin ko sanaar ka.
Sannan da lafiyarka. Kayi tunanin taya shaye shayenka ke cutarda wadancahn abubuwan.
4=ka tambayi wani dan uwanka ko kuma wanda kamyarda dashi shin ya yakeji a cikin zuciyarsa game da shaye shayenka.
5=ka tambayi kanka idan akwai wasu abubuwa da suke hanaka daina shaye shaye ko kuma abubuwan da sukeja kaki chanzawa.
Abubuwa biyar da zasu sa kadaijna shaye shaye
1-ka tuna ma kanka dalilan dayasa kakeso ka daina
2-kayi tunanin lokutan baya da ka fara tunanin bari.ida ka taba toh menene yayi maka aiki kuma menen bai yi maka aiki ba.
3-ka shairya ,kuma ka saka lokutan farawa da daina shayeshaye.
4-kacire abinda yake saka ka kana shaye shaye a zuciyarka irinsu abokananka na banza,a wajen aikin ka,
Makaranta, da sauran wurare.
5-ka fadama yan uwa da abokanan arziki zak daina shaye shaye domin su temake ka da gudun mawa irin tasu.
Ka zabi hanyar da zakabi domin chanzawa
Da zarar ka fara tunanin daina shaye shaye,toh lokaci yayi wanda zaka zabi hanyar da zakabi domin bari. Irinsu;
Dexoctation.wannan shine step din farko domin zaka sakak jikin ka dole yayi control din withdrawal symptom maana idan ya nuna a jikinka kamar mai shan sigari da zaka ga yayi baki.
Behavioural counseling.kungiyoyi ko family sukan iya temaka wajen ganin sun fada maka dalilan fara shaye shayenka kuma su taimaka wajen gyaran halayyarka,alakarka day an uwanka,lafiyarka da ayyukanka.
Medication.yana nufin magance shaye shay eta hanyar treatment na asibiti,gyaran kwakwalwa da sauran magunguna da zasu taimaka wajen chanzawarka.
Long term follow up.hakan yana nufin bibiyar wadan da suke baka shawarwari na dogon lokaci irin su kungiyoyi da kuma zuwa meeting akai akai .hakan zaisa ka chaza halinka na shaye shaye.
Ire iren treatment domin daina shaye shaye.
1-residential treatment.hakan yana nufin zama waje daya da kuma daina zuwa duk wani wajen kake shaye shaye da kuma abubuwanda suke tilastamaka kayi shaye shaye.irin wannan treatment din yana daukar watanni ko shekaru kafin mutum yayi normal.
2-day treatment.wannan kalan treatment din yana nufin wasu mutane wanda zasu so su daina shaye shaye amma basu bukatar killacewa,zasu zauna gidadomin zuwa binci kensu da duba su sannan kuma duk rana suna haduwa a treatment center na kamar awa 7 zuwa 8.sannan da dare yayi ka dawo gida.
3-Sober living communities.sober yana nufin haduwa a wani gida wanda akwai sauran masu shaye shaye wanda suma suna bukatar dainawa,hakan yana da dadi idan baka da wurin zuwa ko kuma kana tunanin dawowa gida zai sa ka koma ruwa da wuri.
Hanyoyin da zaka bi domin zabar treatment mai kyau.
Ka sani cewa ba ko wane treatment bane yake yi kowa aiki
Domin kowa yanada yanda yake shaye shayensa .ko da ace giya kakesha ko wiwi ko sigari.yakamata ka tsaya ka duba irin treatment din daya dace dakai.
Kuma ka dauki dena shaye shaye da mahimmanci domin shaye shaye yana da illa sosai a rayuwar ka,tare da lafiyark,aikinka,da kuma tunaninka.cin nasara a daina shaye shaye yana kunshe da samar da wata sabuwar hanya ta tafiyar da rayuwarka da kuma bayyana raayinka game da dalilan da yasa ka bar shaye shaye.ba mamaki fara chajinka ya samo asaline wajen tafiyar da gajiya ko kuma maganin damuwa.
Sannan kuma sai ka sami wata sabuwar hanya wadda zaka ringa tafiyar da lamarin gajiyarka da kuma damuwarka.
Daina shaye shaye ba abu ne mai sauki ba ko kuka abu wanda zaace zaa barshi lokaci daya.
Sanna nkamar yanda kake neman hanya ta daina shaye shaye , ya kamat ace kana neman wata hanyar ta magance sauran matsalolin lafiya da kuma sauran matsalolin dake damunka domin shaye shaye yana haifar da matsaloli da dama .
0 Comments