Wasu Abubuwa 12 Da Yakamata Duk Uwa Ta Koyawa 'Yarta Kamin Ta Aurar Da Ita:



 
Iyaye mata sunada gagarumin aiki a gabansu musamman wadanda suke da 'ya'ya mata a gabansu.

Ita 'ya mace ba kamar da Namiji bane. Tana bukatar kulawa na musamman a gaba daya rayuwanta.

Duba da yadda duk wani gida macece ke da rike da ragamar shirya wannan gidan. Hakan ya zamewa iyaye mata suyiwa 'ya'yansu mata horo na musamman kamin su aurar dasu.

A wannan darasin mun tunatar da wasu mahimman abubuwan da uwaye ya kamata su tarbiyantar da yaran su mata kamin su aurar dasu.
 
1: Tsafta- Shine abu na farko kuma muhimmi da duk uwa ya kamata ta tarbiyantar da 'yar da yinsa.

A nuna mata mahimmancin da tsafta yake ga 'ya mace a rayuwarta kamin aure da bayan aurenta.
A tarbiyantar da ita yadda zata tsaftace kanta a lokacin da take ganin wankinta. Lokacinda ta yi aikace aikace na gida. Da kuma tsaftar muhalli.

Koyawa 'ya mace tsafta kamin tayi aure ya zama wajibi wajen iyaye.
2: Ado da Kwalliya- Ita mace 'yar ado da kwalliyace, wanda akasarin maza suna sha'awar ganin matansu bayan sun tsaftace jikinsu da muhallinsu, ka sance kuma suna yin ado da kwalliya hakan ne zai sa idan tayi aure mijinta bazai ji kyashin saya mata kayan da zata masa ado da kwalliya ba. 

3:Zama da Kuma Kwanciya- Yadda 'ya mace take zama da kwanciyar ta ba daya bane da Da namiji.

Irin matan da suka kasa samun wannan tarbiyan za a ga ko bayan girmansu da aurensu duk inda suka zauna zasu bude kafafuwansu basu iya zama da kafafuwa a rufe ba.

Haka nan idan zasu kwanta barci dole sai da wando a tare da su domin baza iya kwanciya ba tare da sun gwale kafafuwansu ba.
Muddin aka aurar da mace da irin wannan halin hakan na iya jawo mata kaskanci ko ma ya kashe mata aure.

4: Magana da Iya Tafiya- Yana daga cikin abunda ya zamewa iyaye mata dole na su koyawa 'ya'yansu mata yadda mace take magana da kuma tafiya.

Ita mace ba kamar namiji take ba wajen magana da tafiya. Saboda yadda take da tattausar murya ba a so mace idan tana magana koma da wanene ta riga daga muryarta sama da na wanda take magana dashi koda kuwa na kasa da ita ne.

Haka mace ba a so tana tafiya kamar namiji ta buga kasa da karfi ko tana jan kafa a kasa. Duk wannan mata sun fahimci abunda ake bukata a wannan bangaren.

Koyawa 'ya mace wadannan abubuwan suna da mahimmanci domin zasu taimaka mata a zaman aurenta. 

5: Ladabi da Biyayya- Babban abunda yake da mahimmanci kenan fiye da sauran abubuwan da muka lissafo.

Dole a koyawa 'ya mace sanin mutuncin mutane ta hanyar yi musu ladabi da biyayya.

Ka nuna mata sanin darajar na gaba da ita da kuma mutunta na kasa da ita. 

Koyawa 'ya mace ladabi da biyayya kamin aurar da ita zai bata damar yin mu'amala da kowa da zata tarar da wadanda zasu tarar da ita a gidan mijinta musamman 'yan uwa da abokai da mutanen da mijinta yake hulda dasu. Hakan kuma zai bata damar zama da mijin nata lafiya.

6: Tattali-Wani abu mai mahimmanci kamin aurar da diya mace shine a koya mata da nuna mata yadda ake tattali da alkinta duk wani abu na gida.

A nuna mata yadda zata alkinta kayan abinci ko wasu iri da kuma tattalin duk wasu sutura ko kayan kwalliyar da za a saya mata.
Yana kuma da kyau a nuna mata yadda zata kashe kudi idan an bata na kula da gida ko kuma na kashenwanta.

Macen da aka mata wannan tarbiyan sune a duk randa miji bai da shi take taimaka masa.

7: Haramci Gori- Mata da dama ana siffantasu da iya yin gori akan duk wani abunda suka yiwa mutum a baya hatta mijin da suke aure.
Hakkin uwaye ne a lokacin yiwa yaransu tarbiya kamin aure su nuna musu haramcin yiwa mutum gori da kuma ladan dake akwai na yin abu tsakani da Allah. 

8:Godiya- Akoyawa 'ya mace iya yin godiya da duk kankantar kyuatar da aka mata ko wani abun alheri da za a mata ko aka riga aka mata.
Yaba kyauta na sa mai yin kyauta ba zai gajiya ba wajen bayarwa. Amma idan mace ta zama wacce bata yaba kyauta bazata karfafawa mijinta mata kyautan ba.

9: Girki-Duk uwar data kasa koyawa 'yarta iya girki wannan uwar batada niyar aurar da diyarta da kuma niyar ta zauna zaman aure na har abada.

Yiwa miji girki na cikin abubuwan da suke sace zuciyar namiji akan matarsa. Haka nan rashin iya wannan girkin na nisanta miji ga matarsa.

Bama rashin iya girki ba, mace ta iya amma ta kasa samun lokacin yiwa mijinta wannan girkin tamkar tana warware aurenta ne da kanta sannu a hankali. 

10:Kissa- A dunkule wannan abunda muka lissafo a sama idan aka dunkula su waje guda aka sarrafasu cikin hikima da dabara da nunawa namiji kauna cikin soyayya shine ake kira kissa.

Hakkin iyaye ne su nunawa 'ya'yansu mata yadda ake yin kissa a zaman aure wanda yana da bambamci da zama gaban iyaye.
Ita mace ladabi da biyayya tsagoronsu da wani iya girkinta ta hada da ado da kwalliya da sarrafa girki ba zata iya mallakar miji dasu ba har sai idan ta iya kissa.

11: Jima'i- Akwai wasu muhimman abubuwan da uwaye mata ne ya kamata su karantar da yaransu mata game da Jima'i kamin suyi aure amma ba wasu can a waje ba.

Tsaftace gaban mace kamin Jima'i da bayan Jima'i dole ne mace ta san yadda zata yisu.

Haka nan nunawa 'ya mahimmancin gamsar da mijinta a lokacin Jima'i da abunda zata yi masa bayan nan bai zama abun kunya ko kyama ba ga iyayen da suke burin aurar da yaransu zaman aure na har abada.

12: Kula da Addini- duk wannan abunuwan da muka jero muddin ba ayiwa 'ya mace tarbiyan kula da addini ba duk zasu tashi a banza.
Da zaran iyaye sun horas da 'yarsu akan turba na addini to zasu samu saukin kai wajen yi mata sauran tarbiyan. Don haka daura yara mata akan koyarwa na addini shi ne tushen yi musu duk wani tarbiya kamin suyi aure. 
 
Allah Ya bamu sauke nauyin tarbiyan dake kanmu. Da samun dacen aurar da 'ya'yan mu mata ga mazan da suka dace.

Post a Comment

0 Comments