✿✿╥ ✰✰✰ *ℳU FARKA ℳATA*✰✰✰ ╥✿✿
╦╦╦╦╦╦╦╦╦╦╦╦╦
╥╥╥╥ ❐❐ *HIRA DARE* ❐❐ ╥╥╥╥╥
*✆ WhatsApp*
*☏ +2348037538596*
♜ *_DUNIYAR・・ℳA'AURATA_* ♜
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
*Mu Lura da wannan 'yan'uwa na mata, Hira dare nasa mai-gida ya daina fita yawo da daddare, saboda baya samun hirar dare daga gareki, kuma Galibi idan suka fita, sai sun raba dare Ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke kuma sannan kin yi barci, kinga irin wannan ina amfaninsa?*
_Kin dinga jawo hankalin mai-gida ki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar banza kamar ZINA ya debo cuta, shan giya da sauransu._
*_A kullum bayan sallah isha'i idan akaci abinci, sai a dasa Hira, har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to yau kullum idan ya ga ki na yawan damunsa da hirar._*
*To Zaki ga ya dawo yana so, muddin ki ka Saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba amma idan kika yi sakaci ya Saba da fita, to duk randa kika so ya Bari ba zai Bari ba.*
*[•ℳU FARKA ℳATA•]*
*✆ WhatsApp*
*☏+2348037538596*
╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
⊂( ̄ ̄)⊃•• *ABINCI* ••⊂( ̄ ̄)⊃
*BARIN ℳA ℳAI AIKI RAGAMAR ABINCIN ℳIJINKI DA GIDANKI*
🍲🍜🍛
_Wannan babbar matsala ce, musamman ga matan masu kudi da kuma mata masu aikin gwamnati da matan sarauta_
_Ma'ana anan shine sai kaga mace ta zauna ta mike kafa a gida ba zata tashi ta yima mijinta girki ba._
_Koda kuwa yai tafiya ne ya dawo, sai dai ta sa mai aikinta_
*Wai ita Hutu !*
*_MU FARKA MATA_*
*Duk mai wannan halin gara ma tun wuri ta daina, ko kuma ki sakar ma mai aiki ragamar gidanki, kama daga*
☆ abinci 🍛
☆ kula da yara
☆ aikin gida
*Gyaran dakin ki Dana mijinki.*
_Ko kuma idan mai-gida yasa ki aiki, kice ma mai aikin ta tashi tayi!_
_Sai kace ita ya ajiye, ba ke ba, ya kasance idan ba wurin kwanciya ke babu wani abu da Zaki iya masa komai sai (HOUSE GIRL) wannan kuskure ne babba._
_Muddin kika zauna , sai ta zauna miki domin kina da tashin hankali a gabanki , saboda ko mai aiki bata nuna tana son sa ba, shi zai iya nuna yana sonta, ko ya Fara tunanin Kara aure, don haka kar ki bada ragamar dawainiyar mijinki da me aiki, mu gyara wannan halin namu._
🍛🍲
╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
💔. *KOWACE DA MATSALARTA* 💔
Ma'ana :
*Duk macen da take gidan miji babu wacce bata da matsala.*
*Amma kowa da irin Nata, don haka hakuri akeyi, ko ba miji ba, sai kin samu da uwar miji ko uban miji ko dangin mijinki.*
*Ko kishiya, ko yayyin miji, ko kannin miji, shi zama ya gaji Haka, zo mu zauna ,zo mu Saba, duk abinda ya sameki kiyi kokari ki magani matsalarki, ba tare da kowa ya Sani ba.*
★ *duk sabinin daya sameki tsakanin ki da mijinki, ki yi kokarin boyewa a gaban mutane, saboda gudun wani ya San halin da kuke ciki , kiyi kokarin sharewa, har Ku sulhunta ,saboda masu shigo wa gidanku.*
★ *_KASHE AURE BA NAMU BANE._*
☆ yaji ba namu bane balle idan kina da yara, kin ga kashe aure ba naki bane, duk abinda ya faru, muddin ki ka nemi Saki 📃
☆ idan da gayya yake miki, kin ga ya samu abin yi dama haka yake so, ga kuma ta samu, kin nema da kanki, amma idan kika share, kin kunsa masa bakin-ciki a daina kawo maganar Saki akan karamin abu.
*'YAN-UWA MATA MUYI KOKARI MU SACE ZUCIYOYIN MAZAJENMU*
_ta hanyar kyautata masu ta hanyoyi da dama, saboda mu zauna daram dam dam!_
*A zuciyar su komai aka miki, kiyi hakuri ki zauna, wata Rana sai labari.*
┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳
*_KADA KI ZAUNA A CIKIN DUHUN KAI_*
*ma'ana shine duk abinda kika San baki Sani ba.*
⊂TA FANNIN ⊃
☛ KWALLIYA
☛ KULA DA HAKKIN MIJI
☛ GIRKI TARAIRAYAR MIJI
to ki nemi mai koya miki a cikin sirrin ko kuma kina iya
Zuwa
*☏+2348037538596*
*Sirrin rike miji*
✿ WhatsApp
✿ gmail
✿ text message
*Kan yadda Zaki kula da mijinki ki karanta ki koya*
Amma ba wai ki zauna cikin duhun Kai ba, kina cutar kanki ne
Kuma wadannan abubuwan shi a wurin sa mai-gida ba zai taba cewa baki sabi ba, haushinki zai dinga ji, to tun ba azo rikici ba, kije ki koya, idan baki iya ba, saboda haka mu dinga Hulda da mutanen kwarai wadanda zasu wayar mana da Kai, domin idan mijinki dan gayu ne, muddin baki waye ba ta fannin aure da gayu, to fa komai ki ka yi, zai dinga hantararki, yana nuna miki tsana.
Kuma koda fita zai yi, idan kina da kishiya yar gayu ita zai dauka, ke kuwa cewa zai yi babu Inda za shi dake kina masa kauyanci da duhun Kai, 'yan uwa mu kula da wannan, kada mu zauna cikin duhun Kai .
╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
*_KADAN DAGA CIKIN FALALAR JIMA'I_*
﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏
_Zaki samu a duk lokacin da kika farantawa mijinki wajen kwanciya._
❒ *ke ma zakiji dadin kwanciyar*
❒ *zai Kara miki so a zuciyar mijinki*
❒ *ga kuma kyautar da mijinki zai dinga miki, koda ba ki tambaye shi ba, tunda kina kyautata mai wajen shimfidarsa, dole shima ya kyauta ta miki.*
❒ *kuma zai rage sabani tsakanin ki da mijinki.*
*_Da sauran abubuwan wadanda masu yawa, Wanda ke zai amfana._*
┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳
✰✰・ *HANYAR ℳALLAKAR MIJI* ・✰✰
_________________________________________________
akwai hanyoyin dama da ake amfani dasu wajen mallakar mai-gida kamar haka:
● ki iya kissar kwanciya, da nuna masa kauna a wajen kwanciya
● ki so shi, ki so 'ya'yan sa da yan uwansa gaba daya
● Bari abinda bai so, da yin abinda yake so
● ki kasance mai masa ladabi da biyayya da bin dokokin daya gindaya miki
● tarairayarsa da tarba mai kyau a duk lokacin da ya shigo gida
● tsaftar jiki iya girki, da kula da tarbiyyar yara
● tausayinsa akan al'amuran da kuma idan yana cikin wani hali
● son ibada, imani da kyautatawa ga danginsa
\〇 *TUNATARWA* 〇/
Babu wani Wanda zai iya juyo miki da hankalin mijinki, da ya wuce ke, saboda haka muddin kika rike wadannan sai kin yi masa mallakar da ba macen da zata iya juya shi sai ke
✿ _SHAWARA GA MATA MASU AIKI_ ✿
*DON Allah 'yan'uwa mata mu dinga kokari muna kare mutuncinmu Dana mazajenmu a wurin. Da mike aiki, musamman masu aiki a (local government da state) saboda sai kaga matar aure ba ta da kawa a wurin aiki mace, duk abokanta maza ne! To ko baki da aure, ai bai kamata a matsayinki na mace sai rauni, balle kina da aure Ace kina abota da maza*
_Idan kina wannan kullum mutuncinki raguwa zai yi ba karuwa ba, kuma sai Allah ya kamaki ko kuma ya Kama mijinki ranar gobe kiyama, kin ja masa kenan, tunda shi daya bar ki zuwa aiki, bai yi tunanin haka Zaki yi ba._
*_Mu dinga kulawa da irin wannan, saboda sai kaga mace cikin kankanin lokacin tana abokai maza da yawa kuma ko ba kya fasikanci wannan fuskar da kika bayar , shi zai sa kare da biri kowa ya nemeki da fasikanci_*
_Saboda kin Saki kanki kin zama kamar haja a KASUWANCI,ki zauna kina Hira da su barkatai, ki na sakin zance da bai dace ba har Tafi da shewa.._
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
*AMSARKI ER UWA*
*TAKAETACCEN MATSI DA NI'IMA INGANTACCE*
*SIRRINA NA 1*
Kisamu bawon bagaruwa kidafa kirinka sit bath dashi mace mejego ko macen datajita a bude koda budurwace.....
*SIRRIN NA 2*
Kisamu garin xogale da kwaro da man kadanya da man shanu da man xogale ki hada kicakudasu su hade jikinsu sekirinka insert d la.asar xuwa magrib ko isha.i........
*SIRRIN NA 3*
Kisamu furen tunfafiya da yayan bagaruwa d garafuni kitasfa ruwan yahuce ykoma dan dumi kirinka yin tsarki dasu........
*SIRRIN NA 4*
Kisamu ganyen magarya da bagaruwa kitafasa kitace seki xuba turarem miski a ciki kirinka sit bath d tsarki...woooh ga kqmshi g gyaran hq...
*SIRRIN NA 5*
Kisamu lalle 1cup kidafa kirinka sit bath dashi g gyara gasa dumin jiki......
*SIRRIN NA 6*
Kisamu xuma kirinka dangwalowa kn insert nata....snn kisamu man xaetun d beby oil kirinka yashafawa a kasan hq xakiga gyara
*SIRRIN NA 7*
Kisamu tagargaje kidaka kidama ckn ruwa kirinka wanke hq...snn kisaka xuma....byn nn kuma idan xako kwanta sekiyi insert n almiski orginal......
*SIRRIN NA 8*
Kisamu nonon rakumi d garin ridi seki hada kirinka sha akae akae.......
*SIRRIN NA 9*
Kisamu man hulba da pure madara ta shanu kota ruwa peak d xuma kadan kihada kirinka sha fn ky barci d 3haurs knn.....
*SIRRIN NA 10*
Kisami kankana da madara kitace kisata a fridge kita sha.....kirinka hada gurji da xuma d madara kinsha....kirinka kunun aya dayaji kayan kamshi....yawaeta cin kayan marmari d kayan lambu.....snn kirinka amfani d sabulun xaetun d habba.......yawaeta amfani d ruwan dumi lkcn sanyi xaki iya amfani dn rijiya ko bamfamo sbd beda sanyi........
*Daukewar sha.awa*
kisamu nonon rakumi d garin kanumfari kihadasu kisa rabin karamin ckli n kanumfari d kofi 1 na nonin rakumi...kirinka sha sage d yamma........
Dafatan er uwa xata gwada wnn hanyoyin xata samu biyan bukata....ngd daga naku a kullum meson mace taxama zinariyar mace
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
*KARIN BAYANI*
*wani Karin bayani da Zan yi anan shine 'yan uwana mata muyi da gaske mu kame mazajenmu daga shiga gurbacewar rayuwa*
0 Comments