LITTAFIN FIQHU (DARASI NA 34.) :




RUKU'U DA ƊAGOWA DAGA RUKU'U.

Bayan ya gama karatun Surah kafin a tafi ruku’u, ana so a raba su kaɗan, wato kada ya haɗe karatun Surah da kabbara yayin yin ruku’i. Mutum ya xan yi shiru kaɗan domin akwai limamai masu haɗewa wanda wannan ba daidai ba ne.
Idan an gama karatun sura, sai an tsaya chak, sai a tafi ruku’i. Za a yi kabbarar ana tafiya ruku’u. Sai ya sanya hannayensa a kan gwiwoyinsa kamar yadda Annabi ﷺ ya ce, “Sannan ya yi ruku’u har sai ya nutsu a cikin ruku’u, ya tara hankalinsa.” 
Hakazalika, Allah ﷻ Ya ce: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku yi ruku’u.”
Malik Ɗan Huwaris (رضي الله عنه) ya ce, Manzon Allah ﷺ yana ɗaga hannayensa yayin da yake kabbara har sai sun zo daidai da kunnuwansa. Haka idan ya yi ruku’u yana ɗaga hannayensa har sai sun yi daidai da kunnuwansa.” ()
Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce idan Annabi ﷺ zai yi ruku’u ba ya noƙe kansa kuma ba ya ɗago kansa, yana kasancewa tsakanin haka da haka.
Abu Humaid Assu`udi (رضي الله عنه) yana cewa wasu daga cikin sahabbai na kasance mafi kiyayewar ku da sallar Annabi ﷻ. Ya kasance idan ya yi kabbara yana sanya hannayensa daidai kafaɗunsa. Haka kuma idan ya yi ruku’u yakan tabbatar da hannayensa a kan gwiwarsa, kuma ya buɗe ‘yanyatsunsa, sannan yana daidaita gadon bayansa.
A ina kan mutum ya kamata ya kasance yayin ruku’u? Wajibi ne mutum ya daidaita gadon bayansa yayin ruku’u, sai dai idan yana da wata larura wadda za ta hana shi yin hakan. Kuma dole ya daidaita kansa. Kada ya yi sama da shi kuma kada ya noƙar da shi, zai daidaita kansa yayin ruku’u.
Kuma duk wanda gadon bayansa ya yi ciki, ko ya yi waje, ta yadda idan an ɗora ƙwarya ko ruwa zai gangare ta ƙasansa ko ta wajen wuyansa, bai yi ruku’u ba, domin cikar ruku’u shi ne:
Mutum ya sa hannunsa a kan gwiwa ya kuma riƙe ta.
Ya daidaita wuyansa/kansa, kada ya yi sama ko ya yi waje.
Ya daidaita gadon bayansa, kada ya yi sama ko ya yi ƙasa.
Wannan ita ce siffar cikakken ruku’u.
Abubuwan da suke lalata ruku’u su ne:
1.Rashin riqe gwiwa.
2. Bayan mutum ya yi sama.
3. Bayan mutum ya yi qasa.
4. Wuyan mutum ya yi sama.
5. Mutum ya noƙe kansa.
Wanda ya yi wannan, bai yi cikakken ruku’u ba.
Ya zo a hadisin Rifa’a ya ce idan za ka yi ruku’u ka ɗora tafukanka a kan gwiwoyinka, sannan ka shimfiɗa gadon bayanka, ka daidaita shi.
Dole ne mutum ya zama ya nutsu a cikin ruku’u. Kada ya yi gaggawar ɗagowa sai ya yi tasbihi a cikin ruku’u, mafi ƙaranci sau uku. Amma za a iya yin fiye da uku saboda hadisin Huzaifa (رضي الله عنه) da ya ce, ya ga wani yana sallah ba ya cika ruku’u, ba ya cika sujjada. Sai ya ce masa ba ka yi sallah ba, ko sallarka ba ta yi ba, saboda ba ka cika ruku’u da sujjada ba. Kuma idan ka mutu a haka, da ka mutu a kan addinin da ba shi Allah ﷺ Ya aiko Manzo ﷺ a kansa ba. Hadisin Barra’u Ɗan Azib (رضي الله عنه) ya ce, ruku’un Manzo ﷺ da ɗagowarsa da kuma sujjadarsa kusan kansu ɗaya.
Huzaifa Bn Yaman (رضي الله عنه) ya ce, ya yi sallah tare da Manzon Allah ﷺ ya ji yana cewa a cikin ruku’u: 
((سُبْحانَ رَبِّيَ الْعَظِيمِ)). ()
Sau uku. Kuma a sujjada yana cewa: 
((سُبْحَانَ رَبِّيَ الأَعْلَى)) ().
Shi ma sau uku. Waɗannan lafuza duk sun zo a cikin AlQur’ani, faɗin Allah ﷻ:
﴿ فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ ﴾ () 
Da kuma faɗinSa ﷻ:
﴿ سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى ﴾ ()
A wata ruwayar, ya faɗi kowanne sau uku. Idan ya ƙara akan ukun babu laifi saboda hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) da ta zo da wasu kalolin. Ta ce Annabi ﷺ yakan yawaita faɗin:
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِكَ، اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي)) () 
Saboda Allah ﷻ Ya ce a cikin Alqur’ani:
﴿ فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ ﴾ ()
Da saukar wannan sura Annabi ﷺ yake faɗar wannan. Kuma zai iya cewa:
((سُبُّوُحٌ، قُدُّوسٌ، رَبُّ المَلاَئِكَةِ وَالرُّوحِ)) ().
A cikin ruku’u da sujjada. Auf Bin Maliki Al’Ashja’i ya ce Annabi ﷺ ya kasance yana cewa:
((سُبْحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، وَالْمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءِ، وَالْعَظَمَةِ)) ().
A cikin ruku’u da sujjada. Sayyidina Ali (رضي الله عنه) ya ce, Annabi ﷺ yana faxa a cikin ruku’u:
((اللَّهُمَّ لَكَ رَكَعْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَلَكَ أَسْلَمْتُ، خَشَعَ لَكَ سَمْعِي، وَبَصَرِي، وَمُخِّي، وَعَــــظْمِي، وَعَصَبِي)) ().
Yana cewa: “Allah gareKa na yi ruku’u, kuma da Kai na yi imani, gare Ka nake miƙa wuya da jina da ganina da ɓargona da ƙashina da jijiyoyina, duk sun ƙasƙanta sun miƙa wuya gare Ka, a cikin ruku’una.”
Kuma ana so mutum ya dinga sauya tasbihi, domin akwai daɗi da nishaɗi a cikin sassauyawar. Annabi ﷺ ya yi hani da karanta Alqur’ani a cikin ruku’u ko sujjada. Annabi ﷺ ya ce, “Ku saurara, an hana ni in karanta Alqur’ani ina ruku’u ko sujjada, amma shi ruku’u ku girmama Allah ﷻ a cikinsa, ita ko sujjada, ku ba da ƙoƙari wajen addu’a domin shi ne mafi cancanta a amsa muku.”() 
* * * *

ƊAGOWA DAGA RUKU’U
Liman da mai sallah shi kaɗai, za su ɗago daga ruku’u suna masu ɗaga hannu. Liman zai ce, Sami’Allahu liman hamidah, mamu kuma su ce, Rabbana walakal hamd.
Akwai saɓani ko mamu suma za su iya cewa Sami’allahu liman hamidahu ko kuwa sai dai a raba. Wasu suna ganin za a iya faɗa idan liman ya ce, Sami’Allahu Liman Hamidahu, mamu ma za su faɗa. Wasu suna ganin su ce, Rabbana walakal hamdu kawai.
Saboda hadisin Abu Huraira inda Annabi ﷺ ya ce, “Idan liman ya ce, Sami’Allahu liman Hamidahu, ku ce, Rabbana walakal Hamd, domin idan mutum ya faɗa ya dace da faɗar mala’iku, za a gafarta masa abin da ya gabata na kura-kuransa.” () 
Kuma ya zo da siga guda huɗu:
1. Allahumma Rabbana wa lakal Hamd.
2. Allahumma Rabbana lakal Hamd.
3. Rabbana wa lakal Hamd.
4. Rabbana lakal Hamd.
Duk wanda mutum ya yi a cikin waɗannan ya yi daidai.
Kuma ana iya qara:
((رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ، حَمْداً كَثيراً طَيِّباً مُبارَكاً فِيهِ)) ().
Ko kuma a ƙara da: 
((مِلْءَ السَّمَوَاتِ وَمِلْءَ الأَرْضِ، وَمَا بَيْنَهُمَا، وَمِلْءَ مَا شِئْتَ مِنْ شَيءٍ بَعْدُ. أَهلَ الثَّناءِ وَالْمَجْدِ، أَحَقُّ مَا قَالَ الْعَبْدُ، وَكُلُّنَا لَكَ عَبْدٌ. اللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الجَدِّ مِنْكَ الجَدُّ)) ().
Wannan duk ana ƙarawa, amma ba kowa ba ne yake iya haddacewa, idan ka ce: Allahumma Rabbana wa lakal Hamd ya isa. A kula sosai da sallah domin ita za a fara bincikawa ranar Alƙiyama idan ta yi kyau, komai ya yayi, idan kuwa ta ɓaci komai ya shiga garari.
ZA mu ci gaba insha Allah 
* * * *

Post a Comment

0 Comments