LARURAR GARGASA - TA FITAR GASHI BA BISA KA'IDA BA [HIRSUTISM]:



💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫

Aslm alykm, kamar yadda na alkawarta muku cewa; bayanina nagaba zan tattauna ne game da matsalar nan dakesa ganin gashi ajikin Mata a wasu gurare da azahiri Maza ne kurum akasan suna fidda gashi irin wannan to Allah cikin ikonsa ya nufa gashi. 

Toh saide bayanin akarkashinsa zai ta6o akalla maji6untan abubuwa guda biyu a dunkule da duk suna karkashin wannan matsalar kuma suna tafiya hannu da hannu wato [polycystic ovarian syndrome, hypertrichosis da kuma shi hirsutism].

________________________________________

HIRSUTISM: Wato Gargasa a hausance yanayi ne dake faruwa ga Mata inda suke ganin gasusuwa da ake kira "terminal hairs" warwatse na bayyana ajikin nasu kuma awasu kebantattun guraren da a Mazaje baligai ne kurum akanga hakan; Wato guraren da suka hada: Kan lebe (gashin baki), Saje, Gashin gemu, Gashi akan Nonuwa, Gashi atsakiyar kirji, Gashi a kasan ciki, Gashi agadon baya, Duwawu da kuma cinyoyi... 

Wato de in mun lakanci abun a center ko ince tsakiyar gundarin jikin mutum ake ganin gashin ba sassan gafe da gefe ba..... Eh mana saboda inka kalli Namiji ai duk wani gashi ajikinsa kusan a tsakiyarsa yake; Gashin kai, gemu, kirji, Ciki, Mara haka de zuwa farji.... sai kadan da suke peripheral wato gashin hannuwa.

----------‐-------‐----------------⁰-‐----------------------------

MEKE JAWO HAKAN

Shi wannan yanayi na Hirsutism akaran kansa ba'a kirasa da ciwo ba amma de yanayi ne dake kaiwa ga larura.

Samuwar kwayeye fiye da kima ajikin ovary din Mace, Ciwon adrenal gland dake saman kidney, Ta'ammali da magunguna masu kunshe da hormones, samuwar qari ko tumor ajikin ovary na Mace, Gado ko kuma tangardar kwayoyin halitta yayin goyon ciki.... na daga abubuwan dake haddasa wannan matsala.

----------‐-------‐----------------¹-‐----------------------------

YADDA ABUN KAN FARU SHINE

Yana faruwa ne sakamakon samar da sinadarin androgen da jiki keyi fiye da kima... inda shi kuma androgen din ke bin jini zuwa ko ina ajika, inda daga guraren da androgen kanje hatta ovary na Mace inda kwayayen haihuwar Macen suke acan cikin mararta. Bisa tsautsayi idan androgen yai kicibis da kwayayen halittar Macen koda tun acikin ciki yayin da ake goyon cikinta ne kafin haihuwa toh shikenan matsala ta afku.

Saboda shi wannan sinadarin na androgen shine me haifar da bayyanar suffofin Namiji.... murdewar jiki, gasussuka, murya, sassan jima'i, girman maraina da sauransu. Don haka ajikin Maza kaso mafi yawa yake domin shike taimakawa wajen fitar gashi ajika da sauran abubuwa kamar yadda akaji.

Mata ma nada androgen suma amma kadan ne baida yawa shine ke samar musu da gashin hammata, gashin kai, da farji. Sabanin ajikin Maza dake yana da yawa sai aga hadda gashin hannu, gemu, kirji da kusan ko ina.

Toh kamar kuma hakane sai Allah yasa Mata su kuma suna da sinadarin Estrogen me yawa amma kuma Maza dan kadan... wato saboda Estrogen shike samarwa da Mace cikar sura; Girman nono, Gyaran mahaifa domin daukar ciki, Goyon ciki, karfin sha'awa, laushin jiki, jinin Haila da sauransu, Yayin da mu Maza ke bukatar kaso dan kadan kacal saboda nonon dake kirjinka duk da bame samar da ruwa bane, sannan bamu da mahaifa bama daukar ciki, bama haila.

________________________________________

Toh idan ya zamto ansami tangarda a jiki wancan Androgen din dake taimakawa samuwar gashi ya zamto yana da yawa ajikin Mace kila adalilin gado ko tuntube cikin kwayoyin halittar dake samar da sinadarin jikinta zai zamto nada Androgen ko testosterone fiye da kima.

Wanda tunda munce aikinsa shine samar da gashi toh shine kesa Macen ta rika fitar da gashi har a inda bai kamata ba domin yawan natan babu bambanci dana namiji, shyasa duk inda za'aga gashi a namiji toh itama sai agansa jikinta. Wannan shine abunda ke faruwa.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Don haka anan nakeson cewa; Babu alakar fitar gashi a gemu, ha6a, gashin baki, nono, kirji ko duk wani sashi da nace wannan larura nasa agansa a Mace da zancen Maita, ku dena dorawa mutane Maita, ko dorawa wata kabila cewa duk wacce aka gani da gashi ai yar yare kazace. Wannan wulakantarwa ne, Qage ne, kuma wulakanci ne, walau hausa, kanuri, fulani, yarbawa, katafawa, barebari, zazzagawa kai koma de wanne jinisi ko jiha ce na mutane ana iya samun Mace me wannan suffar.

Ya kamata kowa yasan larurace, kuma kowa na iya samu cikin yayansa ya taso da matsalar koda babu me ita acikin dangi... Duk yada irin wadancan zantuka camfe-camfe ne da suka rika faruwa abaya sakamakon Rashin ilimi, Allah kadai yasan Matan da aka sa akunci ki aka kashe shekarun baya sakamakon zarginsu da maita alhalin ko kusa ba abunda ya hadasu da ita.

----------‐-------‐----------------²-‐----------------------------

SHIN DUK GASHI A MACE NE KE NUFIN HIRSUTISM GARETA ???

A'ah kamar yadda na fada a baya karkashin wannan alama ta gashi akwai wasu larurori guda 2 kari dake tafiya hannu da hannu domin suna da kamanceceniya da juna. A duk inda kaga Gashi de irin wannan gargasa toh kasani alamace ta sinadarin androgen jikin Mace fiye da kima.

■ Toh saide bayan hirsutism akwai kuma HYPERTRICHOSIS shi wannan tsananin fitowar gashin ne fiye da kima shima aguraren da ba'a saba gani ba walau a Macen koma harda Maza.

Domin a Hypertrichosis gashin cunkus za'a gansa akafafu, tsintsiyar hannu, kirji koma duk jiki baki daya, Kai har akan fuska, akan hanci akan sami gashi awasu. Wasu fuskarsu rufe take da gashi kamar kannuka, wannan hypertrichosis ne.

Saide shi hypertrichosis galibi yana da alaka da gadone bakuma na larura bane, Amma akan samu ya zamto yana faruwa ne sakamakon ciwon zakaran wuya wato thyroid, ko ciwon asassan kayan ciki dake narka abinci ko kuma cutar kin cin abinci don kar ai kiba wato anorexia Nervosa, Hakama wasu magunguna da mutum kesha na tsawon lokaci masu alaka da ciwon kwakwalwa, hawan jini, farfadiya, dashen wani organs da akai ma mutum da sauransu.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

■ Baya ga Hypertrichosis sai kuma POLYCYSTIC OVARIAN SYNDROME wanda shi idan anyi ultrasound ne za'a samu kwayayen haihuwar na Mace wato ovaries sun kasance da yawa cunkus fiye da kima waso sama da kwaya 10 ko 14 zuwa sama, wanda kuma ajika itama za'a ganta da gemu, yana fitowa.

Galibi a polycystic ma iya gemu suka fi zuwa da complaints saboda abun sai ahankali inba adau mataki ba zai yawaita yakai ga kirji, da nono da ciki, da saje duk arika ganin gashin.

Infact aduk sanda aka ga Mace me wannan suffar ko complaints din shine abu na farko da muke fara kawowa.

Dukkansu abu uku dinnan ba abun so bane.

----------‐-------‐----------------³-‐----------------------------

SHIN KO GASKE NE ZATON MU NA MATA MASU GASHI KWAI WANI ABUN DABAN TARE DASU

Allah sarki, ance rashin sani yafi dare duhu, magana ta gaskiya babu wani abu waishi ni'ima da Mace me gashi ajika tafi sauran Mata, hasali ma in kun fahimci bayani na ai larurace dake bukatar matakan binkice da zakuji agaba. Don haka shi jima'i kamar yadda nakan fada jikine keyi amma zuciya ke sarrafasa idan kai a ranka gashin kakeso to duk sanda ka sadu da ita ganin gashin shi zaisa ka ka gamsu bawai abunda kaji jikinta ba, koda abushe take kuwa. 

Kamar Maza ne wani komi ni'imarta zaka ga inbabu nono cikakke dazai ja hankalinsa gareta ko saduwar ma bai damu ba, amma da yaga Mace mai tsayyayen nono toh shikenan hankalinsa ya tashi, Haka kuma wani shima Mace me faffadan kugu yakeso.. duk de... don haka babu wata ni'ima ta daban ga Macen dake da gashi ajika, hasali ma larura ce su kansu acikin damuwa suke saide in rashin sani, wanda shine dalilin post din don ankarar dasu.

----------‐-------‐----------------⁴-‐----------------------------

ME YASA A LIKITANCE HAKAN KEDA JAN HANKALI

Dole wannan abu yaja hankali domin akwai tarin hatsarurruka na lafiya da rayuwa dake tattare da Mace me dauke da irin wannan gashin ajika wanda baza ace lafiya kalau ba harsai abunda binkice ya tabbatar daga baya.

Domin da yawa kan rika fisge ko aske gashin da daya-da daya sanda ya fara bayyana musamman agemu tunda nan bazai boyu ba, don gudun tsangwama amma a zahiri ba batun askesa bane damuwa domin ko an aske zai kuma tohowa, toh duk abunda zaka aske kuma kaga ya qara fitowa kuma kasan azahiri bai kamata ma ace akwai shi a inda kike ganinsa ba matsayinki na Mace ai ya kamata ya zamo abun daukar hankali ki nemi ganawa da masana, ba kurum rika tattauna matsalar tsakanin Matan da kila basu da ilimin lafiya sam.

Mu a likitance ganin wanna kadai kai tsaye munga abunda ka iya kaita ga manyan matsolilin da zasu kaita ga:

- Rashin haihuwa
- Ciwon zuciya
- Yawan zubewar ciki
- Kansar mahaifa (endometrial cancer)
- Ciwon hanta dalilin kitse
- Hawan jini
- Haduwa da stroke wato shanyewar jiki
- Kiba da nauyin jiki
- Cutar damuwa da fargaba (Anxiety & depression)
- Ciwon sugar saboda tasirinsa na kaita ga insulin insensitivity wanda zai haddasa ciwon suga ajika.
- Ciwon sankara wato kansar kwayayen haihuwa (ovarian cancer).

Wannan duk complication da zasu iya faruwa in mutum yaki magani in angano matsala. Amma yin maganin zai bada kariya ya kiyaye aukuwarsu, koda zasu auku abun bazai muni ba.
----------‐-------‐----------------⁵-‐----------------------------

MENENE HATSARIN DA MACE ME HAKAN KE CIKI

Kamar yadda nace duk Mace me wannan larurar na cikin hatsarin kamuwa da ciwon sugar, ciwon zuciya, ciwon cancer, hawan jini, da kuma rashin haihuwa.

Wani abu kuma fitacce dasu dama duk inda zakaga masu Hakan to zakaga BASU da GIRMAN NONUWA saboda effect na androgen din ga estrogen dinsu. Hakanan yayin physical exam bayan sun kwabe zaka sami abunda ake kira CLITORIS dinsu ko dan tsaka yana da kauri da girma... wanda kaga duk wannan ma sai azaci wani abun baiwa ne, wanda inajin kilama shiyasa ake ganin kamar sunfi ni'ima.

Don haka abun kunga ashe ya wuce yadda ake zatonsa. Har sai in bayan dukkan anyi gwaje-gwajen da ya dace ayi amma ansamu komi within normal toh sannan ne za'a iya cewa Mace nata bame hatsari bane zuwa yanzu illa iyaka zata rika zuwa follow up lokaci lokaci.

Hakanan a wata Macen rashin daukar matakin kariya ko maganin ka iya kaita ga abunda ake kira VIRILIZATION wato aji Murayarta ta karye irinta Maza sak, sannan taga nonuwanta sunqara kankancewa sun zube, sannan ga bayyanar sanko akanta, sakewar fata, katon clitoris a farjinsu... dade sauran suffofi da suka sha bamban dana lafiyayyar Mace.

----------‐-------‐----------------⁶-‐----------------------------

ALAMOMIN LARURAR PCOS

Sun hada da:

Rashin ganin haila akai akai ko kuma ma aga ta dauke baki daya.

- Rashin samun juna biyu duk kokarin da ake, saboda galibi basa ovulating irin wannan matan ko kuma sunayi amma ba kowanne wata ba

- Bayyana gashi ajika musamman aguraren da a Maza akafi gani kamar yadda na fada abaya; fuska, kirji, ha6a, baya ko duwawu

- Wasu zaka gansu da kiba wato te6a already, duk da wasu slims ne

Gashin kansu baida wani kauri sirara haka za aga gashin kansu

Maikon afuska koda ba'a shafa mai afuska ba, wasu kuma pimples sosai.

Alal hakika wadannan sune mahimman abubuwan da irin wadannan mata suka kebanta da wasu cikinsu

Don haka kema mai karatu watakil ta yiwu kema yanzu da baki kai ko baki ba 25yrs baya ba kina cikin hatsarin matsalar amma baki sani ba, saide in cikin yan uwanki ko mahaifiyarki nada irin matsalar toh saiki shirya......., domin a wasu kai tsaye matsalar kan bayyana ne daga shekarun da suka fara haila, wasu kuma sai bayan sunkai shekaru 25 aduniya. 

Wannan shine damar da Auren wuri kanba wasu aga sanda matsalar ta bayyana Allah ya taimakesu sun aure tun sauna irin 17, 18, 19 ko 20yrs don haka suna da ýaýa biyu ko 3 alokacin, abunda ya kawosu asibiti shine haihuwarce ta tsaya sunzo suji yaya? Kurum sai agano matsalar...

Shiyasa wasu duk da matsalar na hana haihuwa amma sai kaga sunyi sa'a suna da ýaya daga baya matsalar ta bayyana bayan sun ba 25yrs baya ko sun doshi 30yrs.

----------‐-------‐----------------⁷-‐----------------------------

MENENE ABUNYI YANZU KENAN LIKITA

Kamar yadda nace karki taba yadda wata tace miki ai kalau kike bakomi, abunda ya kamata inda rashin sani ne yasa kika share duwawu kika zauna toh yanzu saiki damara ki tashi zuwa asibiti kiga likita... babban asibiti inda ake da Medical doctors ko wadanne irine inde medicals ne su daga nan zasu turaki department din da ya dace in sunga bukatar hakan, ko kuma su fara treating dinki da kansu.

----------‐-------‐----------------⁸-‐----------------------------

ME ZAN TSAMMANIN JI KO GANI

Abu na farko shine kije da shirin cewa bayan kin gama bayani toh likita zai ko zatai exposing dinki in Mace aka hadaki da ita, zaki cire kayanki za abaki gown kila kisa... domin zata ga pattern na gashi da kuma duk inda suke gaba da baya, sama zuwa kasa. Daga nan zata hada findings dinta da abunda kikai bayani. Dole ne sai anyi miki physical examination don kar ai skipping wani mahimmin abun

Daga nan za'a baki gwajin jini kiyi wanda ya kunshi sinadarancan na Androgen, free testosterone, prolactin, TSH da sauransu.

Haka nan daga nan zasu baki scanning shima dole ne domin aduba ovarys dinki agani. Musamman in anasameki da wadancan suffofi.

Domin abun tausayi wasu galibi sanda zasu zo asibiti sakamakon jahiltar matsalar ko wasu sakarkaru can dake nuna musu babu komi zaka samu har sunyi developing ciwon suga wato type 2 diabetes😢. Don haka karki zauna.

----------‐-------‐----------------⁹-‐----------------------------

ME ZAN TSAMMANIN JI IN GWAJIN YA FITO

■ Idan aka sameki da polycystic ovaries, ga hormones sunyi high, kuma ga gashin dama ya fara fito miki ta tabbata kina da polycystic ovarian syndrome din, don haka duk hatsarurrukan can dana lissafa baya kina cikinsu don haka sai kin kula sosai.

■ Idan kuma ya zamto wasu babu gashin amma incodental ansami polycystic ovary.... domin wasu ciwon mara ke kaisu sai aga polycystic ovary amma babu alamun gashi to awannan a iya cewa normal musamman in cikin haila akai scan din illa iyaka gaba inkinga bayyanar gashi toh ki kawo kanki asibiti inbaki gani ba shikenan.

■ Wasu kuma ga gashin amma hormones duk normal level, kuma ovary normal toh suma za'a ce physiologic ne ba wata matsala a wannan lokaci saide zasu cigaba da follow up zarar aka sami wani canji ko aga samun ciki yai wahala.

----------‐-------‐----------------¹⁰-‐----------------------------

SHIN ANA WARKEWA DAGA WANNAN LARURAR

Amsa: Eh kuma A'ah! gaskiya inde anyi diagnosing Mace da PCOS toh saide aita managing amma ba'a warkesa kwata-kwata amma ana dora mutum kan magunguna kuma ya sami saukin fitowar gashin, tare da man da zaike shafawa inya aske. Ko kuma ai masa laser treatment gashin ya dena fitowa baji daya inyai sa'a

Haka zalik za'a baki magungunan da zaki amfani dasu ki dauki ciki ki kuma haihu lafiya ba wata matsala da ikon Allah.

Sannan in already mutum ya sami ciwon suga to itama za'a ke bashi magani domin managin din larurar sugar din don kaucewa hatsarurruka.

----------‐-------‐----------------¹¹-‐----------------------------

ZAKI HADU DA HATSARINE IDAN

Ya zamto kinga wannan bayanin, kuma kinsan kina da larura ko kasan kanwarka nada larurar ko Matarka amma kaqi yin komi akai na taimaka musu ko kikaqi yin komi na nemawa kanki mafita ta hanyar zuwa kiga likita a tantanceki.

Kamar yadda nafada MANYAN LIKITOCI medicals da ake iya samu kai tsaye a manyan asibitoci irinsu Teaching hospitals, Specialist Hospital, Ko Federal Medical Centers (FMC) sune kadai ke iya adressing wannan matsalar, su za'a agani insha Allah, dole sai anga mutum ido da ido, babu wani me baka magani online.

________________________________________

FATAN AN FADAKA, AN KUMA ILMANTU Game da larurar, Allah ka yaye, ka saukaka mana, kasa mu wanye Aamin.
________________________________________

✍🏼
[Ibrahim Y. Yusuf]
03062021-0555a

Post a Comment

0 Comments