KURAJEN PIMPLES NA FUSKA :



🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊🧊

Acne abunda mutane suka fi kira da pimples abunde dake samun kaso me yawa na mutane musamman Mata, duk da cewa Maza ma kan samu wannan matsalar ta kuraje a fuska amma MATA su suka fi damuwa dasu fiye da Maza. 

Su suka fi tambayoyi akan yadda za'a magance su, kuma munsan a zahirance ma mata mutane ne yan kwalliya musamman masu hasken fatar ciki bazance farare ba. Haka ma Mazan a masu hasken fata sukan damu.

Kurajen tayani muni na alikitance suna daya daga cikin matsalolin dake shafar fata masu addabar samari da ’yan mata. 

Suna fitowa ne a daidai lokacin girma ko balaga domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke wadatuwa acikin jiki wanda hakan kan zamto triggers na pimples din.

Wannan sinadarin tare da taimakon abunda ake kira sabeshiyos giland suke da alhakin samar da maiƙo afata har takai ga ya rika taruwa akan musamman fatar fuska ta yadda taruwar maikon a fuska ke ba kwayoyin cuta na bakteriya damar samun muhallin taruwa awurin su haifar da toshewar kafofin gashi tare da sanya ƙurji akan fatar wanda shine in an matse za'a wani ya bulluso da farin ruwa-ruwa ko aga ba ruwan sai yar farar kwaya data fito daga ciki.

Galibi sakamakon bakteriya din wacce akan kira da "firofiyonobakta akne" shikesa koda anbude kafar gashin data toshe karshe ingun ya tashi warkewa yake barin tabon duhu afata, wanda wannan shine babban abunda yafi damun mutanr masu hasken fata.

Sannan yawanci yafi fitowa agurin da bacteriyar tafi samun maiko; wasu kumatu, wasu kasan mukamiki, wasu pimples din akan karan hanci, wasu agoshi, kai wasu har akirjinsu.

SAIDE BAYA GA BAKTERIYA AKWAI TRIGGERS

Triggers kamar abubuwan dakan qara bashi damar fitowa ko addabar mutum musamman cikin abinci ko wasu dabi'u, wanda ya hada da: Shan nonon shanu, cin gyada, cin abincin waken suya, ko cin wake, ko cin toyayyen dankali, ko chips, ko white rice, ko cake. Duk wadannan a wasu sukan iya zama triggers na fitowarsa

Haka ma; Rashin wanke brush din shafa powder ko canzasa akai akai, da rashin wanke rigar pillow akai akai, da yawan tattaba fuska bayan waya📲 ta jima rike ahannu, kwanciya bacci da kwalliya afuska, ko kuwa yawan zama kasancewa cikin stress.

Hakama canzawar sinadaran halitta hormones musamman yayin ko bayan haila yana kawo fitowarsu duk da sukan 6ace, hakama duk da binkice bai tabbatar ba amma ana ganin masturbation ma na qara sanya bayyanarsu.

HANYOYIN KARIYA DAGA PIMPLES

■- Idan ka fahimci triggers din da aka ambata akwai guda dakai ma ka fahimci inkaci ko kayisa sunfi fitoma toh saikai kokarin yin baya baya da triggers din matukar pimples din na damunka, domin ko ansa magani sun mutu inbaka rabu da triggers ba basa fasa fitowa.

■- Abu na gaba shine kiyaye taruwar maikon dake ba kwayoyin cutar pimples din damar zama a fuska, wuya da kirji, duk da wannan kan danyi wahala amma za'a ci nasara in anbi ta wadannan dabaru :

1. Rage maiko a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci yana da kyau atsane mai da mayanin kitchen wipe mai tsabta kafin aci. Idan anyi haka anrage man kusan da kashi hamsin cikin dari koma fiye. inkoman sosai ne toh inba dole ba a hakura, banda cika mai a abinci

2. Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma (medicated soap) ko kuma normal plain sabulu.

3. Shan yayan itatuwa da cin ganyayyaki akai-akai yakan tsane maiko acikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta.            

4. Dena yawan tattabasu, kurum abarsu, inda zasu matsu amatse, wanda bai matsu ba abarsa acigaba dasa magani.

5. Ga wanda wadannan dabaru basu yi musu aiki ba zasu iya zuwa su nemi man shafawa a fuskamai dauke da sinadarin benzoyl peroxide 5%, ko ointment su salycylic acid 6% , azleic acid 10% cream, bioderm ointment da sauransu

Da akan shafa safe da yamma bayan an wanke fuska da ruwan dumi. Ko sau 3 ayini.

6. Idan hakan yaqi wadatarwa toh sai anje asibiti anhada da karbar magungunan sha na kashe kwayoyin cutar tare dana shafawar masu karfi.

8. Ba'a so a rika matse kurajen saboda hakan wasu lokutan shi kan jawo tabo bayan su mutu, anfi so a barsu su fashe da kansu sai a wanke wurin ko kuma asami tsaftattar allura ahuda, asami me tsaftataccen hannu ya matse, duba da yadda sukansa duhu jikin fata.

[[Ibrahim Y. Yusuf]]

Post a Comment

0 Comments