Jerin abincin da ba su dace da lafiyar mai-ciki ba:



Wannan karo mun shiga zauren kiwon lafiya mun kuma kawo maku wasu abinci da masana harkar kiwon lafiya su ka haramtawa mace mai dauke da juna biyu. Daga nau’in abincin da aka hana masu ciki ci akwai:

1. Ganyen da ba a wanke ba

Duk da cewa ganye na da amfani musamman ma ga mai ciki, amma dole masu juna-biyun su kiyayi cin ganye irin su latas da alaiyyahu da ba a wanke da kyau ba.

2. Giya

Ko ya mai ciki ta sha giya yana iya yi mata mugun illa. Haka nan kuma ana so masu shayarwa su guji giya domin tana iya kawo babbar matsala a jikin su.

3. Sinadarin caffeine

Haka kuma ya zama dole mai ciki ta kiyayi daukar abubuwan da ke dauke da caffeine. Sinadarin na iya jawo bari, ko haihuwar bakwaini ko a fito da yaro ba lafiya.

4. Madarar da ba a dafa ba

Masana sun bayyana cewa dole mai ciki ta kiyayi shan danyan nono na madara da ba a tafasa ba. Madara na dauke da listeria wanda zai iya yi wa mai juna biyu illa.

5. Kifi da nama da kwai

Masu ilmin kiwon lafiya sun haramtawa masu ciki cin ‘danyen kwai da ba a dafa ko aka soya ba. Haka kuma a guji kifin (na gwangwani ko wanda aka gasa ko wanda ya sha wata cuta a ruwa) sannan kuma guji cin naman da bai nuna ba.

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments