Babban bambancin da ke tsakanin sallah babba da karama shi ne, ita karamar sallah da an sauko Idi an ci tuwon sallah shi kenan babu sauran hidima sai ta ziyara.
Ita kuwa babbar sallah a kan shafe kusan kwana uku ana hidimar aikin naman dabbar da aka yi layya da ita.
Sai dai wannan wani al'amari ne mai cin rai ga mata da yawa amma kuma mai sa nishadi ga wasu matan ganin cewa daga bana sai badi irin wannan hidima.
A wannan maƙala ta musamman BBC ta yi duba ne kan hanyoyin da mata za su bi wajen sarrafa naman layyarsu don samun saukin lamari.
Mun tattauna da Malama Maijiddah Badamasi Shu'aibu Burji, wacce malamar dabarun sarrafa abinci ce kuma kwararriya kan sinadaran abincin a makarantar 'yan mata ta Karkasara a Kano.
Ta gaya mana hanyoyi 13 da za ki bi wajen sarrafa ko adama naman layyarki.
1. Kina iya ƙuƙƙula naman a ledoji bayan an yayyanka, sai a sa a gidan kankara na firij.
2. A yayyanka nama a tafasa a ƙuƙƙula a leda a sa a firinji. Amfanin tafasawar shi ne ko da za a ɗauke wuta to ba zai yi saurin lalacewa ba.
Sannan kuma zai dinga saukakawa uwagida a yayin da take son yin girki cikin sauri. Shi ma ruwan naman ana iya zuba shi a roba mai murfi a sa a firij don a dinga girki da shi.
3. A soya naman sosai sai a adana ana amfani da shi har ya ƙare.
4. Ana kuma iya soya shi sai a zuba a cikin kakide, duk lokacin da ake son ci sai a sake soya shi sama-sama ko a dumama a na'urar zamani ta microwave.
5. Ana iya yin dambun nama a adana shi. Shi ma ya kan dade bai lalace ba.
6. Ba lallai ki soya naman layyarki duka ba. Za ki iya dabarar yin farfesu da wani bangare na naman.
7. Za ki kuma iya yin kilishi da wani bangare na naman don shi ma ya kan dade ana ci bai lalace ba.
8. Malama Maijidda ta ce a ranar sallah da kwanaki kadan din da za su biyo bayanta ma kina iya ɗiban ɗan naman a yi gashi a ci.
9. Sannan akwai tsire da shi ma za ki dan iya yi wa iyalanki don su samu sauyi.
10. Kuma za ki iya yin kwallon nama wato meat balls ta hanyar tafasa naman da kayan kamshi da na dandano sai kuma a daka shi a turmi a cuccura kamar ƙwallo a tsoma a cikin kwai sai a barbade shi da garin burodi sai a soya cikin mai.
Wadannan kadan kenan daga cikin dumbin hanyoyin da za ki bi wajen sarrafa naman layyarki.
Sai mu ce a ci gaba da bikin sallah lafiya a kuma ci nama a hankali.
0 Comments