HALAYE BAKWAI (7) MARASA AMFANI DA DUK WANI TALAKA YAKE DASU:




1. Suna Kara yawan kudin da suke kashewa dazaran sun Sami Karin kudi. Masu arziki Suna amfani da Karin kudin da suka samune wajen sanyasu a kasuwanci Domin Samun riba.

2. Suna Zama ko abokantaka ko harka da mutane wadanda basuda wata manufa ko Nasara arayuwa.

3. Suna Burin Samun arziki haka Kawai batareda sun Tashi sun yi kokari ba, don haka suke shiga caca irinsu betnaija, mmm dasauransu Domin suyi kudi batareda Shan wahala ba.

4. Suna zargin wani (iyaye, Yan uwa, oga awajen aiki, gwamnati dasauransu) da laifin hanasu Samun abinda sukeso arayuwa. Masu arziki Suna kallon matsalarsu amatsayin nasu don haka sune zasu maganceta dakansu.

5. Basu girmama lokaci. Suna Bata lokaciinsu ne wajen Danna waya, chatting, kallon TV, gulma, Zaman majalisa dasauransu. Masu arziki Suna kallon lokaci amatsayin kudine don haka Suna amfani da lokaci wajen Cimma burinsu Na Rayuwa

6. Sun yarda da jira. Suna cewa "komai lokacine" "banida jarin fara kasuwanci" don haka sunajiran arziki yabiyosu Har gida. Ka taba ganin Wanda yake zaune yaci gasan tsere/gudu? Dole kafara yin abu kafin kasami Nasara aciki

7. Basu Hango Kudi a kusa dasu. Sunada basira, kwakwalwa, hazaka, ilimi, iya magana, hikima dasauransu Amma sunkasa amfani dasu Domin samarwa kansu kudade. 

KUBIYOMU ZAMU CIGABA DA KAWO MAKU SIRRORRIN SAMUN NASARA ARAYUWA. KUYI SHARING WANI ZAI IYA KARUWA DA WANNAN

Post a Comment

0 Comments