GYARAN FARATAN KAFA DA HANNU:




Farce yana da amfani kwarai da gaske ta fuskar ginuwar jiki. Sai dai hakan ba zai samu ba sai idan har mun ba su kulawa ta musamman. Lafiyayyu kuma kyawawan farata su ne wadanda suke sumul-sumul babu wata gargada ko karkacewa a jikinsu. Za ki samu cewa gaba dayansu sun

zama launi guda ba tare da wani dameji na rauni ko tabo a kai ba. Ga wadansu hanyoyi da muke ganin matukar za mu kula da bin su daki-daki, to za mu samu biyan bukata na mallakar kyawawa kuma lafiyayyun farata

YANKE FARCE YANA DAGA CIKIN TSAFTA YAN'UWA
 
MATAKAN GYARA

• 1)- Ki kula da farcenki ta hanyar zuwa salun akai-akai.
 
•2)- Ki guji tara farce ya yi tsayi mai yawan gaske, wato akwai bukatar su zama a yanke a koyaushe.

•3)- Ki guji cire farce da hakori. Ko da ya zama cewa wani abu ya taba farcenki ya yi irin dagowar nan, kada ki sa hakori ki cizge shi, domin hakan zai sa ya fita ba bisa ka’aida ba ta yadda har zai sa a tsarin farcen ya zama wani iri daban. Wato sai ki ga wani bangaren na farcen ya fi wani tsawo. A maimakon haka ki sami reza ko kuma abin yankan farce da ake kira da nail cutter ki yanke farcen da shi.

•4)- Kada ki bari farcenki ya zama a jike koda yaushe, domin hakan zai sa ya rika kakkaryewa tun kafin ma ki kai ga yankewa. Idan ya zama za ki yi aiki da ruwa, yana da kyau ki sami irin safar hannun nan ki sa, don ta kare miki faratanki daga lalacewa.

•5)- Kada ki yi amfani da alkamashi wajen yanke farcenki, ko da farcen ya kasance mai rauni ne, balle kuma ga wanda ba shi da wata matsala.

•6)- Bayan kin kammala da yanke faratanki za ki iya samun man farce ki shafe su da shi, wanda hakan shi zai sanya faratanki su rika walkiya da sheki, ba lallai sai kin sanya jan farce ba.

Idan har ke mai sha’awar tara farce ce to ki tabbata cewa kina kula da su ta hanyar fitar da duk wata dauda da ke shiga cikinsu ta zauna. Idan kika kula barin dauda ta zauna cikin farce ba shi da kyawun gani a ido ma, ballantana ga lafiyar jiki.

Post a Comment

0 Comments