𝘾𝙄𝙒𝙊𝙉 𝙎𝘼𝙉𝙔𝙄..𝙒𝘼𝙉𝘿𝘼 𝘼𝙆𝘼𝙁𝙄 𝙎𝘼𝙉𝙄 𝘿𝘼 𝙄𝙉𝙁𝙀𝘾𝙏𝙄𝙊𝙉...:




Akalla a kowacce shekara ana samun sama da case miliyan daya da rabi (1.5 million cases per year) na cutar infection kuma mafiyawan cases din mata ne. Kuma wadanda kawai sukaje asibiti banda wadanda sukaki zuwa da wadanda ke neman maganin gargajiya (federal ministry of health 2019)

 Cutar sanyi ko infection cuta ce da ta addabi mutane da yawa yan sama da shekara 15 mata da maza. Cutar tana kama wajen fitsari ne ga mata da maza..

𝙈𝙚𝙠𝙚 𝙠𝙖𝙬𝙤 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧?
1. Kwayoyin cutar bacteria kamar su
Nesseiria gonorrhoea, escherichia coli, streptococcus aureus da sauran grand negative da grand positive bacterias. 

2. Kwayoyin cuta na fungus da kashe kashen su.. 

💥 𝙏𝙖𝙮𝙖𝙮𝙖 𝙖𝙠𝙚 𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧?
1. Ana daukan cutar sanyi ne tsakanin macce da namiji, duk wanda keda cutar yana iya likawa wani lokacin saduwa,
2. Ana iya dauka cutar idan kin saka panties din mai cutar ko gajeren wando mai cutar.
3. Idan mai cutar taje toilet 🚽 da buta 🫖ta kama ruwa idan hannun ta ya taba gaban ta sai ta riko butar ta fito da ita, ke kuma kika dauki butan kikaje kika taba gaban ki. Kema zaki dauka ta wannan hanyar..
4. Kama ruwa da ruwan dake dauke da wadannan cututtukan ko wanka cikin pool dinda keda gurbatattun ruwa.

Akwai hanyõyi da yawa da ake iya daukan wannan cuta batare da macce ko namiji sunyi sex ba

💥 💥 💥 Amma bincike bai tabbatar da ana iya daukan wannan cuta dafa shiga toilet ba... Kamar yanda wasu kecewa toilet infection..

𝘼𝙡𝙖𝙢𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧
1. Jin zafi lokacin da ake fitsari
2. Jin zafi lokacin saduwa
3. Rikitarwar alada ga mata
4. Fitar wasu ruwan kamar madara kamar majina masu wari ga mata ko maza
5. Kaikayi ga gaban macce ko namiji
6. Rashin sha'awar jima'i ko daukewar sha'awa ko bushewar gaba ga macce..
7. Jin ciwo a kasan cibiya ga maza ko ciwon gafe gefen ciki ga mata
8. Yawan fitsari akai akai amma fitsarin baya zuwa da yawa.

𝙎𝙪𝙬𝙖 𝙨𝙪𝙠𝙖𝙛𝙞 𝙠𝙖𝙢𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙢𝙚 𝙮𝙖𝙨𝙖?
mata sunfi maza saurin kamuwa da wannan ciwon saboda wajen fitsarin macce (urethra) gajeruwa ce kuma tana kusa da farar jikin su (fatar jikin musamman wajen pubic Region waje ne mai saurin gumibda damshi shiyasa kwayoyin cuta suke daddale a wajen.). Maza kuma suna iya kasancewa da cutar amma basu sani ba dan basu ganin alamar komai sai suyi ta zubawa mata cutar.

𝙏𝙖𝙮𝙖𝙮𝙖 𝙖𝙠𝙚 𝙢𝙖𝙜𝙖𝙣𝙘𝙚 𝙘𝙪𝙩𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙢𝙖𝙩𝙖𝙠𝙖𝙣 𝙠𝙖𝙧𝙞𝙮𝙖?
1. A daina bin mata barkatai ko biyar maza barkatai batare da robar kariya ba

2. Mata a rika canja panties duk bayan wata daya.. Tsaffin ba'a ce kiyi kyauta dasu ba, ki wanke su sa gishiri ki barsu ga rana har tsawon kwana 3

3. Ko yaushe akaje toilet a rika wanke hannaye da sabulu kafin kama ruwa da bayan kama ruwa musamman mata

4. Maza adaina shan magungunan gargajiya da sunann maganin sanyi. Aje asibiti.

5. Mata ku daina wanke gabanku da sabulu musamman dettol, saboda tana kashe normal flora (wato wasu kwayoyin halittu ne masu taimakawa wajen yaki da miyagun cututtuka) kuma ku rika shan nonon shanu, yana taimakawa wajen kara yawan wannan Normal flora din

6. Idan miji yanada cutar to tabbas har matanshi su duka sai kowa yasha maganin kuma zasu kauracewa sex sai bayan anji dama ko kuma idan za'ayi sex din ayi amfani da roba.. Inma yanada budurwa waje itama sai tasha maganin.

7. Koda kunje asibiti an baku magana kun fara shan magani da kawana biyu kukaji sauki toh kada ku daina shan maganin sai ankai 2 weeks.

💥 💥 💥 💥 💥 Idan da tambaya ko karin bayani ko neman shawara...
KU RUBUTA A COMMENT BOX zan amsa insha Allah 👏 👏 👏 👏 👏

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments