AMFANIN KURKUR(TUMERIC)




 

kamar yadda kuka sani ana amfani da Kurkur wajen GIRKI da kuma GYARAN JIKI. 
bari mudau gyaran jiki, A nijeria kabilar kanuri da shuwa su sukafi amfani dashi wajen gyaran amare don su sami fata mai laushi da haske sannan kurkur yana magance kuraje (pimples),kaushin fata,kyasbi da kuma tabo. saboda haka zan koya muku hadin kurkur wanda zaisa fatar ku haske da kuma laushi(haske bana blicing ba)..

1.kurkur
lemon tsami
gurji
nono ko madara
zaki markada gurji sai ki matsa lemon tsami ki zuba madara da kurkur sai ki kwaba su hadu sannan ki shafa duka jikinki ya samu karmar awa daya sai ki wanke kiyi kamar na sati daya zakiga canji
2.zaki iya kwaba kurkur da madara da kwai ki rika shafawa sau biyu arana don samun hasken fata

3.kurkur
man zaitun
madara da lemon tsami
ki hadesu ki kwaba sai ki rinkg shafawa a fuska kamar minti talatin sai ki wanke kiyi kamar sati biyu kinayi kullum.

 

AMFANI DA KURKUR WAJEN GYARAN FATA 

Kurkur (Turmeric) ba kawai ana amfani da sha wurin sanya abinci ya yi kamshi da kuma dandano ba ne, a’a, ana amfani da shi wurin gyaran fata.


An fara amfani da Kurkum wajen rinin tufafi ne, daga baya aka fara amfani da shi wurin girki a Indiya. Har yanzu ana amfani da kurkum yayin bukukuwa a Indiya saboda launinsa.


A Kudancin Indiya ma akan yi amfani da sha wurin yi wa amarya ado, inda ango yake shafa mata a wuya. Amare a Indiya sukan shafa kurkum a jikinsu don gyaran jiki.


A Najeriya kabilar Kanuri da Shuwa daga kasar Barno sukan yi amfani da kurkum wurin gyara wa amare fata don su samu fata mai laushi da haske da kuma kamshi.. Kurkum kan magance kurajen fata da kaushin fata da tabon fata da kyesbi da kuma sauran cututtukan fata. Yakan taimaka wurin magance yaushi da jemewar fata, sannan na sanya fata haske da kuma taushi.

 

Na kuma kare jiki daga illar hasken rana.
 

Yadda ake hadawa:
 

1. Ki hada cokali 4 na hodar kurkum da jus din lemon tsami da kuma ruwan gurji a cikin kwano ko roba.
2. Daga nan ki zuba cokali 3 na nono ko kuma danyar madara.
3. Sai ki zuba ruwan dumi, sannan ki rika gaurayawa har sai hadin ya gaurayu sosai.
4. Daga nan ki shafa a jikinki zuwa awa daya.
5. Wanke jikinki da ruwan dumi, sannan ki tsane da tawul mai tsabta.

Post a Comment

0 Comments